YUSH 13

Za A Hallaka Ifraimu

1 Sa’ad da Ifraimu ta yi magana, mutane suka yi rawar jiki. An ɗaukaka ta cikin Isra’ila,

Amma ta yi laifi ta wurin bauta gunkin nan Ba’al,

Ta kuwa mutu.

2 Har yanzu suna ta ƙara yin zunubi,

Suna yi wa kansu gumaka na zubi,

Da gwaninta sukan yi gumaka da azurfarsu,

Dukansu aikin hannu ne.

Sukan ce, “Ku miƙa wa waɗannan hadayu!”

Mutane sukan sumbaci siffofin maruƙa.

3 Don haka za su zama kamar ƙāsashin da akan yi da safe,

Ko kuwa kamar raɓa mai kakkaɓewa da wuri.

Za su zama kamar ƙaiƙayi wanda ake shiƙarsa cikin iska a masussuka,

Ko kuwa kamar hayaƙin da yake fita ta bututu.

4 Ubangiji ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnku

Tun daga ƙasar Masar.

Banda ni ba ku san wani Allah ba,

Banda ni kuma ba wani mai ceto.

5 Ni ne wanda ya san ku a cikin jeji,

A ƙasar da take da ƙarancin ruwan sama.

6 Sa’ad da suka sami wurin kiwo, suka ƙoshi,

Sai suka yi girmankai,

Suka manta da ni.

7 Zan zama musu kamar zaki,

Kamar damisa zan yi kwanto a gefen hanya.

8 Zan auka musu kamar beyar,

Wadda aka ƙwace mata ‘ya’ya.

Zan yage ƙirjinsu, in cinye su kamar zaki,

Kamar mugun naman jeji zan yayyage su.

9 “Zan hallaka ku, ya mutanen Isra’ila!

Wane ne zai taimake ku?

10 Yanzu ina sarkinku da zai cece ku?

Ina kuma dukan shugabanninku da za su kāre ku?

Su waɗanda kuka roƙa, kun ce, ‘Ku naɗa mana sarki da shugabanni.’

11 Da fushina na naɗa muku sarki,

Da hasalata kuma na tuɓe shi.

12 “An ƙunshe muguntar Ifraimu,

Zunubinsa kuwa an ajiye shi a rumbu.

13 Naƙudar haihuwarsa ta zo,

Amma shi wawan yaro ne,

Bai fito daga mahaifar ba.

14 Zan fanshe su daga ikon lahira.

Zan fanshe su daga mutuwa.

Ya mutuwa, ina annobanki?

Ya kabari, ina halakarka?

Kan kawar da juyayi daga wurina.

15 Ko da yake Isra’ila tana bunƙasa kamar ciyayi,

Iskar gabas, wato iskar da za ta zo daga jeji,

Za ta busar da maɓuɓɓugarsu da idon ruwansu,

Za ta lalatar da abubuwa masu amfani da yake cikin taskarsu.

16 Samariya za ta ɗauki hakkin zunubinta,

Gama ta tayar wa Allahnta.

Za a kashe mutanenta da takobi.

Za a fyaɗa jariranta a ƙasa,

A kuma tsage matanta masu ciki.”