YAH 6

Ciyar da Mutum Dubu Biyar

1 Bayan haka Yesu ya haye Tekun Galili, wato Tekun Tibariya.

2 Sai taro mai yawa suka bi shi, don sun ga mu’ujizan da yake yi ga marasa lafiya.

3 Sai Yesu ya hau dutse ya zauna a can tare da almajiransa.

4 To, Idin Ƙetarewa, wato idin Yahudawa, ya gabato.

5 Da Yesu ya ɗaga kai ya hango babban taro yana doso shi, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayo gurasar da mutanen nan za su ci?”

6 Ya faɗi haka ne fa domin ya gwada shi, saboda shi kansa ya san abin da zai yi.

7 Filibus ya amsa ya ce, “Ai, ko gurasar dinari metan ma ba ta isa ko wannensu ya sami kaɗan ba.”

8 Sai Andarawas ɗan’uwan Bitrus ɗaya daga cikin almajiransa, ya ce masa,

9 “Ga wani ɗan yaro nan da gurasa biyar na sha’ir, da kuma kifi biyu. Amma me waɗannan za su yi wa mutane masu yawa haka?”

10 Yesu ya ce, “Ku ce wa mutane su zauna.” Wuri ne kuwa mai ciyawa. Sai mazaje suka zazzaune, su wajen dubu biyar.

11 Yesu ya ɗauki gurasar, bayan ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya rarraba wa waɗanda suke zazzaune. Haka kuma ya yi da kifin, gwargwadon abin da ya ishe su.

12 Da suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka saura, kada kome ya ɓata.”

13 Sai suka tattara gutsattsarin gurasar nan biyar na sha’ir da suka saura bayan kowa ya ci, suka cika kwando goma sha biyu.

14 Da jama’a suka ga mu’ujizar da ya yi, suka ce, “Lalle, wannan shi ne annabin nan mai zuwa duniya.!”

15 Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai.

Yesu na Tafiya a kan Ruwan Teku

16 Da magariba ta yi, sai almajiransa suka gangara teku.

17 Suka shiga jirgi suka tasar wa haye tekun zuwa Kafarnahun. A sa’an nan duhu ya yi, Yesu kuwa bai zo wurinsu ba tukuna.

18 Sai tekun ta fara hauka saboda wata riƙaƙƙiyar iska da take busowa.

19 Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko huɗu, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan ruwan, ya kusato jirgin. Sai suka firgita.

20 Amma ya ce musu, “Ni ne, kada ku ji tsoro.”

21 Sa’an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin. Nan da nan sai ga jirgin a gāɓar da za su.

Taro sun Nemi Yesu

22 Kashegari sauran taron da suka tsaya a hayin tekun suka lura ba wani jirgi a wurin, sai wani ɗan ƙarami, suka kuma lura Yesu bai shiga cikinsa tare da almajiransa ba, sai almajiran ne kaɗai suka tafi.

23 Akwai kuwa waɗansu ƙananan jirage daga Tibariya da suka iso kusa da wurin nan da taron suka ci gurasa bayan Ubangiji ya yi godiya.

24 Sa’ad da kuwa taron suka ga ba Yesu, ba almajiransa a nan, su ma suka shiga ƙananan jiragen, suka tafi Kafarnahum neman Yesu.

Yesu Gurasar Rai

25 Da suka same shi a hayin tekun, suka ce masa, “Ya Shugaba, yaushe ka zo nan?”

26 Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga mu’ujizai ba, sai don kun ci gurasar nan kun ƙoshi.

27 Kada ku yi wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama har ya zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. Domin shi ne wanda Uba, wato Allah, ya tabbatar wa da ikon yin haka.”

28 Sai suka ce masa, “Me za mu yi mu aikata ayyukan da Allah yake so?”

29 Yesu ya amsa musu ya ce, “Wannan shi ne aikin da Allah yake so, wato ku gaskata da wanda ya aiko.”

30 Sai suka ce masa, “To, wace mu’ujiza za ka yi mu gani mu gaskata ka? Me za ka yi?

31 Kakannin kakanninmu sun ci manna a jeji, yadda yake a rubuce cewa, ‘Ya ba su gurasa daga Sama su ci.’ ”

32 Sa’an nan Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ba Musa ne ya ba ku gurasar nan daga Sama ba, Ubana ne yake ba ku hakikanin Gurasa daga Sama.

33 Ai, Gurasan Allah shi ne mai saukowa daga Sama, mai ba duniya rai.”

34 Sai suka ce masa, “Ya Ubangiji, ka riƙa ba mu irin wannan gurasa kullum!”

35 Yesu ya ce musu, “Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo gare ni ba zai ji yunwa ba har abada, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada.

