YAH 13

Yesu Ya Wanke Ƙafafun Almajiransa

1 Ana nan tun kafin Idin Ƙetarewa, da Yesu ya san lokacinsa ya yi da zai tashi daga wannan duniya ya koma wurin Uba, da yake ya ƙaunaci mutanensa da suke duniya, ya ƙaunace su har matuƙa.

2 Ana cikin cin abincin dare, Iblis kuwa ya riga ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti ɗan Saminu yă bāshe shi.

3 Yesu kuwa, da yake ya san Uba ya sa kome a hannunsa, ya kuma sani daga wurin Allah ya fito, wurin Allah kuma zai koma,

4 sai ya tashi daga cin abincin, ya ajiye mayafinsa, ya ɗauko ɗan zane ya yi ɗamara da shi.

5 Sa’an nan ya zuba ruwa a daro, ya fara wanke ƙafafun almajiran, yana shafe su da abin da ya yi ɗamara da shi.

6 Sai ya zo kan Bitrus, shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ashe, kai ne za ka wanke mini ƙafa?”

7 Yesu ya amsa ya ce, “Yanzu kam, ba ka san abin da nake yi ba, amma daga baya za ka fahimta.”

8 Bitrus ya ce masa, “Wane ni! Ai, ba za ka wanke mini ƙafa ba har abada!” Yesu ya amsa masa ya ce, “In ban wanke maka ba, ba ka da rabo a gare ni.”

9 Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba ma ƙafafuna kaɗai ba, har ma da hannuwana da kaina!”

10 Yesu ya ce masa, “Wanda ya yi wanka ba ya bukatar wanke kome, sai ƙafafunsa kawai, domin ya riga ya tsarkaka sarai. Ku ma tsarkakakku ne, amma ba dukanku ne ba.”

11 Don ya san wanda zai bāshe shi, shi ya sa ya ce, “Ba dukanku ne tsarkakakku ba.”

12 Bayan ya wanke ƙafafunsu, ya yafa mayafinsa, sai ya sāke kishingiɗa, ya ce musu, “Kun gane abin da na yi muku?

13 Kuna kirana Malam, da kuma Ubangiji. Daidai ne kuwa, don haka nake.

14 Tun da yake ni Ubangijinku da kuma Malaminku, har na wanke muku ƙafa, ashe, ku ma wajibi ne ku wanke wa juna.

15 Na yi muku ishara domin ku ma ku yi yadda na yi muku

16 Lalle hakika, ina gaya muku, bawa ba ya fin ubangijinsa, manzo kuma ba ya fin wanda ya aiko shi.

17 In dai kun san wannan, kuna kuma aikatawa, ku masu farin ciki ne.

18 Ba dukanku nake nufi ba. Na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa duk domin a cika Nassi ne cewa, ‘Wanda yake cin abincina ya tasar mini.’

19 Tun yanzu zan sanar da ku abu tun bai faru ba, domin sa’ad da ya faru ku ba da gaskiya ni ne shi.

20 Lalle hakika, ina gaya muku, wanda ya yi na’am da duk wanda na aiko, ya yi na’am da ni ke nan. Wanda ya yi na’am da ni kuwa, to, ya yi na’am da wanda ya aiko ni.”

Yesu Ya Ce Za a Bāshe Shi

21 Bayan da Yesu ya faɗi haka, ya ji nauyi a ransa, ya yi shaida ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bāshe ni.”

22 Sai almajiran suka duddubi juna, suka rasa da wanda yake.

23 Wani daga cikin almajiransa kuwa, wanda Yesu yake ƙauna, yana kishingiɗe gab da Yesu.

24 Sai Bitrus ya alamta masa ya ce, “Gaya mana, da wa yake?”

25 Shi kuwa da yake kishingiɗe haka gab da Yesu ya karkata, ya ce masa, “Ya Ubangiji, wane ne?”

26 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan tsoma ‘yar lomar nan in ba shi.” Da ya tsoma ‘yar lomar kuwa, sai ya ba Yahuza, Ɗan Saminu Iskariyoti.

27 Da karɓar ‘yar loman nan Shaiɗan ya shige shi. Yesu ya ce masa, “Yi abin da za ka yi, maza.”

28 Amma cikin waɗanda suke cin abinci, ba wanda ya san dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka.

29 Har waɗansu ma sun yi zaton Yesu ya ce masa ya yi musu sayayyar idi ne, ko kuwa ya ba gajiyayyu wani abu, don Yahuza ne yake riƙe da jakar kuɗinsu.

30 Shi kuwa da karɓar ‘yar lomar, sai ya fita, da dare ne kuwa.

Sabon Umarni

31 Bayan ya fita kuma sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum, aka kuma ɗaukaka Allah ta wurinsa.

32 Allah kuma zai ɗaukaka shi zuwa ga zatinsa, nan da nan kuwa zai ɗaukaka shi.

33 Ya ku ‘ya’yana ƙanana, saura ɗan lokaci kaɗan ina tare da ku. Za ku neme ni, amma kamar yadda na faɗa wa Yahudawa cewa, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba,’ haka nake faɗa muku yanzu.

34 Sabon umarni nake ba ku, shi ne ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma, ku ƙaunaci juna.

35 Ta haka, kowa zai gane ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.”

Bitrus Zai Yi Musun Sanin Yesu

36 Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Inda za ni, ba za ka iya bina yanzu ba, amma daga baya za ka bi ni.”

37 Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, don me, ba zan iya binka a yanzu ba? Ai, zan ba da raina saboda kai.”

38 Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, za ka ba da ranka saboda ni? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara, za ka yi musun sanina sau uku.”