MAT 26

Shugabanni Sun Ƙulla Shawara Gaba da Yesu

1 Da Yesu ya gama duk wannan magana, sai ya ce wa almajiransa,

2 “Kun san Idin Ƙetarewa saura kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum a gicciye shi.”

3 Sai manyan firistoci da shugabannin jama’a suka taru a gidan babban firist, mai suna Kayafa.

4 Suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci su kashe shi.

5 Amma suka ce, “Ba dai a lokacin idi ba, don kada jama’a su yi hargitsi.”

An Shafi Yesu da Man Ƙanshi a Betanya

6 To, sa’ad da Yesu yake Betanya a gidan Saminu kuturu,

7 sai wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tandu na man ƙanshi mai tsadar gaske, ta tsiyaye masa a kā, a lokacin da yake cin abinci.

8 Amma da almajiran suka ga haka, sai suka ji haushi suka ce, “Wannan almubazzaranci fa!

9 Da ma an sayar da man nan kuɗi mai yawa, an ba gajiyayyu!”

10 Yesu kuwa da ya lura da haka, sai ya ce musu, “Don me kuke damun matar nan? Ai, alheri ta yi mini, na gaske kuwa.

11 Kullum kuna tare da talakawa, amma ba kullum ne kuke tare da ni ba.

12 Zuba man nan da ta yi a jikina, ta yi shi ne domin tanadin jana’izata.

13 Hakika, ina gaya muku, duk inda za a yi bisharar nan a duniya duka, abin da matar nan ta yi za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”

Yahuza Ya Yarda Ya Ba Da Yesu

14 Sai ɗaya daga cikin sha biyun nan, mai suna Yahuza Iskariyoti, ya je wurin manyan firistoci,

15 ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi a gare ku?” Sai suka ƙirga kuɗi azurfa talatin, suka ba shi.

16 Tun daga lokacin nan ne ya riƙa neman hanyar da zai bashe shi.

Yesu Ya Ci Idin Ƙetarewa tare da Almajiransa

17 To, a ranar farko ta idin abinci marar yisti sai almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, “Ina kake so mu shirya maka cin Idin Ƙetarewa?”

18 Sai ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce lokacinsa ya yi kusa, zai ci Idin Ƙetarewa a gidanka tare da almajiransa.’ ”

19 Almajiran kuwa suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka shirya Idin Ƙetarewa.

20 Da magariba ta yi, sai ya zauna cin abinci tare da almajiran nan goma sha biyu.

21 Suna cikin cin abinci, sai ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”

22 Sai suka yi baƙin ciki gaya, suka fara ce masa da ɗaya ɗaya, “Ni ne, ya Ubangiji?”

23 Sai ya amsa ya ce, “Wanda muke ci a ƙwarya ɗaya, shi ne zai bashe ni.

24 Ɗan Mutum zai tafi ne, yadda labarinsa yake a rubuce, duk da haka kaiton mutumin nan da yake ba da Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da zai fiye masa.”

25 Sai Yahuza da ya bashe shi ya ce, “Ko ni ne, ya Shugaba?” Yesu ya ce masa, “Ga shi, kai ma ka faɗa.”

Cin Jibin Ubangiji

26 Suna cikin cin abinci, sai Yesu ya ɗauki gurasa, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba almajiran, ya ce, “Ungo, ku ci. Wannan jikina ne.”

27 Sai ya ɗauki ƙoƙo bayan ya kuma yi godiya ga Allah, sai ya ba su, ya ce, “Dukkanku ku shassha.

28 Wannan jinina ne na tabbatar alkawari, wanda za a zubar saboda mutane da yawa, domin gafarar zunubansu.

29 Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai dai a ranar nan da za mu sha wani sabo tare da ku a Mulkin Ubana.”

30 Da suka yi waƙar yabon Allah, sai suka fita suka tafi Dutsen Zaitun.

Bitrus Zai Yi Musun Sanin Yesu

31 Sai Yesu ya ce musu, “Duk za ku yi tuntuɓe sabili da ni a wannan dare domin a rubuce yake cewa, ‘Zan bugi makiyayi, tumakin garken kuwa za su fasu.’

32 Amma fa bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa ƙasar Galili.”

33 Bitrus ya ce masa, “Ko duk sun yi tuntuɓe sabili da kai, ni kam ba zan yi tuntuɓe ba faufau.”

34 Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, ko a wannan dare, kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”

35 Bitrus ya ce masa, “Ko za a kashe ni tare da kai, ba zan yi musun saninka ba.” Haka ma duk almajiran suka ce.

Yesu ya Yi Addu’a a Gatsemani

36 Sa’an nan Yesu ya zo da su wani wuri da ake kira Gatsemani. Ya ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, Ni kuwa zan je can in yi addu’a.”

37 Sai ya ɗauki Bitrus da ‘ya’yan nan na Zabadi biyu, ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai.

38 Sai ya ce musu, “Raina yana shan wahala matuƙa, har ma kamar in mutu. Ku dakata a nan, ku zauna a faɗake tare da ni.”

39 Da ya ci gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubana, in mai yiwuwa ne, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalar nan. Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka.”

