YAH 19

1 Sa’an nan Bilatus ya sa a tafi da Yesu, a yi masa bulala.

2 Sai soja suka yi wani kambi na ƙaya suka sa masa a kā, suka yafa masa wata alkyabba mai ruwan jar garura.

3 Suka yi ta zuwa wurinsa, suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!” suna ta marinsa.

4 Sai Bilatus ya sāke fitowa, ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi, domin ku san ban same shi da wani laifi ba.”

5 Sa’an nan Yesu ya fito, sāye da kambin ƙayar, da alkyabba mai ruwan jar garura. Sai Bilatus ya ce musu, “To, ga mutumin!”

6 Da manyan firistoci da dogaran Haikali suka gan shi, suka ɗau kururuwa suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi ku da kanku, ku gicciye shi, ni kam, ban same shi da wani laifi ba.”

7 Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ai, muna da Shari’a, bisa ga Sharian nan kuwa ya wajaba a kashe shi, saboda ya mai da kansa Ɗan Allah.”

8 Da Bilatus ya ji maganan nan sai ya ƙara tsorata.

9 Ya sāke shiga fāda, ya ce wa Yesu, “Daga ina kake?” Amma Yesu bai amsa masa ba.

10 Saboda haka Bilatus ya ce masa, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka sani ba ni ne da ikon sakinka, ko gicciye ka?”

11 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina in ba an ba ka daga Sama ba, saboda haka wanda ya bāshe ni gare ka ya fi ka zunubi.”

12 A kan wannan Bilatus ya nemi ya sake shi, sai dai Yahudawa suka ɗau kururuwa suna cewa, “In dai ka saki wannan, kai ba masoyin Kaisar ba ne. Ai, kowa ya mai da kansa sarki, ya tayar wa Kaisar ke nan.”

13 Da Bilatus ya ji wannan magana, sai ya fito da Yesu, ya zauna a kan gadon shari’a, wurin da ake kira Daɓe, da Yahudanci kuwa, Gabbata.

14 Ran nan kuwa ranar shirin Idin Ƙetarewa ce, wajen tsakiyar rana. Sai ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku!”

15 Sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce musu, “A! In gicciye sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu ba mu da sarki sai Kaisar.”

16 Sa’an nan ya bāshe shi gare su su gicciye shi.

An Gicciye Yesu

17 Sai suka tafi da Yesu. Ya kuwa fita, shi kansa yake ɗauke da gicciyensa, har zuwa wurin da ake kira Wurin Ƙoƙon Kai, da Yahudanci kuwa, Golgota.

18 Nan suka gicciye shi, da kuma waɗansu mutum biyu tare da shi, ɗaya ta kowane gefe, Yesu kuwa a tsakiya.

19 Bilatus kuma ya rubuta wata sanarwa, ya kafa ta a kan gicciyen. Abin da aka rubuta ke nan, “Yesu Banazare Sarkin Yahudawa.”

20 Yahudawa da yawa kuwa sun karanta wannan sanarwa, domin wurin da aka gicciye Yesu kusa da birni ne. An kuwa rubuta ta da Yahudanci, da Romanci, da kuma Helenanci.

21 Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce wa Bilatus, “Kada ka rubuta ‘Sarkin Yahudawa’, sai dai ka rubuta, ‘A faɗarsa shi ne Sarkin Yahudawa.’ ”

22 Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta na rubuta ke nan.”

23 Bayan soja sun gicciye Yesu, suka ɗibi tufafinsa, suka kasa kashi huɗu, kowane soja ya ɗauki kashi guda. Suka kuma ɗauki taguwa tasa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta.

24 Sai suka ce wa juna, “Kada mu tsaga ta, sai dai mu yi kuri’a a kanta, mu ga wanda zai ci.” Wannan kuwa domin a cika Nassi ne cewa,

“Sun raba tufafina a junansu.

Taguwata kuwa suka jefa kuria akanta”

25 Haka fa sojan suka yi. To, kusa da gicciyen Yesu kuwa da uwa tasa, da ‘yar’uwa tata, da Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magadaliya, suna tsaye.

26 Da Yesu ya ga uwa tasa, da almajirin nan da yake ƙauna suna tsaye kusa, ya ce wa uwa tasa, “Iya, ga ɗanki nan!”

27 Sa’an nan ya ce wa almajirin, “Ga tsohuwarka nan!” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.

Mutuwar Yesu

28 Bayan haka, Yesu da ya san duk an gama kome, domin a cika Nassi sai ya ce, “Ina jin ƙishirwa.”

29 To, akwai wani gora cike da ruwan tsami a ajiye a nan. Sai suka jiƙa soso da ruwan tsamin, suka soka a sandan izob suka kai bakinsa.

30 Da Yesu ya tsotsi ruwan tsamin nan ya ce, “An gama!” Sa’an nan ya sunkuyar da kansa ya ba da ransa.

An Soki Kwiɓin Yesu

31 Da yake ran nan ranar shiri ce, don kada a bar jikuna a gicciye ran Asabar (domin wannan Asabar ɗin babbar rana ce), sai Yahudawa suka roƙi Bilatus a karya ƙafafunsu, a kuma ɗauke jikunan.

32 Sai soja suka zo suka karya ƙafafun na farkon nan, da kuma na ɗayan da aka gicciye tare da shi.

33 Amma da suka zo wurin Yesu, suka kuma ga ya riga ya mutu, ba su karya ƙafafunsa ba.

34 Sai dai ɗaya daga cikin sojan nan ya soke shi da mashi a kwiɓi, nan da nan sai ga jini da ruwa suka gudano.

35 Wanda ya gani ɗin kuwa shi ya ba da shaida kan haka, shaida tasa kuwa gaskiya ce, ya kuma san gaskiya yake faɗa, domin ku ma ku ba da gaskiya.

36 Wannan kuwa don a cika Nassi ne cewa, “Ƙashinsa ɗaya ba za a karya ba.”

37 Wani Nassi kuma ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.”

Jana’izar Yesu

38 Bayan haka Yusufu, mutumin Arimatiya, wanda yake almajirin Yesu ne amma a ɓoye domin tsoron Yahudawa, ya roƙi Bilatus izinin ɗauke jikin Yesu. Bilatus kuwa ya ba shi izini, ya kuwa zo ya ɗauke jikin Yesu.

39 Nikodimu kuma, wanda farkon zuwansa wurin Yesu da dad dare ne, ya zo da mur da al’ul a gauraye, wajen awo ɗari.

40 Sai suka ɗauki jikin Yesu suka sa shi a likkafanin lilin game da kayan ƙanshin nan, bisa ga al’adar Yahudawa ta jana’iza.

41 A wurin da aka gicciye shi kuwa akwai wani lambu, a cikin lambun kuma da wani sabon kabari wanda ba a taɓa sa kowa ba.

42 Da yake ranar shiri ce ta Yahudawa, kabarin kuma na kusa, sai suka sa Yesu a nan.