MAT 18

Wane ne Mafi Girma?

1 A lokacin nan almajirai suka zo wurin Yesu, suka ce, “Wa ya fi girma duka a Mulkin Sama?”

2 Sai ya kira wani ƙaramin yaro, ya sa shi a tsakiyarsu,

3 ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in ba kun juyo kun zama kamar ƙananan yara ba, har abada ba za ku shiga Mulkin Sama ba.

4 Duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar ɗan yaron nan, ai, shi ne mafi girma a Mulkin Sama.

5 “Wanda duk ya karɓi ƙaramin yaro ɗaya kamar wannan saboda sunana, Ni ya karɓa.

6 Amma fa duk wanda ya sa ɗaya daga cikin waɗannan ‘yan yara masu gaskatawa da ni ya yi laifi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.”

Sanadodin Yin Zunubi

7 “Kaiton duniya saboda sanadodin tuntuɓe! Lalle sanadodin tuntuɓe ba su da makawa, duk da haka kaiton wanda shi ne sanadin!

8 In kuwa hannunka ko ƙafarka suna sa ka laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai dungu ko da gurguntaka, da a jefa ka madawwamiyar wuta da hannu biyu ko ƙafa biyu.

9 In kuwa idonka yana sa ka laifi, to ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da ido ɗaya, da a jefa ka Gidan Wuta da ido biyu.”

Misali na Ɓatacciyar Tunkiya

10 “Ku dai lura, kada ku raina ɗaya daga cikin waɗannan ‘yan yara. Ina gaya muku, mala’ikunsu a Sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin Sama.[

11 Domin Ɗan Mutum ya zo ne musamman ceton abin da ya ɓata.]

12 To, me kuka gani? In wani na da tumaki ɗari, ɗayarsu ta băce, ashe, ba zai bar tasa’in da taran nan a gindin dutse, ya je neman wadda ta ɓăce ba?

13 In kuwa ya samo ta, labudda, ina gaya muku, ai, farin cikin da yake yi a kanta ya fi na tasa’in da taran nan da ba su taɓa ɓăcewa ba.

14 Haka ma, ba nufin Ubanku da yake cikin Sama ba ne ɗaya daga cikin waɗannan ‘yan yara ya hallaka.”

Ɗan’uwan da Ya Yi Laifi

15 “In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, sai ka je, ka gaya masa laifinsa, kai da shi, ku kaɗai. In ya saurare ka, to, kā maido da ɗan’uwanka ke nan.

16 In kuwa bai saurare ka ba, sai ka tafi da mutum ɗaya ko biyu, don a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.

17 In kuma ya ƙi sauraronsu, sai ka shaida wa ikilisiya. In kuma har ya ƙi sauraron ikilisiyar, ka maishe shi kamar bare, ko mai karɓar haraji.”

Kullewa da Warwarewa

18 “Hakika, ina gaya muku, kome kuka ƙulla a duniya, zai zama abin da aka riga ƙullewa a Sama ne. Kome kuka warware a duniya, zai zama abin da aka riga warwarewa a Sama ne.

19 Har wa yau dai ina gaya muku, in mutum biyu daga cikinku, ra’ayinsu ya zo ɗaya a nan duniya a kan wani abin da za su roƙa, Ubana kuwa da yake Sama zai yi musu shi.

20 Gama kuwa inda mutum biyu ko uku suka taru saboda sunana, ni ma ina nan a tsakiyarsu.”

Misali na Bawa Wanda Bai Yafe Ba

21 Sai Bitrus ya matso ya ce masa, “Ya Ubangiji, sau nawa ɗan’uwana zai yi mini laifi in yafe masa? Har sau bakwai?”

22 Yesu ya ce masa, “Ba sau bakwai kawai na ce maka ba, sai dai bakwai har saba’in.

23 “Saboda haka za a misalta Mulkin Sama da wani sarkin da yake so ya yi ƙididdigar dukiyarsa da yake hannun bayinsa.

24 Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wanda yake bi talanti dubu goma bashi.

25 Da yake ya gagara biya, sai ubangidansa ya yi umarni a sayar da shi da mata tasa da ‘ya’yansa da kuma duk abin da ya mallaka, a biya kuɗin.

26 Sai bawan ya faɗi a gabansa ya yi masa ladabi, ya ce, ‘Ya ubangida, ka yi mini haƙuri, zan biya ka tsaf.’

27 Saboda tausayin bawan nan ubangidansa ya sake shi, ya yafe masa bashin.

28 Amma wannan bawa, da fitarsa sai ya tarar da wani abokin bautarsa, wanda yake bi dinari ɗari bashi. Ya cafi wuyarsa, ya ce, ‘Biya ni abin da nake binka.’

29 Sai abokin bautarsa ya faɗi a gabansa, ya yi ta roƙonsa ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, ai, zan biya ka.’

30 Amma ya ƙi, ya kuma je ya sa shi a kurkuku, har yā biya bashin.

31 Da abokan bautarsa suka ga abin da ya faru, suka yi baƙin ciki gaya, har suka je suka gaya wa ubangidansu duk abin da ya gudana.

32 Sai ubangiji nasa ya kira shi, ya ce masa, ‘Kai mugun bawa ne! Na yafe maka duk bashin nan saboda ka roƙe ni,

33 ashe, bai kyautu kai ma ka ji tausayin abokin bautarka, kamar yadda na ji tausayinka ba?’

34 Ubangijinsa ya yi fushi, ya ba da shi ga masu azabtarwa har yă biya duk bashin da ake binsa.

35 Haka kuma Ubana da yake Sama zai yi da ko wannenku, in ba ku yafe wa ‘yan’uwanku da zuciya ɗaya ba.”