W. W. 2

1 Ni fure ce na Sharon,

Furen bi-rana na cikin kwari.

2 Kamar yadda furen bi-rana yake a cikin ƙayayuwa,

Haka ƙaunatacciyata take a cikin sauran mata.

3 Kamar yadda itacen gawasa yake a cikin itatuwan jeji,

Haka ƙaunataccena yake a cikin sauran maza.

Da farin ciki na zauna a inuwarsa,

Ina jin daɗin halinsa ƙwarai.

4 Ya kai ni babban ɗakin da ake liyafa,

Ƙauna ita ce tutarsa a gare ni.

5 Ka ciyar da ni da wainar zabibi,

Ka ba ni ‘ya’yan gawasa in sha in wartsake!

Gama na cika da sha’awarka.

6 Bari ka ta da kaina da hannun hagunka,

Ka rungume ni da hannun damanka.

7 Ku ‘yan matan Urushalima,

Ku rantse da bareyi, da batsiyoyi,

Ba za ku shiga tsakaninmu ba,

Ku bar ta kurum.

8 Na ji muryar ƙaunataccena!

Ya zo a guje daga kan tuddai,

Ya sheƙo daga tuddai zuwa wurina.

9 Ƙaunataccena kamar barewa yake,

Kamar sagarin kishimi.

Ga shi can, yana tsaye a bayan katangarmu.

Yana leƙe ta tagogi,

Yana kallona ta cikin asabari.

10 Ƙaunataccena ya yi magana da ni.

Tashi mu tafi, ƙaunatacciyata, kyakkyawa.

11 Gama lokacin sanyi ya wuce,

Ruwa kuma ya ɗauke.

12 Furanni suna hudowa a itatuwa ko’ina.

Lokacin raira Waƙoƙi ya yi,

Lokacin da kurciyoyi suke kuka ya yi.

13 ‘Ya’yan ɓaure sun nuna,

Tohon inabi yana ƙanshi.

Tashi mu tafi, ƙaunatacciyata, kyakkyawa!

14 Ya kurciyata kina zaune a kogon dutse mai tsayi.

Bari in ga fuskarki, in kuma ji muryarki,

Gama muryarki tana da daɗin ji,

Fuskarki kuma tana da kyan gani.

15 Ku kama mana ‘yan ƙananan diloli

Waɗanda suke ɓata gonakin inabi,

Gama gonakin inabinmu sun yi fure.

16 Ƙaunataccena nawa ne, ni ma tasa ce,

Yana kiwon garkensa a cikin furannin bi-rana,

17 Har hurowar iskar safiya,

Sa’ad da duhu ya kawu.

Komo ya ƙaunataccena, yi kamar barewa,

Kamar sagarin kishimi a kan duwatsu.