YAH 10

Misali na Garken Tumaki

1 “Lalle hakika, ina gaya muku, wanda bai shiga garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya haura ta wani gu, to, shi ɓarawo ne, ɗan fashi kuma.

2 Wanda kuwa ya shiga ta ƙofar, makiyayin tumakin ne.

3 Mai tsaron ƙofar yakan buɗe masa, tumakin kuma sukan saurari murya tasa, yakan kama sunan nasa tumaki, ya kai su waje.

4 Bayan ya fitar da dukan nasa waje, sai ya shige gabansu, tumakin na biye da shi, domin sun san murya tasa.

5 Ba za su bi baƙo ba, sai dai su guje shi, don ba su san muryar baƙo ba.”

6 Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su gane abin da ya faɗa musu ba.

Yesu Ne Makiyayi Mai Kyau

7 Don haka Yesu ya sāke ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ni ne ƙofar tumakin.

8 Duk waɗanda suka riga ni zuwa cewa, su ne ni, ɓarayi ne, ‘yan fashi kuma, amma tumakin ba su kula da su ba.

9 Ni ne ƙofar. Kowa ya shiga ta wurina zai sami ceto, ya kai ya kawo, ya kuma yi kiwo.

10 Ɓarawo yakan zo ne kawai don sata da kisa da hallakarwa. Ni kuwa na zo ne domin su sami rai, su kuma same shi a yalwace.

11 Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau kuwa shi ne mai ba da ransa domin tumakin.

12 Wanda yake ɗan asako kuwa, ba makiyayin gaske ba, tumakin kuma ba nasa ba, da ganin kyarkeci ya doso, sai ya watsar da tumakin, ya yi ta kansa, kyarkeci kuwa ya sure waɗansu, ya fasa sauran.

13 Ya gudu ne fa, don shi ɗan asako ne, ba abin da ya dame shi da tumakin.

14 Ni ne Makiyayi mai kyau. Na san nawa, nawa kuma sun san ni,

15 kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uban. Ina ba da raina maimakon tumakin.

16 Ina kuma da waɗansu tumaki da ba na wannan garke ba ne. Su ma lalle in kawo su, za su kuwa saurari muryata, su zama garke guda, makiyayi kuma guda.

17 Domin wannan uba yake ƙaunata, domin ina ba da raina in ɗauko shi kuma.

18 Ba mai karɓe mini rai, don kaina nake ba da shi. Ina da ikon ba da shi, ina da ikon ɗauko shi kuma. Na karɓo wannan umarni ne daga wurin Ubana.”

19 Saboda maganan nan fa, sai rabuwa ta sāke shiga tsakanin Yahudawa.

20 Da yawa daga cikinsu suka ce, “Ai, mai iska ne, haukansa kawai yake yi. Don me za ku saurare shi?”

21 Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, wannan magana, ai, ba ta mai iska ba ce. Ashe, iska tana iya buɗe wa makaho ido?”

Yahudawa Sun Ƙi Yesu

22 Lokacin idin tsarkakewa ne kuwa a Urushalima,

23 damuna ce kuma, Yesu kuwa na zagawa a Shirayin Sulemanu cikin Haikali,

24 sai Yahudawa suka kewaye shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In dai kai ne Almasihun, ka gaya mana a fili.”

25 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, na faɗa muku, ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi da sunan Ubana, suke shaidata.

26 Amma ku ba ku gaskata ba, domin ba kwa cikin tumakina.

27 Tumakin nan nawa sukan saurari muryata, na san su, suna kuma bi na.

28 Ina ba su rai madawwami, ba kuwa za su halaka ba har abada, ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.

29 Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba kuwa mai iya ƙwace su daga ikon Uban.

30 Ni da Uba ɗaya muke.”

31 Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu su jajjefe shi.

32 Yesu ya amsa musu ya ce, “Na nuna muku ayyuka nagari masu yawa daga wurin Uba, a kan wanne a cikinsu za ku jajjefe ni?”

33 Yahudawa suka amsa suka ce, “Ba don wani aiki nagari za mu jajjefe ka ba, sai don sāɓo, don kai, ga ka mutum, amma kana mai da kanka Allah.”

34 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a Shari’arku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’?

35 To, in waɗanda Maganar Allah ta zo musu ya ce da su alloli (Nassi kuwa ba ya tashi),

36 kwa ce da wanda Uba ya keɓe, ya kuma aiko duniya, ‘Sāɓo kake,’ domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne’?

37 In ba ayyukan da Ubana yake yi nake yi ba, to, kada ku gaskata ni.

38 Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uba na cikina, ni kuma ina cikin Uba.”

39 Sai suka sāke ƙoƙarin kama shi, amma ya fita daga hannunsu.

40 Sa’an nan ya sāke komawa hayin Kogin Urdun, wurin da Yahaya ya fara yin baftisma, ya zauna a can,

41 mutane kuwa da yawa suka zo wurinsa, sai suka riƙa cewa, “Hakika, Yahaya bai yi wata mu’ujiza ba, amma duk abin da ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.”

42 Nan fa mutane da yawa suka gaskata da shi.