W. YAH 20

Shekara Dubu

1 Sa’an nan na ga wani mala’ika yana saukowa daga Sama, yana a riƙe da mabuɗin mahallaka, da kuma wata babbar sarƙa a hannunsa.

2 Sai ya kama macijin nan, wato, macijin nan na tun dā dā, wanda yake shi ne Ibilis, shi ne kuma Shaiɗan, ya ɗaure shi har shekara dubu,

3 ya jefa shi mahallakar, ya rufe, ya kuma yimƙe ta da hatimi, don kada ya ƙara yaudarar al’ummai, har dai shekarun nan dubu su ƙare. Bayan wannan lalle ne a sake shi zuwa ɗan lokaci kaɗan.

4 Sa’an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.

5 Sauran matattu kuwa, ba su sāke rayuwa ba, sai bayan da shekaran nan dubu suka cika. Wannan fa shi ne tashin matattu na farko.

6 Duk wanda yake da rabo a tashin nan na farko, mai albarka ne, tsattsarka ne. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kan irin waɗannan, amma za su zama firistocin Allah da na Almasihu, su kuma yi mulki tare da shi har shekara dubu.

7 Bayan shekaran nan dubu sun ƙare, sai a saki Shaiɗan daga ɗaurinsa,

8 ya kuma fito ya yaudari al’ummai waɗanda suke kusurwoyin nan huɗu na duniya, wato, Gog da Magog, ya tattara su saboda yaƙi, yawansu kamar yashin teku.

9 Sai kuma su bazu, su mamaye duk duniya, su yi wa sansanin tsarkaka da ƙaunataccen birni ƙawanya, sai wuta ta zubo daga sama ta lashe su.

10 Shi kuwa Ibilis mayaudarinsu, sai da aka jefa shi a tafkin wuta da ƙibiritu, a inda dabbar nan da annabin nan na ƙarya suke, za a kuma gwada musu azaba dare da rana har abada abadin.

Ranar Shari’a a Gaban Babban Farin Kursiyi

11 Sa’an nan na ga wani babban kursiyi fari, da wanda yake a zaune a kai, sai sama da ƙasa suka guje wa Zatinsa, suka ɓace.

12 Sai na ga matattu manya da yara, a tsaitsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Sai kuma aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne Littafin Rai. Aka kuwa yi wa matattu shari’a bisa ga abin da yake a rubuce a cikin littattafan, gwargwadon aikin da suka yi.

13 Sai teku ta ba da matattun da suke a cikinta, mutuwa da Hades kuma sun ba da matattun da suke a gare su, aka kuwa yi wa kowa shari’a gwargwadon aikin da ya yi.

14 Sa’an nan aka jefa mutuwa da Hades a tafkin nan na wuta. Wannan ita ce mutuwa ta biyu, wato, tafkin wuta.

15 Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a Littafin Rai ba, sai a jefa shi a tafkin nan na wuta.