W. YAH 16

Tasoshin Azaba

1 Sai na ji wata murya mai ƙara daga Haikalin, tana ce wa mala’ikun nan bakwai, “Ku je ku juye tasoshin nan bakwai na fushin Allah a kan duniya.”

2 Daga nan mala’ikan farko ya je ya juye abin da yake a tasarsa a kan duniya, sai kuwa waɗansu mugayen miyaku masu azabtarwa suka fito a jikin mutanen da suke da alamar dabbar nan, suke kuma yi wa siffarta sujada.

3 Mala’ika na biyu ya juye abin da yake a tasarsa a teku, ya zama kamar jinin mataccen mutum, kowane abu mai rai na cikin teku kuma ya mutu.

4 Mala’ika na uku ya juye abin da yake a tasarsa a koguna da maɓuɓɓugan ruwa, sai suka zama jini.

5 Na kuwa ji mala’ikan ruwa yana cewa,

“Kai mai adalci ne a hukuncin nan naka,

Ya kai Mai Tsarki, wanda kake a yanzu, kake kuma a dā.

6 Don mutane sun zub da jinin tsarkaka da na annabawa,

Ga shi kuwa, ka ba su jini su sha.

Sakamakonsu ke nan!”

7 Sai na ji wata murya a bagadin ƙona turare, tana cewa,

“Hakika, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki,

Hukuncinka daidai yake, na adalci ne kuma!”

8 Sai mala’ika na huɗu ya juye abin da yake a tasarsa a rana, sai aka yardar mata ta ƙona mutane da wuta.

9 Sai matsanancin zafi ya ƙona mutane, har suka zagi sunan Allah, shi da yake da ikon waɗannan bala’i, ba su kuwa tuba sun ɗaukaka shi ba.

10 Mala’ika na biyar ya juye abin da yake a tasarsa a kursiyin dabbar nan, sai mulkinta ya zama duhu, har mutane suka ciji leɓunansu don azaba,

11 suka zagi Allah Mai Sama saboda azabarsu da miyakunsu, ba su kuma tuba da ayyukansu ba.

12 Mala’ika na shida ya juye abin da yake a tasarsa a babban kogin nan Yufiretis, sai ruwansa ya ƙafe, don a shirya wa sarakuna daga gabas tafarki.

13 Na kuma ga baƙaƙen aljannu masu kama da kwaɗi gudu uku, suna fitowa daga bakin macijin nan, da bakin dabbar nan, da kuma bakin annabin nan na ƙarya,

14 su iskoki ne, aljannu masu yin abubuwan al’ajabi, masu zuwa wurin sarakunan duniya duka, don su tara su saboda yaƙi a babbar ranar nan ta Allah Maɗaukaki.

15 (“Ga ni nan a tafe kamar ɓarawo! Albarka tā tabbata ga wanda yake a zaune a faɗake, yana saye da tufafinsa, don kada ya tafi tsirara, a ga tsiraicinsa.”)

16 Sai suka tattara su a wurin da ake kira Armageddon da Yahudanci.

17 Mala’ika na bakwai ya juye abin da yake a tasarsa a sararin sama, sai aka ji wata murya mai ƙara daga Haikali, wato, daga kursiyin, ta ce, “An gama!”

18 Sai aka yi ta walƙiya, da ƙararraki masu tsanani, da aradu, da wata babbar rawar ƙasa irin wadda ba a taɓa yi ba, tun da ɗan adam yake a duniya, gawurtacciyar rawar ƙasa ƙwarai da gaske.

19 Babban birnin nan kuwa ya rabu gida uku, biranen al’ummai kuma suka fāɗi. Sai Allah ya tuna da Babila mai girma, don ya sa ta, ta sha fushinsa mai tsananin gaske.

20 Kowane tsibiri ya ɓace, manyan duwatsu ma ba a ƙara ganinsu ba.

21 Waɗansu manyan ƙanƙara kuma kamar kayan jaki suka faɗo a kan mutane daga sama, har mutane suka zagi Allah, saboda bala’in ƙanƙarar. Bala’in nan da matuƙar bantsoro yake!