YAH 18

An Ba Dda Yesu, An Kama Shi

1 Bayan Yesu ya yi maganan nan, ya fita, shi da almajiransa zuwa hayin Rafin Kidron, inda wani lambu yake, ya kuma shiga da almajiransa.

2 Yahuza ma wanda ya bāshe shi ya san wurin, domin Yesu ya saba haɗuwa da almajiransa a can.

3 Yahuza kuwa bayan ya ɗauko ƙungiyar soja, da waɗansu dogaran Haikali daga manyan firistoci da Farisiyawa, suka zo wurin, riƙe da fitilu, da jiniyoyi, da makamai,

4 Yesu kuwa da ya san duk abin da zai same shi, ya yiwo gaba, ya ce musu, “Wa kuke nema?”

5 Suka amsa masa suka ce, “Yesu Banazare.” Yesu ya ce musu, “Ni ne.” Yahuza kuwa da ya bāshe shi yana tsaye tare da su.

6 Da Yesu ya ce musu, “Ni ne,” suka ja da baya da baya, har suka fāɗi.

7 Sai ya sāke tambayarsu, “Wa kuke nema?” Suka ce, “Yesu Banazare.”

8 Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na gaya muku, ni ne. In kuwa ni kuke nema, ku bar waɗannan su tafi.”

9 Wannan kuwa domin a cika maganar da ya yi ne cewa, “A cikin waɗanda ka ba ni ban yar da ko ɗaya ba.”

10 Bitrus kuwa da yake yana da takobi, ya zaro ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama. Sunan bawan Malkus.

11 Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Mai da takobinka kube. Ba sai in sha ƙoƙon da Uba ya ba ni in sha ba?”

Yesu a Gaban Babban Firist

12 Sai ƙungiyar soja da shugabansu, da dogaran nan na Yahudawa suka kama Yesu, suka ɗaure shi,

13 suka tafi da shi wurin Hanana da fari, don shi surukin Kayafa ne, wanda yake shi ne babban firist a shekaran nan.

14 Kayafa kuwa shi ne ya yi wa Yahudawa shawara, cewa ya fiye musu mutum ɗaya ya mutu saboda jama’a.

Bitrus Ya Yi Musun Sanin Yesu

15 Sai Bitrus ya bi bayan Yesu, haka kuma wani almajiri. Almajirin nan kuwa sananne ne ga babban firist, sai ya shiga har gidan firist ɗin tare da Yesu,

16 Bitrus kuwa ya tsaya a bakin ƙofa daga waje. Sai ɗaya almajirin da yake sananne ga babban firist ya fita, ya yi magana da wadda take jiran ƙofa, sa’an nan ya shigo da Bitrus.

17 Baranyar da yake jiran ƙofar kuwa ta ce wa Bitrus, “Anya! Kai ma ba cikin almajiran mutumin nan kake ba?” Ya ce, “A’a, ba na ciki.”

18 To, barori da dogaran Haikali kuwa sun hura wutar gawayi, don ana sanyi, suna tsaitsaye, suna jin wutar. Bitrus ma yana tsaye tare da su yana jin wutar.

Babban Firist ya Tuhumi Yesu

19 Sai babban firist ya tuhumi Yesu a kan almajiransa da kuma koyarwa tasa.

20 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a bayyane, na kuma sha koyarwa a majami’u da Haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban faɗi kome a ɓoye ba.

21 Don me kake tuhumata? Tuhumi waɗanda suka saurare ni a kan abin da na faɗa musu, ai, sun san abin da na faɗa.”

22 Da ya faɗi haka, wani daga cikin dogaran da suke tsaye kusa, ya mari Yesu, ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?”

23 Yesu ya amsa masa ya ce, “In na faɗi mugun abu to, ka ba da shaida kan haka. In kuwa daidai na faɗa, to, don me za ka mare ni?”

24 Sai Hanana ya aika da shi a ɗaure wurin Kayafa, babban firist.

Bitrus Ya Sāke Musun Sanin Yesu

25 To, Bitrus kuwa yana tsaye yana jin wuta. Sai suka ce masa, “Anya! Kai ma ba cikin almajiransa kake ba?” Sai ya mūsu ya ce, “A’a, ba na ciki.”

26 Sai wani daga cikin bayin babban firist, wato dangin wanda Bitrus ya fille wa kunne, ya ce, “Ashe, ban gan ka tare da shi a lambun ba?”

27 Sai Bitrus ya sāke yin musu. Nan da nan kuwa zakara ya yi cara.

Yesu a Gaban Bilatus

28 Daga wurin Kayafa kuma suka kai Yesu fādar mai mulki. Da asuba ne kuwa. Su kansu ba su shiga fādar ba, wai don kada su ƙazantu su kāsa cin jibin Ƙetarewa.

29 Saboda haka, Bilatus ya fito wajensu, ya ce, “Wace ƙara kuka kawo ta mutumin nan?”

30 Sai suka amsa masa suka ce, “Da wannan ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu bāshe shi gare ka ba.”

31 Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga shari’arku!” Sai Yahudawa suka ce masa, “Ai, ba mu da ikon zartar da hukuncin kisa a kan kowa.”

32 Wannan kuwa don a cika maganar da Yesu ya yi ne, wadda ta kwatanta irin mutuwar da zai yi.

33 Sai Bilatus ya koma cikin fāda, ya kira Yesu ya ce masa, “Ashe, kai ɗin nan, kai ne Sarkin Yahudawa?”

34 Yesu ya amsa ya ce, “Wato wannan faɗarka ce, ko kuwa waɗansu ne suka ce da ni haka a wurinka?”

35 Bilatus ya amsa ya ce, “Ni Bayahude ne? Ai, jama’arku da manyan firistoci su ne suka bāshe ka gare ni. Me ka yi?”

36 Yesu ya amsa ya ce, “Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da mulkina na duniyan nan ne da barorina za su yi yaƙi kada a bāshe ni ga Yahudawa. Amma hakika, mulkina ba daga nan yake ba.”

37 Sai Bilatus ya ce masa, “Wato ashe, sarki ne kai?” Yesu ya amsa ya ce, “Yadda ka faɗa, ni sarki ne. Domin haka musamman aka haife ni, don haka kuma musamman na shigo duniya, domin in shaidi gaskiya. Kowane mai ƙaunar gaskiya kuwa yakan saurari muryata.”

38 Bilatus ya ce masa, “Wane abu ne, wai shi gaskiya?”

An Hukunta wa Yesu Mutuwa

Bayan da ya faɗi haka, ya sāke fitowa wurin Yahudawa, ya ce musu, “Ni kam, ban same shi da wani laifi ba.

39 Amma dai kuna da wata al’ada, in Idin Ƙetarewa ya yi, nakan sakar muku mutum ɗaya. To, kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?”

40 Sai suka sāke ɗaukar kururuwa suna cewa, “A’a, ba wannan ba, sai dai Barabbas!” Barabbas ɗin nan kuwa ɗan fashi ne.