1 Yesu kuwa ya hau Dutsen Zaitun.
2 Da sassafe kuma ya sāke shiga Haikali. Duk mutane suka zo wurinsa, ya kuwa zauna yana koya musu.
3 Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka kawo wata mace da aka kama da zina. Da suka tsai da ita a tsaka,
4 suka ce masa, “Malam, matan nan an kama ta ne, suna cikin yin zina.
5 To, a Attaura Musa ya umarce mu mu kashe irin waɗannan da jifa, kai kuwa me ka ce?”
6 Sun faɗi haka ne don su gwada shi, ko sa sami hanyar kai ƙararsa. Amma Yesu ya sunkuya, ya yi ta rubutu a ƙasa da yatsa.
7 Da suka dinga tambayarsa sai ya ɗaga, ya ce musu, “To, marar zunubi a cikinku ya fara jifanta da dutse.”
8 Sai ya sāke sunkuyawa, ya yi ta rubutu a ƙasa.
9 Su kuwa da suka ji haka suka fita da ɗaya ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, aka bar Yesu shi kaɗai, da matar tsaye a tsakiya.
10 Sai Yesu ya ɗaga, ya ce mata, “Uwargida, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?”
11 Ta ce, “Babu, ya Ubangiji.” Sai Yesu ya ce, “Ni ma ban hukunta ki ba. Yi tafiyarki. Daga yau kada ki ƙara yin zunubi.”]
Yesu Hasken Duniya
12 Sai Yesu ya ƙara musu da cewa, “Ni ne Hasken duniya. Wanda yake bi na ba zai yi tafiya a duhu ba, amma zai sami hasken rai,”
13 Saboda haka Farisiyawa suka ce masa, “Kanka kake wa shaida, shaidarka kuwa ba tabbatacciya ba ce.”
14 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ko na shaidi kaina, ai, shaidata tabbatacciya ce, domin na san inda na fito, da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ba, ko kuma inda za ni.
15 Ku kuna hukunci irin na duniya ne, ni kuwa ba na hukunta kowa.
16 Amma ko da zan yi hukunci, hukuncina na gaskiya ne, domin ba ni kaɗai nake ba, ni da Uba wanda ya aiko ni ne.
17 A Attaurarku ma a rubuce yake, cewa shaidar mutum biyu tabbatacciya ce.
18 Ni ne nake shaidar kaina, Uba da ya aiko ni kuma yana shaidata.”
19 Saboda haka suka ce masa, “Ina Uban naka yake?” Yesu ya amsa ya ce, “Ko ni ko Ubana, ba wanda kuka sani. Da kun san ni, da kun san Ubana ma.”
20 Ya faɗi wannan magana ne a baitulmalin Haikali, lokacin da yake koyarwa a wurin. Duk da haka ba wanda ya kama shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna.
Inda Za Ni Ba Ku Iya Zuwa Ba
21 Sai ya ƙara ce musu, “Zan yi tafiya, za ku kuwa neme ni, amma za ku mutu da zunubinku. Inda za ni kuwa ba za ku iya zuwa ba.”
22 Saboda haka sai Yahudawa suka ce, “Wato zai kashe kansa ke nan da ya ce, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba’?”
23 Sai ya ce musu, “Ku daga ƙasa kuke, ni kuwa daga sama nake. Ku na duniyan nan ne, ni kuwa ba na duniyar nan ba ne.”
24 Shi ya sa na ce muku za ku mutu da zunubanku. Domin in ba ku gaskata ni ne shi ba, za ku mutu da zunubanku.”
25 Sai suka ce masa, “Kai wane ne?” Yesu ya ce musu, “Daidai yadda na gaya muku.
26 Akwai abubuwa da yawa da zan faɗa game da ku, in kuma hukunta. Amma shi wannan da ya aiko ni mai gaskiya ne. Abin da na jiyo daga gare shi kuwa, shi nake shaida wa duniya.”
27 Ba su gane maganar Uba yake yi musu ba.
28 Sai Yesu ya ce, “Sa’ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa’an nan ne za ku gane ni ne shi, ba na yin kome kuma ni kaɗai, sai dai Uba ya koya mini, haka nake faɗa.
