ROM 7

Ƙiyasi da Aure

1 Ya ‘yan’uwa, ko ba ku sani ba, shari’a tana da iko da mutum, muddin yana raye ne kawai? Da waɗanda suka san shari’a fa nake.

2 Misali, mace mai aure, shari’a ta ɗaure ta ga mijinta muddin yana da rai. Amma in mijinta ya mutu, ta kuɓuta daga igiyar auren ke nan.

3 Don haka, muddin mijinta yana da rai, in ta auri wani, sai a kira ta mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, ta kuɓuta daga igiyar wannan aure, ko da ta auri wani kuwa, ita ba mazinaciya ba ce.

4 Haka kuma ‘yan’uwana, kun zama matattu ga Shari’a, ta wurin jikin Almasihu, domin ku zama mallakar wani, wato, wanda aka tashe shi daga matattu, domin mu ba da amfani ga Allah.

5 Ai, dā sa’ad da muke zaman halin mutuntaka, muguwar sha’awa wadda faɗakarwar Shari’a take sa a yi, ita take aiki a gaɓoɓinmu, tă wurin haddasa mutuwa.

6 Amma a yanzu mun ‘yantu daga Shari’a, mun mutu daga abin da dā ya ɗaure mu ke nan, har muna iya bauta wa Allah da sabon rai da Ruhu, ba da tsofaffin rubutattun ka’idodi ba.

Damuwa wadda Zunubin da Yake a Cikinmu Take Haddasawa

7 To, me kuma za mu ce? Shari’a zunubi ce? A’a, ko kusa! Amma kuwa duk da haka, da ba domin Shari’a ba, da ban san zunubi ba. Da ba domin Shari’a ta ce, “Kada ka yi ƙyashi” ba, da ban san ƙyashi ba.

8 Amma zunubi, da ya sami ƙofa ta hanyar umarni, sai ya haddasa ƙyashi iri iri a zuciyata. Gama da ba domin shari’a ba, da zunubi ba shi da wani tasiri.

9 Dā kam, sa’ad da ban san shari’a ba, ni rayayye ne, amma da na san umarnin, sai zunubi ya rayu, ni kuma sai na mutu.

10 Umarnin nan kuwa, wanda manufarsa a gare ni rai ne, sai ya jawo mini mutuwa.

11 Don kuwa zunubi ya sami ƙofa ta hanyar umarni, sai ya yaudare ni, ta wurinsa kuwa ya kashe ni.

12 Domin haka Shari’a da kanta mai tsarki ce, umarnin kuma mai tsarki ne, daidai ne, nagari ne.

13 Wato, abar nan da take tagari ta jawo mini mutuwa ke nan? A’a, ko kusa! Zunubi ne ya jawo, domin ya bayyana kansa shi zunubi ne, gama ta wurin abar nan tagari ya jawo mini mutuwa, ta dalilin umarnin nan kuma, zunubi ya bayyana matuƙar muninsa.

14 Mun dai san Shari’a aba ce ta ruhu, ni kuwa mai halin mutuntaka ne, bautar zunubi kawai nake yi.

15 Ban ma fahimci abin da nake yi ba. Don ba abin da nake niyya yi, ba shi nake aikatawa ba, abin da nake ƙi, shi nake yi.

16 To, idan abin da ba na niyya, shi nake yi, na yarda ke nan Shari’a aba ce mai kyau.

17 Ashe kuwa, ba ni nake yinsa ba ke nan, zunubin da ya zaune mini ne.

18 Don na sani ba wani abin kirki da ya zaune mini, wato a jikina. Niyyar yin abin da yake daidai kam, ina da ita, sai dai ikon zartarwar ne babu.

19 Nagarin abin da nake niyya yi kuwa, ba shi nake yi ba, sai dai mugun abin da ba na niyya, shi nake aikatawa.

20 To, idan abin da ba na niyya shi nake yi, ashe kuwa, ba ni nake yinsa ba ke nan, zunubin da ya zaune mini ne.

21 Sai na ga, ashe, ya zama mini ka’ida, in na so yin abin da yake daidai, sai in ga mugunta tare da ni.

22 Ni kam, a birnin zuciyata, na amince da shari’ar Allah.

23 Amma ina ganin wata ka’ida dabam a gaɓoɓina, wadda take yaƙi da ka’idar da hankalina ya ɗauka, har tana mai da ni bawan ƙa’idar nan ta zunubi wadda take zaune a gaɓoɓina.

24 Kaitona! Wa zai cece ni daga jikin nan, wanda yake kai ni ga mutuwa?

25 Godiya tā tabbata ga Allah, akwai, ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu! Ashe kuwa, ni a kaina, da hankalina, hakika Shari’ar Allah nake bauta wa, amma da jikina ka’idar zunubi nake bauta wa.