W. W. 1

Amarya da ‘Yan Matan Urushalima

1 Ga waƙar Sulemanu mafi daɗi.

2 Leɓunanka sun lulluɓe ni da sumba,

Ƙaunarka ta fi ruwan inabi zaƙi.

3 Akwai ƙanshi kuma kewaye da kai,

Jin amon sunanka yana tunasar da ni.

Ba wata matar da za ta ƙi ƙaunarka.

4 Ka ɗauke ni mana, mu gudu,

Ka zama sarkina, ka kai ni ɗakinka.

Da yake kana nan za mu yi farin ciki,

Za mu sha ruwan inabi, mu yi murna da ƙaunarki.

Ya dace a ƙaunace ka!

5 Rana ta sa na zama akawala kyakkyawa.

Matan Urushalima, bisa ga launi, ni ƙasa ƙasa ce,

Kamar alfarwar hamada,

Kamar labulen fādar Sulemanu.

6 Kada ka raina ni saboda launina,

Domin rana ta dafe ni.

‘Yan’uwana suna fushi da ni,

Sun sa ni aiki a gonar inabi.

Ba ni da zarafin da zan lura da kaina.

7 Faɗa mini, ƙaunataccena,

Ina za ka kai garkenka kiwo?

Ina za su huta sa’ad da rana ta take?

Ina zan neme ka a cikin garkunan makiyaya?

8 Mafi kyau cikin mata, ashe, ba ki san wurin ba?

Tafi, ki bi garken,

Ki samar wa awakinki wurin kiwo

Kusa da alfarwan makiyaya.

Amarya da Ango

9 Ke ƙaunatacciyata, kina ɗauke hankalina

Kamar yadda goɗiya take ɗauke hankalin ingarmun karusan Fir’auna.

10 Kitsonki yana da kyau a kumatunki,

Ya sauka a wuyanki kamar lu’ulu’ai.

11 Mu kuma za mu ƙera miki sarƙar zinariya,

A yi miki ado da azurfa.

12 A sa’ad da sarki yake kan kujerarsa,

Yana jin daɗin ƙanshin turarena ƙwarai.

13 Ƙaunataccena yana da ƙanshin mur

Lokacin da yake kwance a ƙirjina.

14 Ƙaunataccena kamar furen jeji yake

Wanda yake huda a gonar inabi a En-gedi.

15 Ke kyakkyawa ce ƙwarai, kyakkyawa ce ke, ya ƙaunatacciyata,

Idonki suna haskaka da ƙauna.

16 Kai kyakkyawa ne ƙwarai, ya ƙaunataccena, kana da bansha’awa.

Koriyar ciyawa ita ce gadonmu.

17 Itatuwan al’ul su ne jigajigan gidanmu,

Itatuwan fir su ne rufin gidan.