YAH 12

An Shafi Yesu da Man Ƙanshi a Betanya

1 Idin Ƙetarewa sauran kwana shida, sai Yesu ya zo Betanya inda Li’azaru yake, wanda Yesu ya tasa daga matattu.

2 Nan aka yi masa abincin dare, Marta ce ta yi hidima, Li’azaru kuwa yana cikin masu ci tare da shi.

3 Sai Maryamu ta ɗauko awo guda na man ƙanshi na nardi tsantsa, mai tamanin gaske, ta shafa a ƙafafun Yesu, sa’an nan ta shafe su da gashinta. Duk gidan ya game da ƙanshin man.

4 Amma Yahuza Iskariyoti, ɗaya daga cikin almajiransa, wato wanda zai bāshe shi, ya ce,

5 “Me ya hana a sayar da man nan a kan dinari ɗari uku, a ba talakawa kuɗin?”

6 Ya faɗi haka fa, ba wai don yana kula da gajiyayyu ba, a’a, sai dai don shi ɓarawo ne, da yake kuma jakar kuɗinsu tana hannunsa, yakan riƙa taɓa abin da yake ciki.

7 Sai Yesu ya ce, “A ƙyale ta, dā ma ta ajiye shi domin tanadin ranar jana’izata.

8 Ai, kullum kuna tare da gajiyayyu, amma ba kullum kuke tare da ni ba.”

An Ƙulla Shawara Gāba da Li’azaru

9 Da taron Yahudawa mai yawa suka ji labari yana nan, sai suka zo, ba domin Yesu kaɗai ba, har ma don su ga Li’azaru wanda ya tasa daga matattu.

10 Sai manyan firistoci suka yi shawarar kashe Li’azaru, shi ma,

11 domin ta dalilinsa Yahudawa da yawa suke warewa, suna gaskatawa da Yesu.

Mutanen Urushalima Sun Marabci Yesu

12 Kashegari babban taron da suka zo idi, da suka ji Yesu yana zuwa Urushalima,

13 suka ɗaɗɗauko gazarin dabino suka firfita taryensa, suna ta da murya suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji, Sarkin Isra’ila!”

14 Da Yesu ya sami wani jaki sai ya hau, yadda yake a rubuce cewa,

15 “Kada ki ji tsoro, ya ke ‘yar Sihiyona,

Ga sarkinki na zuwa a kan aholakin jaki!”

16 Da fari almajiransa ba su gane abin nan ba, amma bayan an ɗaukaka Yesu, suka tuna abin nan a rubuce yake game da shi, har ma aka yi masa shi.

17 Taron da yake tare da shi sa’ad da ya kira Li’azaru yă fito daga kabari, ya tashe shi daga matattu, su suka riƙa shaidarwa da haka.

18 Shi ya sa taron suka fita taryensa, don sun ji ya yi mu’ujizan nan.

19 Sai Farisiyawa suka ce wa juna, “Kun ga! Ba abin da muka iya! Ai, duk duniya tana bayansa.”

Waɗansu Helenawa Sun Nemi Yesu

20 To, a cikin waɗanda suka zo idin yin sujada akwai waɗansu Helenawa.

21 Sai suka zo wurin Filibus, mutumin Betsaida ta ƙasar Galili, suka roƙe shi suka ce, “Maigida, muna bukatar mu gana da Yesu.”

22 Sai Filibus ya je ya gaya wa Andarawas, Andarawas kuma ya zo da Filibus, suka gaya wa Yesu.

23 Yesu ya amsa musu ya ce, “Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum.

24 Lalle hakika, ina gaya muku, in ba an binne ƙwayar alkama ta mutu ba, za ta zauna ita kaɗai. Amma in ta mutu sai ta hayayyafa.

25 Mai ƙaunar ransa zai rasa shi. Wanda kuwa ya ƙi ransa a duniyan nan, ya kiyaye shi ke nan, har ya zuwa rai madawwami.

26 Wanda duk zai bauta mini, ya bi ni. Inda nake kuma, nan bawana zai kasance shi ma. Kowa yake bauta mini, Uba zai girmama shi.”

