ROM 15

Faranta wa Ɗan’uwanka Rai, ba kanka Ba

1 To, mu da muke ƙarfafa, ya kamata mu ɗauki nauyin raunana, kada mu yi sonkai.

2 Kowannenmu yă faranta wa maƙwabcinsa rai, don kyautata zamansa da kuma inganta shi.

3 Gama ko Almasihu ma bai yi sonkai ba, amma kamar yadda yake a rubuce cewa, “Zagin da waɗansu suka yi maka duk yā komo kaina.”

4 Ai, duk abin da aka rubuta tun dā, an rubuta shi ne domin a koya mana, domin mu ɗore a cikin sa zuciyar nan tamu ta wurin haƙuri da ta’aziyyar da Littattafai suke yi mana.

5 Allah mai ba da haƙuri da ta’aziyya, yă ba ku zaman lafiya da juna bisa halin Almasihu Yesu,

6 domin ku ɗaukaka Allah, Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma Ubansa, nufinku ɗaya, bakinku ɗaya.

Bishara ga Al’ummai

7 Saboda haka ku karɓi juna da hannu biyu biyu, kamar yadda Almasihu ya karɓe ku hannu biyu biyu, domin a ɗaukaka Allah.

8 Ina dai gaya muku, Almasihu ya zama bara ga Isra’ila, domin nuna gaskiyar Allah, domin kuma tabbatar da alkawaran nan, da Allah ya yi wa kakannin kakanninmu,

9 al’ummai kuma su ɗaukaka Allah saboda jinƙansa. Yadda yake a rubuce,

“Domin haka zan yabe ka a cikin al’ummai,

In kuma yi waƙar yabon sunanka.”

10 Har wa yau kuma an ce,

“Ya ku al’ummai, ku yi ta farin ciki tare da jama’arsa.”

11 Da kuma,

“Ku yabi Ubangiji, ya ku al’ummai duka,

Dukkan kabilai kuma su yabe shi.”

12 Ishaya kuma ya ce,

“Tsatson Yesse zai bayyana,

Wanda zai tashi yă mallaki al’ummai,

A gare shi ne al’ummai za su sa zuciya.”

13 Allah mai kawo sa zuciya, yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama saboda bangaskiyarku, domin ku yi matuƙar sa zuciya ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.

14 Ya ‘yan’uwana, ni ma da kaina na amince da ku, cewa ku da kanku masu nagarta ne ƙwarai da gaske, masu cikakken sani, kun kuma isa ku gargaɗi juna.

15 Duk da haka, a kan waɗansu batatuwan da na rubuto muku, na ƙara ƙarfafawa ƙwarai, domin tuni, saboda alherin da Allah ya yi mini

16 da ya sa ni bawan Almasihu Yesu ga al’ummai, ina hidimar bisharar Allah, domin al’ummai su zama hadaya mai karɓuwa a gare shi, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki.

17 Ashe kuwa, ina da dalilin yin alfarma da Almasihu Yesu a game da al’amarin Allah.

18 Ba zan kuskura in faɗi kome ba, sai abin da Almasihu ya aikata ta wurina, a wajen sa al’ummai biyayya ta wurin maganata da aikina,

19 ta wurin ikon mu’ujizai, da abubuwan al’ajabai, da kuma ta wurin ikon Ruhun, har dai daga Urushalima da kewayenta, har zuwa Ilirikun, na yi bisharar Almasihu a ko’ina.

20 Har ya zama mini abin buri in sanar da bishara, a inda ba a taɓa sanar da sunan Almasihu ba, don kada in ɗora ginina a kan harsashin wani,

21 sai dai kamar yadda yake a rubuce,

“Waɗanda ba a taɓa faɗa wa labarinsa ba, za su gane,

Waɗanda ba su taɓa jin labarinsa ba ma, za su fahimta.”

Bulus Ya Shirya yă Ziyarci Roma

22 Shi ya sa sau da yawa ban sami sukunin zuwa wurinku ba.

23 A yanzu kuwa tun da yake ba sauran wani wuri da ya rage mini a lardin nan, shekaru da yawa kuma ina ɗokin zuwa wurinku,

24 ina sa zuciya in gan ku, in zan wuce zuwa ƙasar Asbaniya, har ma ku raka ni zuwa can, bayan da na ɗan ɗebe kewa da ganinku.

25 Amma a yanzu kam, za ni Urushalima, don in kai wa tsarkaka gudunmawa.

26 Mutanen Makidoniya da na Akaya, sun ji daɗin yin gudunmawar daidai gwargwado ga matalauta, a cikin tsarkakan da suke a Urushalima.

27 Sun kuwa ji daɗin yin haka, domin hakika kamar bashi ne a kansu. Domin tun da yake al’ummai sun yi tarayya da su a kan ni’imarsu ta ruhu, ashe kuwa, ya kamata su ma su taimake su da ni’imarsu ta duniya.

28 In kuwa na gama wannan, na kuma danƙa musu wannan taimako lafiya, sai in bi ta kanku zuwa ƙasar Asbaniya.

29 Na kuma sani, in na zo wurinku, zan zo ne a cikin falalar albarkar Almasihu

30 Amma ina roƙonku ‘yan’uwa, saboda Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma ƙaunar nan da Ruhu yake bayarwa, ku taya ni yin addu’a da naciya ga Allah saboda kaina,

31 domin in tsira daga maƙiyan bangaskiya a Yahudiya, don kuma gudunmawar da nake kaiwa Urushalima, ta zama abar karɓa ga tsarkaka,

32 har in Allah ya yarda in iso wurinku da farin ciki, mu wartsake tare.

33 Allah mai ba da salama ya kasance tare da ku duka. Amin.