YAH 16

1 “Na faɗa muku duk wannan ne domin in kawar muku da sanadin tuntuɓe.

2 Za su fisshe ku daga jama’a. Hakika, lokaci ma na zuwa da kowa ya kashe ku, zai zaci bautar Allah yake yi.

3 Za su yi haka ne kuwa domin ba su san Uba ko ni ba.

4 Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin in lokacinsu ya yi ku tuna na faɗa muku.”

Aikin Ruhu Mai Tsarki

“Ban faɗa muku abubuwan nan tun da farko ba, domin ina tare da ku.

5 Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’

6 Amma saboda na faɗa muku waɗannan abubuwa, ga shi baƙin ciki ya cika zuciyarku.

7 Duk da haka ina gaya muku gaskiya, zai fiye muku in tafi, domin in ban tafi ba, Mai Taimakon nan ba zai zo gare ku ba. In kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku.

8 Sa’ad da kuwa ya zo zai faɗakar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci.

9 Wato a kan zunubi, domin ba su gaskata da ni ba,

10 a kan adalci, don za ni wurin Uba, ba kuwa za ku ƙara ganina ba.

11 a kan hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulkin duniyar nan hukunci.

12 “Ina da sauran abubuwa da yawa da zan gaya muku tukuna, amma ba za ku iya ɗaukarsu a yanzu ba.

13 Sa’ad da kuwa Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku cikin dukan gaskiya, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai faɗa, zai kuma sanar da ku al’amuran da za su auku.

14 Zai ɗaukaka ni, domin zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku.

15 Duk abin da Uba yake da shi, nawa ne. Shi ya sa na ce zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku.”

Baƙin Ciki Zai Koma Farin Ciki

16 “Bayan ɗan lokaci kaɗan, ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma, za ku gan ni.”

17 Sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da ce mana, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’? da kuma cewa, ‘Domin za ni wurin Uba’?”

18 Suka ce, “Me yake nufi da, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ’ ɗin? Ai, ba mu san abin da yake faɗa ba.”

19 Yesu kuwa ya sani suna so su tambaye shi, sai ya ce musu, “Wato kuna tambayar juna ne abin da nake nufi da cewa, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’?

20 Lalle hakika, ina gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, amma duniya za ta yi farin ciki. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki.

21 Idan mace tana naƙuda takan sha wuya, don lokacin haihuwarta ya yi. Amma da zarar ta haifi jinjirin, ba ta ƙara tunawa da wahalar da ta sha, domin murnar an sami baƙon duniya.

22 Haka ku ma yanzu kuke tare da baƙin ciki, amma zan sāke ganinku, sa’an nan zuciyarku za ta yi fari, ba kuwa mai ɗauke muku farin cikinku.

23 A ran nan, ba za ku yi mini wata tambaya ba. Lalle hakika, ina gaya muku, kome kuka roƙi Uba zai ba ku saboda sunana.

24 Har yanzu dai ba ku roƙi kome da sunana ba. Ku roƙa, za ku samu, domin farin cikinku ya zama cikakke.”

Na Yi Nasara da Duniya

25 “Duk wannan na faɗa muku da misalai ne. Lokaci yana zuwa da ba zan ƙara faɗa muku kome da misalai ba, sai dai in ba ku labarin Uba a sarari.

26 A ran nan za ku yi roƙo da sunana. Ban kuwa ce muku zan roƙar muku Uba ba,

27 domin shi Uban kansa na ƙaunarku, domin kun ƙaunace ni, kun kuma gaskata daga wurin Uban na fito.

28 Daga wurin Uban ne na fito, na shigo duniya, har wa yau kuma zan bar duniya in koma wurin Uba.”

29 Sai almajiransa suka ce, “Yauwa! Yanzu ne fa kake magana a sarari, ba da misali ba!

30 Yanzu ne muka tabbata ka san kome, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito.”

31 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe, yanzu kun gaskata?

32 To, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansu, ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka kuwa ba ni kaɗai nake ba, domin Uba na tare da ni.

33 Na faɗa muku wannan ne domin a gare ni ku sami salama. A duniya kuna shan wuya, amma dai ku yi farin ciki, ai, na yi nasara da duniya.”