ROM 11

Sauran Isra’ila

1 To, ina tambaya. Wato, Allah ya juya wa jama’arsa baya ke nan? A’a, ko kusa! Ai, ni ma da kaina Ba’isra’ile ne, zuriyar Ibrahim, na kabilar Biliyaminu.

2 Ko kaɗan, Allah bai juya wa jama’arsa da ya zaɓa tun dā baya ba. Ko ba ku san abin da Nassi ya faɗa ba ne, a game da Iliya? Yadda ya kai kuka ga Allah, a kan Isra’ila, ya ce,

3 “Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka, sun rurrushe bagadanka na hadaya. Ni kaɗai ne na ragu, suna kuwa neman raina.”

4 Amma me Allah ya amsa masa? Cewa ya yi, “Na keɓe wa kaina mutum dubu bakwai waɗanda ba su taɓa durƙusa wa Ba’al ba.”

5 Haka ma a wannan zamani akwai ragowa, waɗanda aka zaɓa saboda alherinsa.

6 In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga aikin lada ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma.

7 To, yaya ke nan? Ashe, abin da Isra’ila take nema, ba su samu ba ke nan, amma zaɓaɓɓun nan sun samu, sauran kuwa sun taurare.

8 Yadda yake a rubuce cewa,

“Allah ya toshe musu basira,

Ya ba su ido, ba na gani ba,

Da kuma kunne, ba na ji ba,

Har ya zuwa yau.”

9 Dawuda kuma ya ce,

“Da ma shagalinsu ya zama musu tarko, abin shammatarsu,

Sanadin faɗuwarsu kuma, har aniyarsu ta koma kansu.

10 Idonsu kuma yă shiga duhu, har su kasa gani,

Ka kuma tanƙwara bayansu har abada.”

Ceton Al’ummai

11 Ina kuma tambaya. Faɗuwar da suka yi, sun faɗi ba tashi ke nan? A’a, ko kusa! Sai ma faɗuwarsu ta zama sanadin ceto ga al’ummai, don a sa Isra’ila kishi.

12 To, in kuwa duniya ta arzuta da hasararsu, wa zai kimanta yawan albarka, in adadinsu masu ɗungumawa ga Allah ya cika?

13 Da ku al’ummai fa nake. Tun da yake ni manzo ne ga al’ummai, ina taƙama da aikina,

14 ko ta wane hali in sa kabilata kishin zuci, har in ceci waɗansunsu.

15 Domin in an sulhunta duniya ga Allah, saboda yar da su da aka yi, to, in an karɓe su fa, ba sai rai daga matattu ba?

16 In curin farko tsattsarka ne, haka sauran gurasar ma. In kuma saiwa tsattsarka ce, haka rassan ma.

17 Amma in an sassare waɗansu rassan zaitun na gida, kai kuma da kake zaitun na jeji aka ɗaura aure da kai a gurbinsu, kana kuma shan ni’imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan,

18 kada ka yi wa sauran rassan alwashi. In kuwa ka yi, ka tuna fa, ba kai kake ɗauke da saiwar ba, saiwar ce take ɗauke da kai.

19 Kila za ka ce, “Ai, an sare rassan nan ne, don a ɗaura aure da ni.”

20 Hakika haka ne, amma saboda rashin bangaskiyarsu ne aka sare su, kai kuwa saboda bangaskiyarka ne kake kafe. Kada fa ka nuna alfarma, sai dai ka ji tsoron Allah.

21 Da yake Allah bai bar rassan asalin ba, kai ma ba zai bar ka ba.

22 Dubi fa alherin Allah da kuma tsananinsa, wato, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, alherinsa kuwa a gare ka, muddin ka ɗore a cikin alherin. In ba haka ba, kai ma sai a datse ka.

23 Ko su ma, in dai ba su nace wa rashin bangaskiyarsu ba, sai a ɗaura aure da su, domin Allah yana da ikon sāke mai da su.

24 Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali?

Komar da Isra’ila ga Matsayinsa

25 ‘Yan’uwa, ga wata asirtacciyar gaskiya da nake so ku sani, domin kada ku zaci ku masu hikima ne, taurarewar nan–wadda ba mai tabbata ba ce–ta sami Isra’ilawa ne, har adadin al’ummai masu ɗungumawa zuwa ga Allah ya cika.

26 Ta haka nan ne Isra’ila duka za su sami ceto, kamar yadda yake a rubuce cewa,

“Mai Ceto zai zo daga Sihiyona,

Zai kuma kawar da rashin bin Allah daga zuriyar Yakubu,”

27 “Cikar alkawarina a gare su ke nan,

Sa’ad da na ɗauke musu zunubansu.”

28 A game da bishara kuma, maƙiyan Allah ne su, domin amfaninku ne kuwa. Amma a game da zaɓen Allah, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu.

29 Domin baiwar Allah da kiransa ba sa tashi.

30 Kamar yadda kuka ƙi bin Allah a dā, amma a yanzu aka yi muku jinƙai saboda rashin biyayyarsu,

31 haka su ma da suke marasa biyayya a yanzu, yanzu a yi musu jinƙai kamar yadda aka yi muku.

32 Don Allah ya kulle kowa a cikin rashin biyayya, domin ya nuna jinƙai ga kowa.

33 Zurfin hikimar Allah da na saninsa da rashin iyaka suke! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban bincikewa, hanyoyinsa kuma sun fi gaban bin diddigi!

34 “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji?

Ko kuwa wa ya taɓa ba shi wata shawara?”

35 “Wa kyauta ta shiga tsakaninsu da Allah, ya fara bayarwa,

Har da za a sāka masa?”

36 Ai, daga gare shi ne, ta wurinsa kuma, dukkan abubuwa suke, shi ne kuma makomarsu. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada. Amin.