YAH 5

Warkarwa a Tafkin Betasda

1 Bayan haka aka yi wani idi na Yahudawa, Yesu kuwa ya tafi Urushalima.

2 A Urushalima, kusa da Ƙofar Tumaki, akwai wani ruwa da ake ce da shi Betasda da Yahudanci, an kuwa kewaye shi da shirayi biyar.

3 A shirayin nan kuwa marasa lafiya da yawa sun saba kwanciya, makafi, da guragu, da shanyayyu. [Suna jira a motsa ruwan.

4 Don lokaci lokaci wani mala’ika yakan sauko cikin ruwan ya motsa shi. Duk kuwa wanda ya fara shiga bayan an motsa ruwan, sai ya warke daga duk irin cutar da yake da ita.]

5 A nan kuwa akwai wani mutum da ya shekara talatin da takwas da rashin lafiya.

6 Da Yesu ya gan shi kwance, ya kuma sani ya daɗe da wannan hali, sai ya ce masa, “Kana so a warkar da kai?”

7 Marar lafiyar ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, ai, ba ni da wanda zai angaza ni cikin ruwan lokacin da aka motsa shi. Lokacin da na doshi ruwan kuma sai wani ya riga ni shiga.”

8 Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka yi tafiya!”

9 Nan take mutumin ya warke, ya ɗauki shimfiɗarsa ya yi tafiya tasa.

Ran nan kuwa Asabar ce.

10 Saboda haka Yahudawa suka ce da wanda aka warkar ɗin, “Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka ɗauki shimfiɗarka ba.”

11 Sai ya amsa musu ya ce, “Ai, wanda ya warkar da ni, shi ne ya ce in ɗauki shimfiɗata, in tafi.”

12 Suka tambaye shi, “Wane mutum ne ya ce maka ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi?”

13 Wanda aka warkar ɗin kuwa bai san ko wane ne ba, domin Yesu ya riga ya tashi saboda taron da yake wurin.

14 Bayan haka Yesu ya same shi a Haikali, ya ce masa, “Ka ga fa, ka warke! To, ka daina yin zunubi, don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka.”

15 Sai mutumin ya tafi ya gaya wa Yahudawa, Yesu ne ya warkar da shi.

16 Saboda haka, Yahudawa suka fara tsananta wa Yesu, don yana yin irin waɗannan abubuwa ran Asabar.

17 Yesu kuwa ya amsa musu ya ce, “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina yi.”

18 Don haka, Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi, ba don ya keta Asabar kaɗai ba, har ma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato, yana daidaita kansa da Allah.

Ikon Ɗan

19 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, Ɗan ba ya yin kome shi kaɗai, sai abin da ya ga Uba yana yi. Domin duk abin da Uban yake yi, haka shi Ɗan ma yake yi.

20 Domin Uban na ƙaunar Ɗan, yana kuma nuna masa duk abin da shi kansa yake yi, har ma zai nuna masa ayyukan da suka fi waɗannan, domin ku yi al’ajabi.

21 Yadda Uba yake ta da matattu ya kuma raya su, haka Ɗan ma yake rayar da wanda ya nufa.

22 Uba ba ya hukunta kowa, sai dai yā danƙa dukkan hukunci ga Ɗan,

23 domin kowa yă girmama Ɗan, kamar yadda ake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan.

24 Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai jin maganata, yake kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami. Ba za a yi masa hukunci ba, domin ya riga ya tsere wa mutuwa, ya kai ga rai.

25 “Lalle hakika, ina gaya muku, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da matattu za su ji muryar Ɗan Allah, masu ji kuwa su rayu.

26 Yadda Uba kansa yake tushen rai, haka ya sa Ɗan ya zama tushen rai.

27 Ya kuma ba shi ikon zartar da hukunci, saboda shi Ɗan Mutum ne.

28 Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci na zuwa da duk waɗanda suke kaburbura za su ji murya tasa,

29 su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta su tashi, tashin rai, waɗanda suka yi rashin gaskiya kuwa su tashi, tashin hukunci.

Shaidun Yesu

30 “Ba na iya yin kome ni kaɗai. Yadda nake ji, haka nake yin hukunci. Hukuncina kuwa na adalci ne, domin ba nufin kaina nake bi ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.

31 In na shaida kaina, shaidata ba tabbatacciya ba ce.

32 Akwai wani mashaidina dabam, na kuwa san shaidar da yake yi mini tabbatacciya ce.

33 Kun aika wajen Yahaya, shi kuma ya shaidi gaskiya.

34 Duk da haka shaidar da na dogara da ita ba ta mutum ba ce. Na dai faɗi haka ne domin ku sami ceto.

35 Yahaya fitila ne mai ci, mai haske kuma, kun kuwa yarda ku yi farin ciki matuƙa da haskensa ɗan lokaci kaɗan.

36 Amma shaidar da ni nake da ita ta fi ta Yahaya ƙarfi. Domin ayyukan da Uba ya ba ni in gama, su ainihin ayyukan nan da nake yi, ai, su ne shaidata a kan cewa, Uba ne ya aiko ni.

37 Uban kuma da ya aiko ni, shi kansa ya shaide ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ba, ko ganin kama tasa.

38 Maganarsa kuwa ba ta zauna a zuciyarku ba, domin ba ku gaskata wanda ya aiko ni ba.

39 Kuna ta nazarin Littattafai, don a tsammaninku a cikinsu za ku sami rai madawwami, alhali kuwa su ne suke shaidata.

40 Duk da haka, kun ƙi zuwa wurina ku sami rai.

41 Ba na karɓar girma wurin mutane.

42 Amma fa na san ku, ba ku da ƙaunar Allah a zuci.

43 Ni na zo ne da sunan Ubana, ga shi, ba ku karɓe ni ba. In da wani zai zo da sunan kansa, shi za ku karɓa.

44 Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karɓar girma a junanku, girman da yake daga Allah Makaɗaici kuwa, ba kwa nemansa?

45 Kada ku zaci zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi.

46 Da dai kun gaskata Musa, da kun gaskata ni, domin labarina ya rubuta.

47 In kuwa ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, ta yaya za ku gaskata maganata?”