YUSH 14

Ana Roƙon Isra’ila Ta Komo wurin Ubangiji

1 Ya mutanen Isra’ila, ku komo wurin Ubangiji Allahnku,

Gama zunubinku ya sa kun yi tuntuɓe.

2 Ku komo wurin Ubangiji, ku roƙe shi,

Ku ce, “Ka gafarta mana zunubanmu,

Ka karɓe mu saboda alherinka,

Mu kuwa za mu yabe ka da bakinmu.

3 Assuriya ba za ta cece mu ba,

Ba kuwa za mu hau dawakai ba.

Ba za mu kuma ƙara ce da aikin hannuwanmu,

‘Kai ne Allahnmu,’ ba.

A wurinka ne maraya yakan sami jinƙai.”

Ubangiji Ya Yi wa Isra’ila Alkawarin Sabon Rai

4 Ubangiji ya ce, “Zan warkar musu da riddarsu.

Zan kuma ƙaunace su sosai,

Gama fushina zai huce.

5 Zan zama kamar raɓa ga Isra’ila,

Isra’ila za ta yi fure kamar lili,

Saiwarta za ta shiga kamar itacen al’ul.

6 Tohonta zai buɗo,

Kyanta zai zama kamar itacen zaitun,

Ƙashinta kuwa kamar itacen al’ul na Lebanon.

7 Waɗanda za su komo, za su zauna a inuwarta,

Za su yi noman hatsi da yawa.

Za su yi fure kamar kurangar inabi.

Ƙanshinsu zai zama kamar ruwan inabi na Lebanon.

8 Ya mutanen Ifraimu, me zan yi da gumaka?

Ni ne wanda yake amsa muku, mai lura da ku kuma.

Ni kamar itacen fir ne mai ganyaye kore shar.

Daga gare ni, kuke samun ‘ya’ya.”

9 Duk wanda yake da hikima, bari ya fahimci abubuwan nan.

Duk wanda yake da ganewa, bari ya san abubuwan nan,

Gama hanyoyin Ubangiji masu gaskiya ne,

Masu adalci kuwa za su yi tafiya a cikinsu,

Amma masu zunubi za su yi tuntuɓe a kansu.