ROM 8

Rayuwa a Cikin Ruhu

1 Saboda haka a yanzu, ba sauran kayarwa ga waɗanda suke na Almasihu Yesu.

2 Ka’idar nan ta Ruhu mai ba da rai da yake ga Almasihu Yesu ta ‘yanta ni daga ka’idar zunubi da ta mutuwa.

3 Abin da ba shi yiwuwa Shari’a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi.

4 Wannan kuwa domin a cika hakkokin Shari’a ne a gare mu, mu da ba zaman halin mutuntaka muke yi ba, sai dai na Ruhu.

5 Masu zaman halin mutuntaka, ai, ƙwallafa ransu ga al’amuran halin mutuntaka suke yi, masu zaman Ruhu kuwa ga al’amuran Ruhu.

6 Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga ala’muran Ruhu kuwa rai ne da salama.

7 Don ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka gāba ne da Allah, gama ba ya bin Shari’ar Allah, ba kuwa zai iya ba.

8 Masu zaman halin mutuntaka, ba dama su faranta wa Allah rai.

9 Amma ku kam, ba masu zaman halin mutuntaka ba ne, masu zaman Ruhu ne, in dai har Ruhun Allah yana zaune a zuciyarku. Duk wanda ba shi da Ruhun Almasihu kuwa, ba na Almasihu ba ne.

10 In kuwa Almasihu yana a zuciyarku, ba ruwan jikinku da zunubi ke nan, Ruhu kuwa rai ne a gare ku saboda kun sami adalcin Allah.

11 In kuwa Ruhun wannan da ya ta da Yesu daga matattu yana zaune a zuciyarku, to, shi da ya ta da Almasihu Yesu daga matattu zai kuma raya jikin nan naku mai mutuwa, ta wurin Ruhunsa da yake a zaune a zuciyarku.

12 Domin haka, ‘yan’uwa, kun ga halin mutuntaka ba shi da wani hakki a kanmu har da za mu yi zamansa.

13 In kuna zaman halin mutuntaka, za ku mutu ke nan, amma in da ikon Ruhu kuka kashe ayyukan nan na halin mutuntaka, sai ku rayu.

14 Duk waɗanda Ruhun Allah yake bishe su, su ne ‘ya’yan Allah.

15 Ai, ruhun da kuka samu ba na bauta ba ne, har da za ku koma zaman tsoro. A’a, na zaman ‘ya’ya ne, har muna kira, “Ya Abba! Uba!”

16 Ruhu da Kansa ma, tare da namu ruhu suna yin shaida, cewa mu ‘ya’yan Allah ne.

17 In kuwa ‘ya’ya muke, ashe, magāda ne kuma, magādan Allah, abokan gādo kuma da Almasihu, in dai har muna shan wuya tare da shi, a kuwa ɗaukaka mu tare da shi.

18 Ai, a ganina, wuyar da muke sha a wannan zamani, ba ta isa a kwatanta ta da ɗaukakar da za a bayyana mana ba.

19 Ga shi, duk halitta tana marmari, tana ɗokin ganin bayyanar ‘ya’yan Allah.

20 An sarayar da halitta ta zama banza, ba da nufinta ba, amma da nufin wanda ya sarayar da ita. Duk da haka, akwai sa zuciya,

21 gama za a ‘yantar da halitta da kanta ma, daga bautar ruɓewa, domin ta sami ‘yancin nan, na ɗaukaka na ‘ya’yan Allah.

22 Mun dai san dukan halitta tana nishi, na shan azaba kuma irin ta mai naƙuda, har ya zuwa yanzu.

23 Banda haka ma, har mu kanmu da muka riga muka sami Ruhu Mai Tsarki, wanda yake shi ne nunan fari, a cikin abubuwan da za mu samu, muna nishi a ranmu, muna ɗokin cikar zamanmu na ‘ya’yan Allah, wato, fansar jikin nan namu ke nan.

24 Sa’ad da aka cece mu ne muka yi wannan sa zuciya. Amma kuwa, ai, sa zuciya ga abin da aka samu, ba sa zuciya ba ce. Wa yake sa zuciya ga abin da ya samu?

25 In kuwa muna sa zuciya ga abin da ba mu samu ba, da jimiri mukan yi sauraronsa.

26 Haka kuma Ruhu yake yi mana taimako a kan gajiyawarmu, domin ba mu ma san abin da ya kamata mu roƙa ba, amma Ruhu da kansa yana yi mana roƙo da nishe-nishen da ba su hurtuwa.

27 Amma shi mai fayyace zukatanmu ya san abin da Ruhu yake niyya, domin bisa ga nufin Allah ne Ruhu yake yi wa tsarkaka roƙo.

Mun Zarce A Ce da Mu Masu Nasara Ne

28 Mun kuma sani al’amura duka suna aikatawa tare, zuwa alheri ga waɗanda suke ƙaunar Allah, wato, waɗanda suke kirayayyu bisa ga nufinsa.

29 Waɗanda Allah ya riga ya zaɓa tun tuni, su ne ya ƙaddara su ɗauki kamannin Ɗansa, domin shi Ɗan yă zama na farko a cikin ‘yan’uwa masu yawa.

30 Waɗanda ya ƙaddarar nan kuwa, su ne ya kira. Waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar. Waɗanda ya kuɓutar ɗin kuwa, su ne ya ɗaukaka.

31 To, me kuma za mu ce a game da haka? Da yake Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?

32 Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai ba mu kome tare da shi hannu sake ba?

33 Wa zai ɗora wa zaɓaɓɓun Allah laifi? Allah ne yake kuɓutar da su!

34 Wa zai hukunta su? Almasihu Yesu wanda ya mutu, ko kuwa a ce wanda ya tashi daga matattu, shi ne wanda yake zaune dama ga Allah, shi ne kuwa wanda yake roƙo saboda mu!

35 Wa zai iya raba mu da ƙaunar da Almasihu yake yi mana? Ƙunci ne? ko masifa? ko tsanani? ko yunwa? ko huntanci? ko hatsari? ko takobi?

36 Kamar yadda yake a rubuce cewa,

“Saboda kai ne ake kashe mu yini zubur,

An lasafta mu kamar tumakin yanka.”

37 Duk da haka kuwa a cikin wannan hali duka, har mun zarce ma a ce mana masu nasara, ta wurin wannan da ya ƙaunace mu.

38 Domin na tabbata, ko mutuwa ce, ko rai, ko mala’iku, ko manyan mala’iku, ko al’amuran yanzu, ko al’amura masu zuwa, ko masu iko,

39 ko tsawo, ko zurfi, kai, ko kowace irin halitta ma, ba za su iya raba mu da ƙaunar da Allah yake yi mana ta wurin Almasihu Yesu Ubangijinmu ba.