YAH 17

Addu’ar Yesu don Almajiransa

1 Da Yesu ya faɗi haka, sai ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka domin Ɗan ya ɗaukaka ka,

2 tun da ka ba shi iko a kan dukkan ‘yan adam, yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi.

3 Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko.

4 Na ɗaukaka ka a duniya da yake na cika aikin da ka ba ni in yi.

5 Yanzu kuma, ya Uba, ka ɗaukaka ni zuwa ga zatinka da ɗaukakan nan da nake da ita tare da kai tun kafin duniya ta kasance.

6 “Na bayyana sunanka ga mutanen da ka ba ni daga cikin duniya. Dā ma naka ne, ka kuwa ba ni su, sun kuma kiyaye maganarka.

7 Yanzu kuwa sun san duk iyakar abin da ka ba ni daga gare ka yake.

8 Domin kuwa maganar da ka faɗa mini na faɗa musu, sun kuwa karɓa, sun kuma san hakika na fito daga wurinka ne, sun kuma gaskata kai ne ka aiko ni.

9 Ni, roƙo nake yi dominsu. Ba duniya nake roƙa wa ba, sai dai su waɗanda ka ba ni, domin su naka ne.

10 Dukkan nawa naka ne, duk naka kuma nawa ne, an kuma ɗaukaka ni a zukatansu.

11 Yanzu kuma ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai tsarki, ka kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni, su zama ɗaya kamar yadda muke.

12 Duk sa’ad da nake tare da su, na kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni. Na kāre su, ba kuwa waninsu da ya halaka, sai dai halakakken nan, domin Nassi ya cika.

13 Amma yanzu ina zuwa wurinka. Ina faɗar wannan magana tun ina duniya, domin farin cikina ya zama cikakke a zukatansu.

14 Na faɗa musu maganarka, duniya kuwa ta ƙi su, domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne.

15 Ba na roƙonka ka ɗauke su daga duniya, sai dai ka kāre su daga Mugun nan.

16 Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne.

17 Ka tsarkake su cikin gaskiya. Maganarka ita ce gaskiya.

18 Kamar yadda ka aiko ni duniya, haka ni ma na aike su duniya.

19 Saboda su ne nake miƙa kaina, domin su ma a tsarkake su cikin gaskiya.

20 “Ba kuwa waɗannan kaɗai nake roƙa wa ba, har ma masu gaskatawa da ni ta maganarsu,

21 domin dukansu su zama ɗaya, kamar yadda kai, ya Uba, kake cikina, ni kuma nake cikinka, haka su ma su kasance cikinmu, domin duniya ta gaskata, cewa kai ne ka aiko ni.

22 Ɗaukakar da ka yi mini, ita na yi musu, domin su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya,

23 ni a cikinsu, kai kuma a cikina, domin su zama ɗaya sosai, duniya ta gane kai ne ka aiko ni, ta kuma gane ka ƙaunace su kamar yadda ka kaunace ni.

24 Ya Uba, ina so waɗanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, su dubi ɗaukakata da ka yi mini, domin ka ƙaunace ni tun ba a halicci duniya ba.

25 Ya Uba mai adalci, duniya kam, ba ta san ka ba, amma ni na san ka , waɗannan kuma sun sani kai ne ka aiko ni.

26 Na sanar da su sunanka, zan kuma sana, domin ƙaunar da ka yi mini tă kasance cikinsu, ni ma in kasance a cikinsu.”