YAK 1

Gaisuwa

1 Daga Yakubu, bawan Allah, da kuma na Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga kabilan nan goma sha biyu da suke a warwatse a duniya. Gaisuwa mai yawa.

Bangaskiya da Tawali’u

2 Ya ku ‘yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje iri iri suka same ku, ku mai da su abin farin ciki ƙwarai.

3 Domin kun san jarrabawar bangaskiyarku takan haifi jimiri.

4 Sai kuma jimiri ya yi cikakken aikinsa, domin ku zama kamilai cikakku kuma, ba ku gaza da kome ba.

5 In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi.

6 Amma fa sai ya roƙa da bangaskiya, ba tare da shakka ba. Don mai shakka kamar raƙuman ruwan teku yake, waɗanda iska take korawa tana tuttunkuɗawa.

7-8 Kada irin mutumin nan mai zuciya biyu, wanda bai tsai da zuciyarsa a gu ɗaya a dukan al’amuransa ba, ya sa rai da wani abu a gun Ubangiji.

9 Ƙasƙantaccen ɗan’uwa yă yi taƙama da ɗaukakarsa.

10 Mai arziki kuma yă yi alfarma da ƙasƙancinsa, gama zai shuɗe kamar hudar ciyawa.

11 In rana ta tāke da ƙunarta, sai ciyawa ta bushe, hudarta ta kaɗe, kyanta kuma ya gushe. Haka ma mai arziki zai gushe yana a cikin tsakiyar harkarsa.

Gwaji da Jarrabawa

12 Albarka tā tabbata ga mai jimirin gwaji, domin in ya jure gwajin, sai ya sami kambin rai, wanda Ubangiji ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari.

13 Duk wanda ake jarabta, kada ya ce Allah ne yake jarabtarsa, gama ba shi yiwuwa a jarabci Allah da mugunta, shi kansa kuwa ba ya jarabtar kowa.

14 Amma kowane mutum yakan jarabtu in mugun burinsa ya ruɗe shi, ya kuma yaudare shi.

15 Mugun buri kuma in ya yi ciki, yakan haifi zunubi. Zunubi kuma in ya balaga, yakan jawo mutuwa.

16 Kada fa a yaudare ku, ya ‘yan’uwana ƙaunatattu.

17 Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.

18 Bisa ga nufinsa ya kawo mu ta maganar gaskiya, domin mu zama kamar nunan fari na halittarsa.

Jin Magana da Aikatawa

19 Ya ‘yan’uwana ƙaunatattu, ku san wannan, wato, kowa yă yi hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi,

20 don fushin mutum ba ya aikata adalci.

21 Saboda haka, sai ku yar da kowane irin aikin ƙazanta da ƙeta iri iri, maganar nan da aka dasa a zuciyarku, ku yi na’am da ita a cikin halin tawali’u, domin ita ce mai ikon ceton rayukanku.

22 Amma ku zama masu aikata maganar, ba masu ji kawai, kuna yaudarar kanku ba.

23 Don duk wanda yake mai jin maganar ne kawai, ba mai aikatawa ba, kamar mutum yake mai duba fuskarsa a madubi,

24 don yakan dubi fuskarsa ne kawai ya tafi, nan da nan kuwa sai ya mance kamanninsa.

25 Amma duk mai duba cikakkiyar ka’idar nan ta ‘yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai ya mance ba, sai dai mai aikatawa ne ya zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake aikatawa.

26 In wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, sai dai ya yaudari kansa, to, addinin mutumin nan na banza ne.

27 Addini sahihi kuma marar aibu a gaban Allah Ubanmu, shi ne a kula da gwauraye mata, da marayu a cikin ƙuntatarsu, a kuma a keɓe kai marar aibi daga duniya.