MAT 16

Neman Alama

1 Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo suka roƙe shi ya nuna musu wata alama daga Sama, domin su gwada shi.

2 Ya amsa musu ya ce, “In magariba ta yi, kuka ga sama ta yi ja, kukan ce, ‘Aha, gari zai yi sarari.’

3 Da safe kuma in kun ga sama ta yi ja, ta kuma gama gari, kukan ce, ‘Yau kam, za a yi hadiri.’ Kuna iya gane yanayin sararin sama, amma ba kwa iya gane alamun zamanin nan.

4 ‘Yan zamani, mugaye, maciya amana, suke nema su ga wata alama, amma ba wata alamar da za a nuna musu, sai dai ta Yunusa.” Sai ya bar su ya tafi.

Yistin Farisiyawa da Sadukiyawa

5 Da almajiran suka isa wancan ƙetare, ashe, sun manta ba su kawo gurasa ba.

6 Sai Yesu ya ce musu, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa.”

7 Sai suka yi magana da juna suka ce, “Ba mu kawo gurasa ba fa!”

8 Da Yesu ya lura da haka sai ya ce, “Ya ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da juna a kan ba ku zo da gurasa ba?

9 Ashe, har yanzu ba ku gane ba? Ba ku tuna da gurasa biyar ɗin nan na mutum dubu biyar ba? Kwando nawa kuka ɗauka?

10 Ko kuma gurasan nan bakwai na mutum dubu huɗu, manyan kwanduna nawa kuka ɗauka?

11 Yaya kuka kasa ganewa? Ba zancen gurasa na yi ba, sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa.”

12 Sa’an nan ne fa suka fahimta cewa, ba ce musu ya yi, su yi hankali da yistin gurasa ba, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da ta Sadukiyawa.

Hurcin Bitrus a kan Yesu

13 To, da Yesu ya shiga ƙasar Kaisariya Filibi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane suke cewa, Ɗan Mutum yake?”

14 Sai suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yahaya Maibaftisma, waɗansu kuwa Iliya, waɗansu kuma Irmiya, ko kuwa ɗaya daga cikin annabawa.”

15 Ya ce musu, “Amma ku fa, wa kuke cewa, nake?”

16 Sai Bitrus ya amsa, ya ce, “Kai ne Almasihu, Ɗan Allah Rayayye.”

17 Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai mai albarka ne, Saminu, ɗan Yunusa! Domin ba ɗan adam ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin Sama.

18 Ina dai gaya maka, kai ne Bitrus, a kan dutsen nan ne zan gina ikilisiyata, wadda ikon Hades ba zai rinjaye ta ba.

19 Zan ba ka mabuɗan Mulkin Sama. Kome ka ƙulla a duniya, zai zama abin da aka riga ƙullewa a Sama ne. Kome ka warware a duniya, zai zama abin da aka riga warwarewa a Sama ne.”

20 Sai ya kwaɓi almajiransa ƙwarai kada su gaya wa kowa shi ne Almasihu.

Yesu Ya Faɗi Irin Mutuwar da Zai Yi

21 Tun daga lokacin nan Yesu ya fara bayyana wa almajiransa, lalle ne ya tafi Urushalima, ya sha wuya iri iri a hannun shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.

22 Sai Bitrus ya ja shi waje ɗaya, ya fara tsawata masa, ya ce, “Allah ya sawwaƙe, ya Ubangiji! Wannan har abada ba zai same ka ba!”

23 Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka yi nesa da ni, ya Shaiɗan! Tarko kake a gare ni. Ba ka tattalin al’amuran Allah, sai dai na mutane.”

24 Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa, ya bi ni.

25 Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi.

26 Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa? Me kuma mutum zai iya bayarwa ya fanshi ransa?

27 Domin Ɗan Mutum zai zo da ɗaukakar Ubansa tare da mala’ikunsa. A sa’an nan ne zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikinsa.

28 Hakika, ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba, sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin Mulkinsa.”