YAH 15

Yesu Ne Itacen Inabi na Hakika

1 “Ni ne itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomi.

2 Kowane reshe a cikina da ba ya ‘ya’ya, sai ya datse shi. Kowane reshe mai yin ‘ya’ya kuwa yakan tsarkake shi don ya ƙara haihuwa.

3 Koyanzu ma ku tsarkakku ne saboda maganar da na faɗa muku.

4 Ku zauna a cikina, ni kuma a cikinku. Kamar yadda reshen inabi, ba ya iya ‘ya’ya shi kaɗai, sai ko ya zauna itacen inabin, haka ku ma ba za ku iya ba, sai kun zauna a cikina.

5 Ni ne itacen inabin, ku kuwa rassan. Wanda ya zauna a cikina, ni kuma a cikinsa, shi ne mai yin ‘ya’ya da yawa. Domin in ba game da ni ba, ba za ku iya kome ba.

6 Duk wanda bai zauna a cikina ba, za a yar da shi can, kamar reshe, yă bushe, a kuma tattara irinsu a jefa wuta, a ƙone.

7 In kun zauna a cikina, maganata kuma ta zauna a cikinku, za ku roƙi duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku.

8 Yadda ake ɗaukaka Ubana ke nan, in kuna ‘ya’ya da yawa, ta haka kuma kuke tabbata almajiraina.

9 Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, ku zauna cikin ƙaunar da nake muku.

10 In kun bi umarnina, za ku zauna cikin ƙaunar da nake muku, kamar yadda ni na bi umarnin Ubana, na kuma zauna cikin ƙaunar da yake mini.

11 Na gaya muku haka domin farin cikina ya kasance a cikinku, farin cikinku kuma ya zama cikakke.

12 “Wannan fa shi ne umarnina, cewa ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.

13 Ba ƙaunar da ta fi haka ga mutane, wato mutum yă ba da ransa saboda aminansa.

14 Ku aminaina ne in kuna yin abin da na umarce ku.

15 Nan gaba ba sauran in ce da ku bayi, don bawa bai san abin da ubangijinsa yake yi ba. Sai dai in ce da ku aminai, domin na sanar da ku duk abin da na jiyo wurin Ubana.

16 Ba ku kuka zaɓe ni ba, ni ne na zaɓe ku, na sa ku ku je ku yi ‘ya’ya, ‘ya’yanku kuma su tabbata, domin kome kuka roƙi Uba da sunana yă ba ku.

17 Na umarce ku haka domin ku ƙaunaci juna.”

Ƙiyayyar Duniya

18 In duniya ta ƙi ku, ku sani sai da ta ƙi ni kafin ta ƙi ku.

19 Da ku na duniya ne da duniya ta so abinta, amma saboda ku ba na duniya ba ne, na kuma zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku.

20 Ku tuna da maganar da na yi muku cewa, ‘Bawa ba ya fin ubangijinsa.’ In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun kiyaye maganata, da sai su kiyaye taku ma.

21 Duk wannan za su yi muku saboda sunana, don ba su san wanda ya aiko ni ba.

22 Da ba domin na zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu kam, ba su da wani hanzari a kan zunubinsu.

23 Wanda ya ƙi ni ya ƙi Ubana ma.

24 Da ba domin na yi ayyuka a cikinsu da ba wanda ya taɓa yi sai ni ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun gani, sun kuma ƙi mu, ni da Ubana duka.

25 An yi wannan kuwa domin a cika maganar da yake a rubuce a cikin Shari’arsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’

26 Amma sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, wato Ruhu na gaskiya, mai fitowa daga wurin Uba, shi ne zai shaida ni.

27 Ku ma shaidu ne, domin tun farko kuke tare da ni.