MAT 25

Misali na Budurwai Goma

1 “Sa’an nan za a kwatanta Mulkin Sama da ‘yan mata goma da suka ɗauki fitilunsu suka tafi taryen ango.

2 Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuwa masu hikima.

3 Don kuwa a lokacin da wawayen nan suka ɗauki fitilunsu, ashe, ba su riƙo mai ba.

4 Masu hikimar nan kuwa sun riƙo kwalaben mai da fitilunsu.

5 Da yake angon ya yi jinkiri, duk sai suka yi gyangyaɗi, har barci ya share su.

6 Can tsakar dare sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito ku tarye shi!’

7 Duk ‘yan matan nan suka tashi suka gyaggyara fitilunsu.

8 Sai wawayen nan suka ce wa masu hikimar, ‘Ku sa mana ɗan manku kaɗan mana, fitilunmu na mutuwa!’

9 Amma masu hikimar suka amsa suka ce, ‘Ai, watakila ba zai ishe mu mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’

10 Tun suna wajen sayen, sai angon ya iso, waɗanda suke shirye suka shiga wurin biki tare da shi, aka kuma rufe ƙofa.

11 Daga baya sai waɗancan ‘yan matan ma suka iso, suka ce, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ka buɗe mana!’

12 Sai ya amsa ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, ni ban san ku ba.’

13 Don haka, sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ba, ko kuwa sa’ar.”

Misali na Talanti

14 “Kamar mutum ne da zai yi tafiya, ya kira bayinsa, ya danƙa musu dukiyarsa.

15 Ya ba ɗaya talanti biyar, ɗaya talanti biyu, wani kuma ya ba shi ɗaya, kowa dai gwargwadon ƙarfinsa. Sa’an nan ya tafi.

16 Shi wanda ya karɓi talanti biyar ɗin nan, nan da nan sai ya je ya yi ta jujjuya su, har wuri ya bugi wuri.

17 Haka kuma wanda ya karɓi talanti biyu, shi ma sai wuri ya bugi wuri.

18 Amma wannan da ya karɓi talanti ɗaya ɗin, sai ya je ya tona rami ya ɓoye kuɗin ubangijinsa.

19 To, da aka daɗe sai ubangijin bayin nan ya dawo ya daidaita lissafi da su.

20 Shi wannan da ya karɓi talanti biyar sai ya matso ya kawo waɗansu talanti biyar, ya ce, ‘Ya ubangiji, kā ba ni talanti biyar, ga shi kuma, na ci ribar biyar.’

21 Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangidanka.’

22 Sai mai talanti biyun nan kuma ya matso, ya ce, ‘Ya ubangiji, kā ba ni talanti biyu, ga shi kuma, na ci ribar biyu.’

23 Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangijinka.’

24 Shi kuma wanda ya karɓi talanti guda ɗin, sai ya matso, ya ce, ‘Ya ubangiji, na sani kai mutum ne mai tsanani, kana son girbi inda ba kai ka shuka ba, mai son banza ne.

25 Shi ya sa na ji tsoro, har na je na yi tono na ɓoye talantinka. To, ga kayanka nan!’

26 Sai ubangijinsa ya amsa masa ya ce, ‘Kai mugun bawa, malalaci! Ashe, ka sani ina girbi inda ba ni na shuka ba, ni kuma mai son banza ne?

27 Ya kamata ka sa kuɗina a ma’aji, da na dawo kuma da sai in karɓi abina har da riba!

28 Don haka sai ku karɓe talantin daga gunsa, ku bai wa mai goman nan.

29 Don duk mai abu a kan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.

30 Ku kuma jefa banzan bawan nan a baƙin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baki.’ ”

Shara’anta wa Al’ummai

31 “Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa tare da mala’iku duka, sa’an nan ne zai zauna a maɗaukakin kursiyinsa.

32 Za a tara dukan al’ummai a gabansa, zai kuma ware su dabam dabam, kamar yadda makiyayi yake ware tumaki da awaki.

33 Zai sa tumaki a damansa, awaki kuwa a hagunsa.

34 Sa’an nan ne Sarki zai ce wa waɗanda suke dama da shi, ‘Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya.

35 Domin na ji yunwa, kun ba ni abinci. Na ji ƙishirwa, kun ba ni na sha. Na yi baƙunci, kun saukar da ni.

36 Na yi huntanci, kun tufasar da ni. Na yi rashin lafiya, kun ziyarce ni. Ina kurkuku, kun kula da ni.’

37 Sa’an nan ne masu adalci za su amsa masa su ce, ‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa muka cishe ka, ko kuwa da ƙishirwa muka shayar da kai?

38 A yaushe kuma muka gan ka baƙo muka sauke ka, ko kuwa huntu muka tufasar da kai?

39 Ko kuma a yaushe muka gan ka da rashin lafiya, ko a kurkuku muka kula da kai?’

40 Sai Sarkin zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake kun yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ‘yan’uwana mafi ƙanƙanta, ai, ni kuka yi wa.’

41 Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke na hagun, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, ku shiga madawwamiyar wuta, wadda aka tanadar wa Iblis da mala’ikunsa.

42 Don na ji yunwa, ba ku ba ni abinci ba. Na ji ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba.

43 Na yi baƙunci, ba ku sauke ni ba. Na yi huntanci, ba ku tufasar da ni ba. Na yi rashin lafiya, ina kuma kurkuku, ba ku kula da ni ba.’

44 Sa’an nan su ma za su amsa su ce, ‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa, ko da ƙishirwa, ko da baƙunci, ko da huntanci, ko da rashin lafiya, ko a kurkuku, ba mu kula da kai ba?’

45 Sa’an nan zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ai, ni ne ba ku yi mini ba.’

46 Waɗannan ne za su shiga madawwamiyar azaba, masu adalci kuwa rai madawwami.”