29 Wanda kuwa ya aiko ni yana tare da ni, bai bar ni ni kaɗai ba, domin koyaushe ina aikata abin da yake so.”
30 Sa’ad da Yesu yake faɗar haka, mutane da yawa suka gaskata da shi.
Gaskiya Za ta ‘Yanta Ku
31 Sai Yesu ya ce wa Yahudawan nan da suka gaskata shi, “In dai kun zauna kan maganata, hakika ku almajiraina ne.
32 Za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ‘yanta ku.”
33 Suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne, ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya kuma za ka ce za a ‘yanta mu?”
34 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai aikata zunubi bawan zunubi ne.
35 Ai, bawa ba ya ɗorewa a gida har abada, ɗa kuwa yana ɗorewa.
36 In kuwa Ɗan ya ‘yanta ku, za ku ‘yantu, ‘yantuwar gaske.
37 Na san dai ku zuriyar Ibrahim ne, amma kuwa kuna neman kashe ni, don maganata ba ta shigarku.
38 Ina faɗar abin da na gani a wurin Ubana, ku kuma kuna yin abin da kuka ji daga wurin naku uba.”
Ubanku Iblis Ne
39 Suka amsa masa suka ce, “Ai, Ibrahim ne ubanmu.” Yesu ya ce musu, “Da ku ‘ya’yan Ibrahim ne, da sai ku yi aikin da Ibrahim ya yi.
40 Ga shi yanzu, kuna neman kashe ni, ni mutumin da na gaya muku gaskiyar da na ji wurin Allah. Ba haka Ibrahim ya yi ba.
41 Ku kuna aikin da ubanku yake yi ne.” Suka ce masa, “Ba a haife mu daga fasikanci ba, ubanmu ɗaya ne, wato Allah.”
42 Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku da kun ƙaunace ni, domin daga wurin Allah na fito, ga ni nan kuwa. Ban zo domin kaina ba, shi ne ya aiko ni.
43 Don me ba kwa gane maganata? Don ba kwa iya jimirin jin maganata ne.
44 Ku na ubanku Iblis ne, niyyarku kuwa ku aikata burin ubanku. Shi dā ma tun farko mai kisankai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa’ad da yake ƙarya, cinikinsa yake yi, don shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.
45 Amma domin ina faɗar gaskiya, ba kwa gaskata ni.
46 A cikinku wa zai iya haƙƙaƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya nake faɗa, to, don me ba kwa gaskata ni?
47 Na Allah yakan saurari Maganar Allah. Abin da ya sa ba kwa sauraronta ke nan, don ku ba na Allah ba ne.”
Kafin Ibrahim, Nake
48 Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ashe, gaskiyarmu da muka ce kai Basamariye ne, kana kuma da iska.”
49 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ba mai iska ba ne. Ubana nake girmamawa, ku kuwa wulakanta ni kuke yi.
50 Ba ni nake nemar wa kaina girma ba, akwai mai nemar mini, shi ne kuma mai yin shari’a.
51 Lalle hakika, ina gaya muku, kowa ya kiyaye maganata ba zai mutu ba har abada.”
52 Sai Yahudawa suka ce masa, “To, yanzu kam, mun tabbata kana da iska. Ai, Ibrahim ya mutu, haka ma annabawa, kana kuwa cewa kowa ya kiyaye maganarka ba zai mutu ba har abada.
53 Wato ka fi ubanmu Ibrahim ne, ya kuwa mutu? Annabawa ma sun mutu! Wa ka mai da kanka ne?”
54 Yesu ya amsa ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba a bakin kome take ba. Ubana shi ne mai ɗaukaka ni, wanda kuke cewa, shi ne Allahnku.
55 Ku ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Da na ce ban san shi ba, da na zama maƙaryaci kamarku. Amma na san shi, ina kuma kiyaye magana tasa.
56 Ubanku Ibrahim ya yi farin ciki matuƙa ya sami ganin zamanina, ya kuwa gan shi, ya yi murna.”
57 Sai Yahudawa suka ce masa, “Har yanzu ma ba ka kai shekara hamsin ba, wai kuwa har ka ga Ibrahim!”
58 Sai Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne.”
59 Don haka suka ɗebo duwatsu su jajjefe shi. Yesu kuwa ya ɓuya, ya fita daga Haikalin.