YAH 9

Warkar da Wanda aka Haifa Makaho

1 Yesu na wucewa sai ya ga wani mutum da aka haifa makaho.

2 Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Ya Shugaba, wa ya yi zunubi da aka haifi mutumin nan makaho, shi, ko iyayensa?”

3 Yesu ya amsa ya ce, “Ba domin mutumin nan ko iyayensa sun yi zunubi ba, sai domin a nuna aikin Allah ne a kansa.

4 Lalle ne mu yi aikin wanda ya aiko ni tun da sauran rana. Ai, dare zai yi sa’ad da ba mai iya aiki.

5 Muddin ina duniya ni ne hasken duniya.”

6 Da ya faɗi haka sai ya tofa yau a ƙasa, ya cuɗa ƙasa, ya shafa a idanun makahon,

7 ya ce masa, “Je ka, ka wanke ido a ruwan Siluwam,” wato aikakke. Shi ke nan sai ya je ya wanke ido, ya komo yana gani.

8 Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Ashe, ba wannan ne yakan zauna yana bara ba?”

9 Waɗansu suka ce, “Shi ne mana.” Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, kai dai, sun yi kama.” Shi kuwa ya ce, “Sosai ni ne!”

10 Sai suka ce masa, “To, ƙaƙa aka yi idanunka suka buɗe?”

11 Ya amsa ya ce, “Mutumin nan da ake kira Yesu ne ya cuɗa ƙasa ya shafa mini a idanu, ya ce mini, ‘Je ka Siluwam ka wanke ido.’ Na kuwa je na wanke, sai na sami gani.”

12 Suka ce masa, “Ina yake?” Ya ce, “Ban sani ba.”

Farisiyawa Sun Bincika Labarin Wanda aka Warkar

13 Sai suka kai wa Farisiyawa mutumin da yake makaho a dā.

14 To, ran Asabar ne Yesu ya cuɗa ƙasar ya buɗe masa ido.

15 Farisiyawa ma suka tambaye shi ta yadda aka yi ya sami gani. Ya ce musu, “Cuɗaɗɗiyar ƙasa ya shafa a idona, na wanke, ina gani.”

16 Saboda haka, waɗansu Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye Asabar.” Waɗansu kuwa suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai iya yin mu’ujizai haka?” Sai rabuwa ta shiga tsakaninsu.

17 Sai suka sāke ce wa makahon, “To, kai fa, me ka gani game da shi, da yake kai ya buɗe wa ido?” Ya ce, “Ai, annabi ne.”

18 Yahudawa kam, ba su gaskata shi makaho ne a dā ba, ya kuma sami gani, har suka kira iyayen wanda ya sami ganin,

19 suka tambaye su suka ce, “Wannan ɗanku ne da kuke cewa an haife shi makaho? To, ta yaya yake iya gani yanzu?”

20 Sai iyayen nasa suka amsa suka ce, “Mun dai san wannan ɗanmu ne, makaho ne aka haife shi.

21 Amma ta yadda aka yi yake gani yanzu ba mu sani ba, ba mu ma san wanda ya buɗe idon ba. Ku tambaye shi, ai, ba yaro ba ne, zai faɗa da bakinsa.”

22 Iyayensa sun faɗi haka ne don tsoron Yahudawa, don dā ma Yahudawa sun ƙulla, cewa kowa ya amsa, cewa shi ne Almasihu, za a fisshe shi daga jama’a.

23 Shi ya sa iyayensa suka ce, “Ai, ba yaro ba ne, ku tambaye shi.”

24 Sai suka sāke kiran mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka tsoraci Allah dai! Mu kam, mun san mutumin nan mai zunubi ne.”

25 Sai ya amsa ya ce, “Ko mai zunubi ne, ni ban sani ba. Abu ɗaya kam, na sani, dā ni makaho ne, yanzu kuwa ina gani.”

26 Sai suka ce masa, “Shin, me ya yi maka? Ta yaya ya buɗe maka ido?”

27 Ya amsa musu ya ce, “Na riga na faɗa muku, ba ku ji ba. Don me kuke so ku sāke ji? Ko ku ma kuna so ku zama almajiransa ne?”

28 Sai suka fāɗa shi da zagi, suna cewa, “Kai ne dai almajirin wannan ɗin, mu kam, almajiran Musa ne.

29 Mun dai sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan ba mu san ta inda ya fito ba.”

30 Sai mutumin ya amsa musu ya ce, “Yau ga abin mamaki! Ashe, ba ku san ta inda ya fito ba, ga shi kuwa, ya buɗe mini ido!

31 Mun sani Allah ba ya sauraron masu zunubi, amma duk wanda yake mai bautar Allah, yake kuma aikata nufinsa, Allah yakan saurare shi.

32 Tun da aka fara duniya ba a taɓa jin wani ya buɗe idon wanda aka haifa makaho ba.

33 Da mutumin nan ba daga Allah ya fito ba, da ba abin da zai iya yi.”

34 Suka amsa masa suka ce, “Kai da aka haifa a baƙin zunubi ne za ka koya mana?” Sai suka kore shi.

Makanta ta Ruhu

35 Yesu ya ji labari sun kore shi. Da ya same shi, ya ce, “Ka gaskata da Ɗan Mutum ko?”

36 Ya amsa ya ce, “Wane ne shi, ya Shugaba, da zan gaskata da shi?”

37 Yesu ya ce masa, “Ai, ka gan shi, shi ne ma mai magana da kai.”

38 Sai ya ce, “Ya Ubangiji, na ba da gaskiya,” ya kuma yi masa sujada.

39 Yesu ya ce, “Na shigo duniyan nan ne don rarrabewa, domin waɗanda ba sa gani su gani, waɗanda suke gani kuma su makance.”

40 Da Farisiyawan nan da suke tare da shi suka ji haka, suka ce masa, “Wato mu ma makafi ne?”

41 Yesu ya ce musu, “Ai, da makafi ne ku, da ba ku da zunubi. Amma da yake kun ce kuna gani, to, zunubinku ya tabbata.