YUSH 6

1 Mutane sun ce, “Zo, mu koma wurin Ubangiji,

Gama shi ne ya yayyaga,

Shi ne kuma zai warkar.

Shi ne ya yi mana rauni,

Shi ne kuma zai ɗaure raunin da maɗauri.

2 Bayan kwana biyu zai rayar da mu.

A rana ta uku kuwa zai tashe mu

Mu yi zammanmu a gabansa.

3 Mu nace domin mu san Ubangiji

Zuwansa tabbatacce ne kamar wayewar gari.

Zai zo wurinmu kamar ruwan sama,

Kamar ruwan bazara da yake shayar da ƙasa.”

Amsar Ubangiji

4 Ubangiji ya ce, “Me zan yi da ke, ya Ifraimu?

Me zan yi da ke, ya Yahuza?

Ƙaunarku tana kama da ƙāsashi,

Kamar kuma raɓar da take watsewa da wuri.

5 Domin haka na sassare su ta wurin annabawansu,

Na karkashe su da maganar bakina.

Hukuntaina suna kama da hasken da yake ketowa.

6 Gama ƙauna nake so, ba sadaka ba,

Sanin Allah kuma fiye da hadayu na ƙonawa.

7 “Amma sun ta da alkawarina kamar Adamu,

Sun ci amanata.

8 Gileyad gari ne na masu aikata mugunta.

Tana da tabban jini.

9 Kamar yadda mafasa sukan yi fakon mutum,

Haka nan firistoci suka haɗa kansu

Don su yi kisankai a hanyar Shekem,

Ai, sun aikata mugayen abubuwa.

10 Na ga abin banƙyama a cikin Isra’ila,

Karuwancin Ifraimu yana wurin,

Isra’ila ta ƙazantar da kanta.

11 “Ku kuma, ya mutanen Yahuza, an shirya muku ranar girbi,

A lokacin da zan mayar wa mutanena da dukiyarsu.”