ROM 12

Hadaya Mai Rai

1 Don haka ina roƙonku ‘yan’uwa, saboda yawan jinƙai na Allah, ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah. Domin wannan ita ce ibadarku ta ainihi.

2 Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.

3 Albarkacin alherin da aka yi mini ina yi wa kowannenku gargaɗi kada ya ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, sai dai ya san kansa, gwargwadon bangaskiyar da Allah ya ba shi.

4 Wato kamar yadda gaɓoɓi da yawa suke harhaɗe a jiki ɗaya, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba,

5 haka mu ma, ko da yake muna da yawa, jiki ɗaya muke haɗe da Almasihu, kowannenmu kuma gaɓar ɗan’uwansa ne.

6 Da yake muna da baiwa iri iri, gwargwadon alherin da aka yi mana, to, sai mu yi amfani da su. In ta annabci ce, sai mu yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarmu,

7 in ta hidima ce, wajen hidimarmu, mai koyar da Maganar Allah kuwa, wajen koyarwarsa,

8 mai ƙarfafa zuciya kuwa, wajen ƙarfafawarsa, mai yin gudunmawa kuwa, yă bayar hannu sake, shugaba yă yi shugabancinsa da himma, mai yin aikin tausayi, yă yi shi da fara’a.

Gargaɗi a kan Zaman Kirista

9 Ƙauna ta kasance sahihiya. Ku yi ƙyamar abin da yake mugu, ku lazamci abin da yake nagari.

10 A game da ƙaunar ‘yan’uwa kuwa, ku ƙaunaci juna gaya. A wajen ba da girma, kowa yă riga ba ɗan’uwansa.

11 Kada ku sassauta a wajen himma, ku himmantu a ruhu, kuna bauta wa Ubangiji.

12 Sa zuciyar nan taku ta sa ku farin ciki, ku jure wa wahala, ku nace wa yin addu’a.

13 Ku agaji tsarkaka, ku himmantu ga yi wa baƙi alheri.

14 Ku sa wa masu tsananta muku albarka. Ku sa musu albarka, kada ku la’ance su.

15 Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka.

16 Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna alfarma, sai dai ku miƙa kanku ga aikata ayyukan tawali’u. Kada ku aza kanku masu hikima ne.

17 Kada ku rama muguntar kowa da mugunta. Ku yi ta lura al’amuranku su zama daidai a gaban kowa.

18 In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa.

19 Ya ku ƙaunatattuna, kada ku ku yi ramuwa, sai dai ku bar wa fushin Allah. Domin a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce, ni zan saka, in ji Ubangiji.”

20 Har ma “in maƙiyinka yana jin yunwa, sai ka ci da shi. In yana jin ƙishirwa, ka shayar da shi. Don ta haka ne za ka tula garwashin wuta a kansa.”

21 Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.