W. YAH 15

Mala’iku Masu Bala’i Bakwai

1 Na kuma ga wata alama a Sama, mai girma, mai banmamaki, mala’iku bakwai masu bala’i bakwai, waɗanda suke bala’in ƙarshe, don su ne iyakacin fushin Allah.

2 Sai na ga wani abu kamar bahar na gilas, gauraye da wuta, na kuma ga waɗanda suka yi nasara da dabbar nan, da siffarta, da kuma lambar sunanta, a tsaitsaye a bakin bahar na gilas, da molayen yabon Allah a hannunsu.

3 Suna raira waƙar da Musa bawan Allah ya yi, da kuma wadda ake yi wa Ɗan Ragon nan, suna cewa,

“Ayyukanka manya ne, masu banmamaki,

Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki!

Hanyoyinka na adalci ne, na gaskiya ne kuma,

Ya Sarkin al’ummai.

4 Wane ne ba zai ji tsoronka ba, ya Ubangiji,

Ya kuma ɗaukaka sunanka?

Domin kai kaɗai ne Mai Tsarki.

Dukkan al’ummai za su zo su yi maka sujada,

Don ayyukanka na adalci sun bayyana.”

5 Bayan wannan na duba, ga Wuri Mafi Tsarki a buɗe a Haikali a Sama.

6 Sai mala’ika bakwai ɗin nan masu bala’i bakwai suka fito daga Haikalin, saye da tufafin lilin mai tsabta, mai ɗaukar iko, da ɗamarar zinariya a ƙirjinsu.

7 Sai ɗaya daga cikin rayayyun halittan nan guda huɗu, ta ba mala’ikun nan bakwai tasoshi bakwai na zinariya, a cike da fushin Allah, shi da yake a raye har abada abadin.

8 Sai Haikalin ya cika da hayaƙi mai fitowa daga ɗaukakar Allah da ikonsa. Ba mai iya shiga Haikalin nan, sai bayan bala’i bakwai na mala’ikun nan bakwai sun ƙare.