YAK 2

Faɗaka a kan Tara

1 Ya ku ‘yan’uwana, kada ku nuna bambanci muddin kuna riƙe da bangaskiyarku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangiji Maɗaukaki.

2 Misali, in mutum mai zobban zinariya da tufafi masu ƙawa ya halarci taronku, wani matalauci kuma ya shigo a saye da tsummoki,

3 sa’an nan kuka kula da mai tufafi masu ƙawar nan, har kuka ce masa, “Ga mazauni mai kyau a nan,” matalaucin nan kuwa kuka ce masa, “Tsaya daga can,” ko kuwa, “Zauna a nan ƙasa a gabana,”

4 ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ba ke nan, kuna zartar da hukunci da mugayen tunani?

5 Ku saurara, ya ‘yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi matalautan duniyar nan su wadata da bangaskiya, har su sami gado a cikin mulkin nan da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?

6 Amma, kun wulakanta matalauta! Ashe, ba masu arzikin ne suke matsa muku ba? Ba su ne kuwa suke janku zuwa gaban shari’a ba?

7 Ba kuma su ne kuke saɓon sunan nan mai girma da ake kiranku da shi ba?

8 Idan lalle kun cika muhimmin umarni yadda Nassi ya ce, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” to, madalla.

9 Amma in kun nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan, Shari’a kuma ta same ku da laifin keta umarni.

10 Duk wanda yake kiyaye dukkan Shari’a, amma ya saɓa a kan abu guda, ya saɓi Shari’a gaba ɗaya ke nan.

11 Domin shi wannan da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” To, in ba ka yi zina ba amma ka yi kisankai, ai, ka zama mai keta Shari’a ke nan.

12 Saboda haka, maganarku da aikinku su kasance irin na mutanen da za a yi wa shari’a bisa ga ka’idar ‘yanci.

13 Gama Shari’a marar jinƙai ce ga wanda ba ya nuna jinƙai. Amma jinƙai yana rinjayar hukunci.

Bangaskiya Ba Tare da Ayyuka Ba Banza Ce

14 Ya ku ‘yan’uwana, ina amfani mutum ya ce yana da bangaskiya, alhali kuwa ba ya aikin da zai nuna ta? Anya, bangaskiyar nan tāsa ta iya cetonsa?

15 Misali, in wani ɗan’uwa ko ‘yar’uwa suna zaman huntanci, kullum kuma abinci bai wadace su ba,

16 waninku kuma ya ce musu, “To, ku sauka lafiya, Allah ya ba ci, da sha, da tufatarwa” ba tare da kun biya musu bukata ba, ina amfanin haka?

17 Haka ma, bangaskiya ita kaɗai, ba tare da aikin da ya nuna ta ba, banza ce.

18 To, amma wani zai ce, “Ai, kai kana da bangaskiya, ni kuwa sai aikatawa.” To, nuna mini bangaskiya, taka ba tare da aikatawa ba, ni kuma in nuna maka aikatawata, tabbatar bangaskiyata.

19 Ka gaskata Allah ɗaya ne? To, madalla. Ai, ko aljannu ma sun gaskata, amma suna rawar jiki don tsoro.

20 Kai marar azanci! Wato sai an nuna maka, bangaskiya ba tare da aikatawa ba, wofiya ce?

21 Sa’ad da kakanmu Ibrahim ya miƙa ɗansa Ishaku a bagadin hadaya, ashe, ba ta wurin aikatawa ne ya barata ba?

22 Ka gani, ashe, bangaskiyarsa da aikatawarsa duka yi aiki tare, har ta wurin aikatawar nan bangaskiyarsa ta kammala.

23 Aka kuma cika Nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, bangaskiyar nan tasa kuma aka lasafta ta adalci ce a gare shi,” aka kuma kira shi aminin Allah.

24 Kun ga, ashe, Allah yana kuɓutar da mutum saboda aikatawarsa ne, ba saboda bangaskiya ita kaɗai ba.

25 Ashe, ba haka kuma Rahab karuwar nan ta sami kuɓuta saboda aikatawarta ba? Wato, sa’ad da ta sauki jakadun nan, ta fitar da su ta wata hanya dabam?

26 To, kamar yadda jiki ba numfashi matacce ne, haka ma bangaskiya ba aikatawa matacciya ce.