36 Na dai gaya muku, kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba.

37 Duk wanda Uba ya ba ni zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kaɗan.

38 Domin na sauko daga Sama, ba domin in bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.

39 Nufin wanda ya aiko ni kuwa, shi ne kada in yar da kowa daga cikin dukkan waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a ranar ƙarshe.

40 Gama nufin Ubana, shi ne duk wanda yake duban Ɗan, yake kuma gaskatawa da shi, yă sami rai madawwani, ni kuma zan tashe shi a ranar ƙarshe.”

41 Sai fa Yahudawa suka yi masa gunaguni, domin ya ce, “Ni ne Gurasan da ya sauko daga Sama.”

42 Suka ce, “Ashe, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusufu, wanda uwa tasa da ubansa duk mun san su? To, yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko ne daga sama’?”

43 Yesu ya amsa musu ya ce, “Kada ku yi gunaguni a junanku.

44 Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uba wanda ya aiko ni ne ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe.

45 A rubuce yake cikin littattafan annabawa cewa, ‘Dukkansu Allah ne zai koya musu.’ To, duk wanda ya ji, ya kuma koya wurin Uba, zai zo gare ni.

46 Ba wai don wani ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda yake daga wurin Allah, shi ne ya ga Uban.

47 Lalle hakika ina gaya muku, wanda ya ba da gaskiya, yana da rai madawwami.

48 Ni ne Gurasa mai ba da rai.

49 Kakannin kakanninku sun ci manna a jeji, amma kuwa sun mutu.

50 Ga Gurasa mai saukowa daga Sama, domin kowa yă ci, kada ya mutu.

51 Ni ne Gurasan rai da ya sauko daga Sama. Kowa ya ci Gurasan nan, zai rayu har abada. Har ma gurasar da zan bayar naman jikina ne, domin duniya ta rayu.”

52 Sai Yahudawa suka ta da husuma a junansu, suna cewa, “Yaya mutumin nan zai iya ba mu naman jikinsa mu ci?”

53 Sai Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, in ba ku ci naman jikin Ɗan Mutum ba, kuka kuma sha jininsa, ba rai a gare ku.

54 Duk wanda suke cin naman jikina, yake kuma shan jinina, yana da rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe.

55 Domin naman jikina abinci ne na hakika, jinina kuma abin sha ne na hakika.

56 Duk wanda suke cin naman jikina, yake shan jinina, a cikina yake zaune, ni kuma a cikinsa.

57 Kamar yadda rayayyen Uba ya aiko ni, nake kuma rayuwa saboda Uban, haka ma wanda yake ni ne abincinsa zai rayu saboda ni.

58 Wannan shi ne Gurasan da ya sauko daga Sama, ba irin wadda kakannin kakanninku suka ci ba, duk da haka suka mutu. Duk mai cin Gurasan nan zai rayu har abada.”

59 Wannan kuwa a majami’a ya faɗa, sa’ad da yake koyarwa a Kafarnahum.

Kalmomin Rai

60 Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan magana mai wuya ce, wa zai iya jinta?”

61 Yesu kuwa, da yake ya sani a ransa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce musu, “Wato, wannan ne ya zamar muku abin tuntuɓe?

62 Yaya ke nan in kuka ga Ɗan Mutum yana hawa inda yake dā?

63 Ai, Ruhu shi ne mai rayarwa, jiki kam ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku ruhu ne, da kuma rai.

64 Amma fa akwai waɗansunku da ba su ba da gaskiya ba.” Domin tun farko Yesu ya san waɗanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bāshe shi.

65 Sai ya ƙara da cewa, “Shi ya sa na gaya muku, ba mai iya zuwa gare ni, sai ko Uba ya yardar masa.”

66 Kan wannan da yawa daga cikin almajiransa suka koma da baya, ba su ƙara tafiya tare da shi ba.

67 Sai Yesu ya ce wa goma sha biyun, “Ku ma kuna so ku tafi ne?”

68 Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangiji, gun wa za mu je? Kai kake da maganar rai madawwami.

69 Mu kuwa mun gaskata, mun kuma tabbata kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.”

70 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba ni na zaɓe ku, ku goma sha biyu ba? To, ɗayanku Iblis ne.”

71 Wato, yana nufin Yahuza, ɗan Saminu Iskariyoti, don shi ne zai bāshe shi, ko da yake ɗaya daga cikin goma sha biyun nan ne.