W. YAH 19

1 Bayan wannan na ji kamar wata sowa mai ƙarfi ta ƙasaitaccen taro a Sama, suna cewa,

“Halleluya! Yin ceto, da ɗaukaka, da iko, sun tabbata ga Allahnmu,

2 Don hukuncinsa daidai yake, na adalci ne,

Ya hukunta babbar karuwar nan wadda ta ɓata duniya da fasikancinta,

Ya kuma ɗauki fansar jinin bayinsa a kanta.”

3 Sai suka sāke yin sowa, suna cewa,

“Halleluya! Hayaƙinta yana tashi har abada abadin.”

4 Sai dattawan nan ashirin da huɗu, da rayayyun halittan nan huɗu, suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, shi da yake zaune a kan kursiyin, suna cewa, “Amin. Halleluya!”

5 Sai aka ji wata murya daga kursiyin, tana cewa,

“Ku yabi Allahnmu, ya ku bayinsa,

Ku da kuke jin tsoronsa, yaro da babba.”

Bikin Auren Ɗan Rago

6 Sai na ji kamar wata sowar ƙasaitaccen taro, kamar ƙugin ruwa mai gudu, kamar aradu mai ƙara, suna cewa,

“Halleluya! Gama Ubangiji Allahnmu

Maɗaukaki shi ne yake mulki.

7 Mu yi ta murna da farin ciki matuƙa,

Mu kuma ɗaukaka shi,

Domin bikin Ɗan Ragon nan ya zo,

Amaryarsa kuma ta kintsa.

8 An yardar mata ta sa tufafin lallausan lilin

mai ɗaukar ido, mai tsabta.”

Lallausan lilin ɗin nan, shi ne aikin adalci na tsarkaka.

9 Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta wannan, ‘Albarka tā tabbata ga waɗanda aka gayyata, zuwa cin abincin bikin Ɗan Ragon nan.’ ” Ya kuma ce mini, “Wannan ita ce Maganar Allah ta gaskiya.”

10 Sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada, amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da ‘yan’uwanka, waɗanda suke shaidar Yesu. Allah za ka yi wa sujada.” Domin gaskiyar da Yesu ya bayyana ita ce ta ba da ikon yin annabci.

Mahayin Farin Doki

11 Sai na ga sama ta dāre, sai ga wani farin doki! Mahayinsa kuwa ana ce da shi Amintacce, Mai Gaskiya, yana hukunci da adalci, yana kuma yaƙi.

12 Idanunsa kamar harshen wuta suke, kansa da kambi da yawa, yana kuma da wani suna a rubuce, wanda ba wanda ya sani sai shi.

13 Yana saye da riga wadda aka tsoma a jini, sunan da ake kiransa da shi kuma, shi ne Kalman Allah.

14 Rundunonin Sama, saye da lallausan lilin fari mai tsabta, suna a biye da shi a kan fararen dawakai.

15 Daga cikin bakinsa wani kakkaifan takobi yake fitowa, wanda zai sare al’ummai da shi, zai kuwa mallake su da tsanani ƙwarai, zai tattake mamatsar inabi, ta tsananin fushin Allah Maɗaukaki.

16 Da wani suna a rubuce a jikin rigarsa, har daidai cinyarsa, wato Sarkin sarakuna, Ubangijin iyayengiji.

17 Sa’an nan na ga wani mala’ika tsaye a jikin rana. Sai kuma ya kira dukkan tsuntsaye da suke tashi a sararin sama, da murya mai ƙarfi, ya ce, “Ku zo, ku taru wurin babban bikin nan na Allah,

18 ku ci naman sarakuna, da naman sarakunan yaƙi, da naman ƙarfafa, da naman dawakai, da na mahayansu, da naman kowa da kowa, wato, na ɗa da na bawa, na yaro da na babba.”

19 Sai na ga dabbar nan, da sarakunan duniya, da rundunoninsu, sun taru, don su yaƙi wanda yake kan dokin, da kuma rundunarsa.

20 Sai aka kama dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al’ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.

21 Sauran kuwa aka sare su da takobin wanda yake a kan doki, wato, da takobin nan da yake fitowa daga cikin bakinsa. Dukan tsuntsaye kuwa suka ci namansu har suka yi gamba.