MAT 20

Ma’aikata a Garkar Inabi

1 “Mulkin Sama kamar wani maigida yake, wanda ya fita da sassafe ya ɗauki ma’aikata don aikin garkarsa ta inabi.

2 Da ya yi lada da su a kan dinari guda a yini, sai ya tura su garkarsa.

3 Wajen ƙarfe tara kuma da ya fita, sai ya ga waɗansu suna zaman banza a bakin kasuwa.

4 Sai ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi garkata, zan kuwa biya ku abin da yake daidai.’ Sai suka tafi.

5 Da ya sāke fita wajen tsakar rana, da kuma azahar, ya sāke yin haka dai.

6 Wajen la’asar kuma ya fita ya sami waɗansu a tsaitsaye, ya ce musu, ‘Don me kuke zaman banza yini zubur?’

7 Sai suka ce masa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’ Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi garkata.’

8 Da magariba ta yi, mai garkar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kirawo ma’aikatan, ka biya su hakkinsu, ka fara daga na ƙarshe har zuwa na farko.’

9 Da waɗanda aka ɗauka wajen la’asar suka zo, sai ko wannensu ya sami dinari guda.

10 To, da na farkon suka zo suka zaci za su sami fiye da haka. Amma su ma aka ba ko wannensu dinari guda.

11 Da suka karɓa sai suka yi ta yi wa maigidan gunaguni,

12 suna cewa, ‘Na bayan nan, ai, aikin sa’a guda kawai suka yi, ka kuwa daidaita mu, mu da muka yini zubur muna shan wahala da zafin rana.’

13 Sai ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Abokina, ai, ban cuce ka ba. Ashe, ba mu yi lada da kai a kan dinari guda ba?

14 Sai ka karɓi halalinka ka tafi. Ni ne na ga damar ba waɗannan na ƙarshe daidai da yadda na ba ka.

15 Ashe, ba ni da ikon yin abin da na ga dama da abin da yake mallakata? Ko kuwa kana jin haushin alherina ne?’

16 Saboda haka na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma za su koma na ƙarshe.”

Yesu kuma Ya Sāke Faɗar Irin Mutuwar da Zai Yi

17 Yesu na tafiya Urushalima, ya ɗauki almajiran nan goma sha biyu waje ɗaya. Suna tafiya ke nan sai ya ce musu,

18 “To, ga shi, za mu Urushalima, za a kuma ba da Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman Attaura, za su kuwa yi masa hukuncin kisa,

19 su bashe shi ga al’ummai, su yi masa ba’a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma za a tashe shi.”

Roƙon da Mahaifiyar Yakubu da Yahaya ta Yi

20 Sa’an nan uwar ‘ya’yan Zabadi ta matso wurinsa tare da ‘ya’yanta, ta durƙusa a gabansa, ta roƙe shi wani abu.

21 Sai ya ce mata, “Me kike bukata?” Ta ce masa, “Ka yi umarni waɗannan ‘ya’yana biyu su zauna, ɗaya a damanka, ɗaya a hagunka, a mulkinka.”

22 Amma Yesu ya amsa ya ce, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Kwa iya shan ƙoƙon da ni zan sha?” Suka ce masa, “Ma iya.”

23 Sai ya ce musu, “Lalle kwa sha ƙoƙona, amma zama a damana da haguna, ba nawa ba ne da zan bayar, ai, na waɗanda Ubana ya riga ya shirya wa ne.”

24 Da almajiran nan goma suka ji haka, sai suka ji haushin ‘yan’uwan nan biyu.

25 Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani sarakunan al’ummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gasa musu iko.

26 Ba haka zai zama a tsakaninku ba. Amma duk wanda yake son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku.

27 Wanda duk kuma yake so ya shugabance ku, lalle ne ya zama bawanku,

28 kamar yadda Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba sai dai domin shi ya yi bautar, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”

Makafi Biyu Sun Sami Ganin Gari

29 Suna fita daga Yariko ke nan, sai wani babban taro ya bi shi.

30 Ga mutum biyu makafi zaune a bakin hanya. Da suka ji dai Yesu ne yake wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ya Ubangiji, ka ji tausayinmu, ya Ɗan Dawuda!”

31 Jama’a suka kwaɓe su su yi shiru. Amma sai ƙara ɗaga murya suke yi ƙwarai da gaske, suna cewa, “Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, ya Ɗan Dawuda!”

32 Sai Yesu ya tsaya, ya yi kiransu ya ce, “Me kuke so in yi muku?”

33 Suka ce masa, “Ya Ubangiji, mu dai mu sami gani!”

34 Domin tausayi, sai Yesu ya taɓa idanunsu, nan take suka gani, suka bi shi.