YUSH 7

Zunubin Isra’ila da Tayarwarta

1 “Sa’ad da zan warkar da mutanen Isra’ila,

Sai zunubin Ifraimu da muguntar Samariya su bayyana,

Gama suna cin amana.

Ɓarawo yakan fasa, ya shiga,

‘Yan fashi suna fashi a fili,

2 Amma ba su tunani,

Cewa zan tuna da dukan muguntarsu.

Yanzu ayyukansu sun kewaye su,

Ina ganinsu.

3 “Suna faranta zuciyar sarki da muguntarsu,

Na shugabanni kuma da ƙarairayinsu.

4 Dukansu mazinata ne,

Suna kama da tanda da aka zafafa,

Wadda matoyi ya daina iza mata wuta,

Tun daga lokacin cuɗe kullu

Har zuwa lokacin da yisti ya tasar da shi.

5 A ranar bikin sarki,

Sukan sa sarki da shugabanni su bugu da ruwan inabi.

Yakan yi cuɗanya da shakiyai.

6 Zukatansu suna ƙuna da ƙullaƙulle kamar tanderu.

Fushinsu na ci dare farai,

Da safe fushinsu yana ci bal-bal kamar harshen wuta.

7 “Dukansu suna da zafi kamar tanderu.

Suna kashe masu mulkinsu.

Dukan sarakunansu sun faɗi.

Ba wanda ya kawo mini kuka.”

Ifraimu ta Haɗu da Al’ummai

8 Ubangiji ya ce, “Mutanen Ifraimu sun haɗa kansu da al’ummai,

Sun zama kamar wainar da ba a juya ba.

9 Baƙi sun cinye ƙarfinsu, su kuwa ba su sani ba,

Furfura ta faso musu, amma ba su sani ba.

10 Girmankan mutanen Isra’ila ya kai ƙararsu,

Duk da haka ba wanda ya komo wurin Ubangiji Allahnsu,

Ba su kuwa neme shi ba.

11 Ifraimu kamar kurciya take, marar wayo, marar hankali,

Takan tafi Masar da Assuriya neman taimako.

12 Lokacin da suke tafiya, zan shimfiɗa musu ragata,

Zan saukar da su ƙasa kamar yadda akan yi wa tsuntsun da yake tashi sama.

Zan hukunta su saboda mugayen ayyukansu.

13 “Tasu ta ƙare, gama sun ratse, sun rabu da ni.

Halaka za ta auka musu domin sun tayar mini.

Ko da yake zan cece su, duk da haka suna faɗar karya a kaina.

14 Ba su yi kuka gare ni da zuciya ɗaya ba,

Sa’ad da suke kuka a gadajensu,

Sun tsattsaga jikinsu domin abinci da ruwan inabi.

Sun yi mini tawaye.

15 Ko da yake na horar da su, na ƙarfafa damatsansu,

Duk da haka suna shirya mini maƙarƙashiya.

16 Sun juya mini baya, suna bin gunkin nan Ba’al.

Suna kama da tankwararren baka.

Za a kashe shugabanninsu da takobi

Saboda maganganunsu na fariya.

Za su zama abin ba’a a ƙasar Masar.”