40 Ya komo wurin almajiran, ya ga suna barci, sai ya ce wa Bitrus, “Ashe, ba za ku iya zama a faɗake tare da ni ko da na sa’a ɗaya ba?

41 Ku zauna a faɗake, ku yi addu’a, kada ku faɗa ga gwaji. Lalle ruhu ya ɗauka, amma jiki rarrauna ne.”

42 Har wa yau a komawa ta biyu, sai ya je ya yi addu’a, ya ce, “Ya Ubana, in wannan ba zai wuce ba sai na sha shi, to, a aikata nufinka.”

43 Har yanzu dai ya dawo ya ga suna barci, don duk barci ya cika musu ido.

44 Har wa yau ya sāke barinsu, ya koma ya yi addu’a ta uku, yana maimaita maganar dā.

45 Sai ya komo wurin almajiran, ya ce musu, “Har yanzu barci kuke yi, kuna hutawa? To, ga shi, lokaci ya yi kusa. An ba da Ɗan Mutum ga masu zunubi.

46 Ku tashi mu tafi. Kun ga, ga mai bashe ni nan, ya matso!”

An Ba da Yesu, an Kama Shi

47 Kafin ya rufe baki ga Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, da babban taron mutane riƙe da takuba da kulake, manyan firistoci da shugabanni ne suka turo su.

48 To, mai bashe shi ɗin ya riga ya ƙulla da su cewa, “Wanda zan yi wa sumba, shi ne mutumin. Ku kama shi.”

49 Nan da nan ya matso wurin Yesu, ya ce, “Salama alaikun, ya Shugaba!” Sai ya yi ta sumbantarsa.

50 Yesu ya ce masa, “Abokina, abin da ya kawo ka ke nan?” Suka matso suka ɗanke Yesu, suka kama shi.

51 Sai ga ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu ya miƙa hannu ya zaro takobinsa, ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunne.

52 Sai Yesu ya ce masa, “Mai da takobinka kube. Duk wanda ya zare takobi, takobi ne ajalinsa.

53 Kuna tsammani ba ni da ikon neman taimako gun Ubana ba, nan da nan kuwa ya aiko mini fiye da rundunar mala’iku goma sha biyu?

54 To, ta yaya ke nan za a cika Littattafai a kan lalle wannan abu ya kasance?”

55 Nan take Yesu ya ce wa taron jama’a, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗan fashi? Kowace rana nakan zauna a Haikali ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba.

56 Amma duk wannan ya auku ne domin a cika littattafan annabawa.” Daga nan duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.

Yesu a Gaban ‘Yan Majalisa

57 Sai waɗanda suka kama Yesu suka tafi da shi wurin Kayafa, babban firist, inda malaman Attaura da shugabanni suke tare.

58 Amma Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin gidan babban firist. Da ya shiga, sai ya zauna tare da dogaran Haikali, don ya ga ƙarshen abin.

59 To, sai manyan firistoci da ‘yan majalisa duka suka nemi shaidar zur da za a yi wa Yesu don su sami dama su kashe shi.

60 Amma ba su samu ba, ko da yake masu shaidar zur da yawa sun zazzaburo. Daga baya sai waɗansu biyu suka matso,

61 suka ce, “Wannan ya ce, wai zai iya rushe Haikalin nan na Allah, ya kuma gina shi a cikin kwana uku.”

62 Sai babban firist ya miƙe ya ce, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?”

63 Amma Yesu na shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na gama ka da Allah Rayayye, ka faɗa mana ko kai ne Almasihu, Ɗan Allah.”

64 Sai Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa. Ina kuwa gaya muku a nan gaba za ku ga Ɗan Mutum zaune a dama da Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gajimare.”

65 Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa, ya ce, “Ya yi saɓo! Wace shaida kuma za mu nema? Yanzu kun ji saɓon da ya yi!

66 Me kuka gani?” Suka amsa suka ce, “Ya cancanci kisa!”

67 Sai suka tattofa masa yau a fuska, suka bubbuge shi, waɗansu kuma suka mammare shi,

68 suna cewa, “Yi mana annabci, kai Almasihu! Faɗi wanda ya buge ka!”

Bitrus Ya Yi Musun Sanin Yesu

69 To, Bitrus kuwa yana zaune a tsakar gida a waje, sai wata baranya ta zo ta tsaya a kansa, ta ce, “Kai ma, ai, tare kake da Yesu Bagalile!”

70 Amma ya musa a gabansu duka ya ce, “Ni ban san abin da kike nufi ba.”

71 Da ya fito zaure, sai wata baranya kuma ta gan shi, ta ce wa waɗanda suke tsaitsaye a wurin, “Ai, mutumin nan tare yake da Yesu Banazare!”

72 Sai ya sāke musawa har da rantsuwa ya ce, “Ban ma san mutumin nan ba.”

73 Jim kaɗan sai na tsaitsayen suka matso, suka ce wa Bitrus, “Lalle kai ma ɗayansu ne, don irin maganarka ta tona ka.”

74 Sai ya fara la’anar kansa, yana ta rantse-rantse, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba.” Nan da nan sai zakara ya yi cara.

75 Sai Bitrus ya tuna da maganar Yesu cewa, “Kafin carar zakara za ka yi musun sanina sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.