W. YAH 17

Hukunta Babbar Karuwar

1 Sai ɗaya daga cikin mala’ikun nan bakwai masu tasoshin nan bakwai, ya zo ya yi mini magana, ya ce, “Zo in nuna maka hukuncin da za a yi wa babbar karuwar nan, wadda take zaune a bisa ruwa mai yawa,

2 wadda sarakunan duniya suka yi fasikanci da ita, wadda kuma mazaunan duniya suka jarabtu da yin fasikanci da ita.”

3 Sai ya ɗauke ni ya tafi da ni zuwa jeji, Ruhu yana iza ni, sai na ga wata mace a kan wata dabba ja wur, duk jikin dabbar sunayen saɓo ne, tana kuma da kawuna bakwai, da ƙaho goma.

4 Matar kuwa tana saye da tufafi masu ruwan jar garura, da kuma ja wur, ta ci ado da kayan zinariya, da duwatsun alfarma, da lu’ulu’u, tana a riƙe da ƙoƙon zinariya a hannunta, cike da abubuwan ƙyama, da ƙazantar fasikancinta.

5 A goshinta kuma an rubuta wani sunan asiri, “Babila mai girma, uwar karuwai, uwar abubuwa masu banƙyama na duniya.”

6 Sai na ga matar ta bugu da jinin tsarkaka, da kuma jinin mashaidan Yesu.

Da na gan ta, sai na yi mamaki ƙwarai da gaske.

7 Amma mala’ikan ya ce mini, “Don me kake mamaki? Zan buɗa maka asirin matar nan, da kuma na dabbar nan mai kawuna bakwai, da ƙaho goma, da take ɗauke da ita.

8 Dabbar nan da ka gani, wadda dā take nan, a yanzu kuwa ba ta, za ta hawo ne daga ramin mahallaka, ta je ta hallaka, mazaunan duniya kuma waɗanda tun a farkon duniya, ba a rubuta sunayensu a Littafin Rai ba, za su yi mamakin ganin dabbar, don dā tana nan, a yanzu ba ta, za ta kuma dawo.

9 Fahimtar wannan abu kuwa, sai a game da hikima. Wato, kawuna bakwai ɗin nan tuddai ne guda bakwai, waɗanda matar take a zaune a kai.

10 Har wa yau kuma, sarakuna ne guda bakwai, waɗanda biyar daga cikinsu aka tuɓe, ɗaya yana nan, ɗayan bai zo ba tukuna, sa’ad da ya zo kuwa, lalle zamaninsa na lokaci kaɗan ne kawai.

11 Dabbar da take nan dā, a yanzu kuwa ba ta, ita ce ta takwas, daga cikin bakwai ɗin nan kuma ta fito, za ta kuwa hallaka.

12 Ƙahonin nan goma kuwa da ka gani, sarakuna goma ne, waɗanda ba a naɗa ba tukuna, amma sa’a ɗaya tak, za a ba su ikon yin mulki tare da dabbar.

13 Waɗannan ra’ayinsu ɗaya ne, za su kuma bai wa dabbar nan ikonsu da sarautarsu.

14 Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, Ɗan Ragon kuwa zai cinye su, shi da waɗanda suke tare da shi, kirayayyu, zaɓaɓɓu, amintattu, domin shi ne Ubangijin iyayengiji.”

15 Sai mala’ikan nan ya ce mini, “Ruwan nan da ka gani, a inda karuwar nan take a zaune, jama’a ce iri iri, da taro masu yawa, da al’ummai, da harsuna.

16 Ƙahonin nan goma kuma da ka gani, wato, su da dabbar nan za su ƙi karuwar, su washe ta, su tsiraita ta, su ci namanta, su ƙone ta,

17 domin Allah ya nufe su da zartar da nufinsa, su zama masu ra’ayi ɗaya, su bai wa dabbar nan, mulkinsu, har a cika Maganar Allah.

18 Matar nan da ka gani kuwa, ita ce babban birnin da yake mulkin sarakunan duniya.”