MAT 19

Koyarwar Yesu a kan Kisan Aure

1 To, da Yesu ya gama duk wannan magana, sai ya bar ƙasar Galili, ya shiga ta Yahudiya, wadda take ƙetaren Kogin Urdun.

2 Taro mai yawan gaske suka bi shi, ya kuwa warkar da su a can.

3 Sai waɗansu Farisiyawa suka zo wurinsa su gwada shi, suka ce, “Halal ne mutum ya saki mata tasa a kan kowane dalili?”

4 Ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karantawa ba, cewa, wanda ya halicce su tun farko, dā ma ya yi su, namiji da tamata?”

5 Ya kuma ce, “Don haka fa sai mutum ya bar uwa tasa da ubansa, ya manne wa mata tasa. Haka su biyun nan su zama jiki guda.

6 Har nan gaba su zama ba jiki biyu ba ne, ɗaya ne. Abin da Allah fa ya gama, kada mutum ya raba.”

7 Sai suka ce masa, “To, don me Musa ya yi umarni a ba da takardar kisan aure, a kuma saki matar?”

8 Ya ce musu, “Don taurinkanku ne Musa ya yardar muku ku saki matanku, amma ba haka yake ba tun farko.

9 Ina kuma gaya muku, kowa ya saki mata tasa, in ba a kan laifin zina ba, ya kuma auri wata, ya yi zina ke nan. Wanda ma ya auri sakakkiya, ya yi zina.”

10 Sai almajiran suka ce masa, “In ko haka tsakanin mutum da mata tasa yake, ashe ma, rashin yin aure ya fi amfani.”

11 Amma ya ce musu, “Ba duk mutum ne zai iya ɗaukar maganar nan ba, sai dai waɗanda aka yardar wa.

12 Akwai waɗanda aka haifa babanni, akwai waɗanda mutane ne suka mai da su babanni. Akwai kuma waɗanda suka mai da kansu babanni domin ƙaunar Mulkin Sama. Duk mai iya ɗaukar maganar nan, yă ɗauka.”

Yesu Ya Sa wa ‘Yan Yara Albarka

13 Sa’an nan aka kawo masa yara ƙanana domin ya ɗora musu hannu, ya yi musu addu’a, amma almajiran suka kwaɓe su.

14 Yesu kuwa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Sama na irinsu ne.”

15 Sai ya ɗora musu hannu ya yi tafiyarsa.

Saurayi Mai Dukiya

16 Sai ga wani ya matso wurinsa, ya ce, “Malam, wane aiki nagari ne da lalle zan yi in sami rai madawwami?”

17 Sai ya ce masa, “Don me kake tambayata a kan abin da yake nagari? Ai, Managarci ɗaya ne. In kuwa kana so ka sami wannan rai, to, ka kiyaye umarnan nan.”

18 Sai ya ce masa, “Waɗanne?” Yesu ya ce, “Kada ka yi kisankai. Kada ka yi zina. Kada ka yi sata. Kada ka yi shaidar zur.

19 Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, ka kuma ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.”

20 Saurayin ya ce masa, “Ai, duk na kiyaye waɗannan, me kuma ya rage mini?”

21 Yesu ya ce masa, “In kana so ka zama kammalalle, sai ka je ka sayar da duk mallakarka, ka bai wa gajiyayyu, ka sami wadata a Sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.”

22 Da saurayin nan ya ji haka, sai ya tafi, yana baƙin ciki, don yana da arziki ƙwarai.

23 Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Hakika, ina gaya muku, da wuya mai arziki ya sami shiga Mulkin Sama.

24 Har wa yau ina gaya muku, zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta kafar allura, da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.”

25 Da almajiran suka ji haka, sai suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka ce, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?”

26 Amma Yesu ya dube su, ya ce musu, “Ga mutane kam, ba mai yiwuwa ba ne, amma gun Allah kowane abu mai yiwuwa ne.”

27 Sai Bitrus ya amsa ya ce, “To, ai, ga shi mun bar kome, mun bi ka. Me za mu samu ke nan?”

28 Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, a sabon zamani, sa’ad da Ɗan Mutum ya zauna a maɗaukakin kursiyinsa, ku da kuka bi ni, ku ne kuma za ku zauna a kursiyi goma sha biyu, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra’ila.

29 Kowa ya bar gidaje, ko ‘yan’uwa mata, ko ‘yan’uwa maza, ko uwa, ko uba, ko ‘ya’ya, ko gonaki, saboda sunana, zai sami ninkinsu ɗari, ya kuma gāji rai madawwami.

30 Da yawa na farko za su koma na ƙarshe, na ƙarshe kuma za su zama na farko.”