Lalle a Ɗaga Ɗan Mutum Sama

27 “Yanzu ina jin nauyi a raina. Me zan ce kuwa? In ce, ‘Ya Uba ka ɗauke mini wannan lokaci’? A’a, ai, dā ma na zo ne takanas domin wannan lokaci.

28 Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi,”

29 Da taron da yake tsaye a wurin suka ji muryar, suka ce, “An yi cida.” Waɗansu kuwa suka ce, “Wani mala’ika ne ya yi masa magana.”

30 Yesu ya amsa ya ce, “Ba saboda ni aka yi wannan muryan nan ba, sai dominku.

31 Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shari’a, yanzu ne kuma za a tuɓe mai mulkin duniyan nan.

32 Ni kuwa bayan an ɗaga ni daga ƙasa zan ja dukan mutane gare ni.”

33 Ta faɗar haka ya kwatanta irin mutuwar da zai yi.

34 Sai taron suka amsa masa suka ce, “Shari’armu ta gaya mana, cewa Almasihu zai tabbata har abada. To, yaya za ka ce lalle ne a ɗaga Ɗan Mutum? Wane ne Ɗan Mutum ɗin?”

35 Yesu ya ce musu, “Haske na tare da ku har ɗan lokaci kaɗan na gaba. Ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya ci muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda yake tafiya ba.

36 Ku gaskata da hasken, tun kuna tare da shi, domin ku zama mutanen haske.”

Yahudawa Ba Su Gaskata da Shi Ba

Yesu ya faɗi haka, sa’an nan ya tafi ya ɓuya musu.

37 Amma ko da yake ya sha yin mu’ujizai da yawa a gabansu, duk da haka, ba su gaskata shi ba,

38 domin a cika faɗar Annabi Ishaya cewa,

“Ya Ubangiji, wa ya gaskata jawabinmu?

Ga wa kuma aka bayyana ikon Ubangiji?”

39 Shi ya sa ba su iya ba da gaskiya ba. Domin Ishaya ya sāke cewa,

40 “Ya makantar da su, ya kuma taurarar da zuciya tasu,

Kada su gani da idanunsu, su kuma gane a zuci,

Har su juyo gare ni in warkar da su.”

41 Ishaya ya faɗi haka saboda ya ga ɗaukakar Almasihu, ya kuma ba da labarinsa.

42 Duk da haka, da yawa har daga cikin shugabanni ma suka gaskata da shi, amma saboda tsoron Farisiyawa, ba su bayyana ba, don kada a fisshe su daga jama’a.

43 Don sun fi ƙaunar girmamawar mutane da girmamawar Allah.

Maganar Yesu Za ta Yi Hukunci

44 Sai Yesu ya ɗaga murya ya ce, “Wanda yake gaskatawa da ni, ba da ni yake gaskatawa ba, amma ga wanda ya aiko ni ne.

45 Wanda kuma yake dubana, yana duban wanda ya aiko ni ne.

46 Na zo duniya a kan ni haske ne, domin duk mai gaskatawa da ni kada ya yi zaman duhu.

47 Kowa ya ji maganata, bai kuwa kiyaye ta ba, ba ni nake hukunta shi ba. Gama ba don yi wa duniya hukunci na zo ba, sai dai domin in ceci duniya.

48 Wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi maganata ba, yana da mai hukunta shi, maganar da na faɗa, ita za ta hukunta shi a ranar ƙarshe.

49 Ba kuwa domin kaina na yi magana ba, Uban da ya aiko ni shi kansa ya ba ni umarni a kan abin da zan faɗa, da kuma maganar da zan yi.

50 Na kuma san umarnin nan nasa rai ne madawwami. Domin haka, abin da nake faɗa ina faɗa ne daidai yadda Uba ya faɗa mini.”