ZAB 105

Allah da Jama’arsa

1 Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar girmansa,

Ku sanar wa sauran al’umma abubuwan da ya yi!

2 Ku raira masa waƙa, ku raira yabo gare shi,

Ku faɗi dukan abubuwa masu banmamaki da ya yi!

3 Ku yi murna saboda mu nasa ne,

Ku yi murna dukanku da kuke bauta wa Ubangiji!

4 Ku je wurin Ubangiji neman taimako,

Ku tsaya a gabansa koyaushe.

5-6 Ya ku zuriyar bawansa Ibrahim,

Ya ku zuriyar zaɓaɓɓensa Yakubu,

Ku tuna da mu’ujizansa masu girma, masu banmamaki,

Ku tuna kuma da hukuntai waɗanda ya yanke.

7 Shi Ubangiji, shi ne Allahnmu,

Umarnansa domin dukan duniya ne.

8 Zai cika alkawarinsa har abada,

Alkawaransa kuma don dubban zamanai,

9 Yarjejeniyar da ya yi da Ibrahim,

Da alkawarin da ya yi wa Ishaku.

10 Ubangiji ya yi madawwamin alkawari da Isra’ila,

Ya yi madawwamiyar yarjejeniya da Yakubu sa’ad da ya ce,

11 “Zan ba ka ƙasar Kan’ana,

Za ta zama mallakarka.”

12 Jama’ar Ubangiji kima ne,

Baƙi ne kuwa a ƙasar.

13 Suka yi ta yawo daga ƙasa zuwa ƙasa,

Daga wannan mulki zuwa wancan,

14 Amma bai yarda kowa ya zalunce su ba,

Ya tsauta wa sarakuna da yawa saboda su.

15 Ya ce, “Kada ku taɓi bayina, zaɓaɓɓu,

Kada ku cuci annabawana!”

16 Sa’ad da Ubangiji ya aukar da yunwa a ƙasarsu,

Ya kuma sa abincinsu duka ya ƙare,

17 Sai ya aika da Yusufu ya riga su zuwa,

Shi wanda aka sayar da shi kamar bawa.

18 Ƙafafunsa suka yi rauni saboda an ɗaure su da sarƙa,

Aka kuma sa wa wuyansa ƙuƙumi na baƙin ƙarfe,

19 Har kafin faɗar da ya yi, ta cika.

Maganar Ubangiji ta tabbatar da gaskiyar abin da ya faɗa.

20 Sa’an nan Sarkin Masar ya sake shi,

Mai mulkin dukan sauran al’umma ya ‘yantar da shi.

21 Ya sa shi ya lura da mulkinsa,

Ya sa shi ya yi mulki a bisa dukan ƙasar.

22 Ya ba shi cikakken iko bisa dukan ma’aikatan hukuma.

Ya ba shi ikon umartar mashawartansa.

23 Sa’an nan Yakubu ya tafi Masar,

Ya zauna a ƙasar.

24 Ubangiji ya sa jama’arsa suka hayayyafa da yawa,

Ya sa su fi ƙarfin maƙiyansu.

25 Ya sa Masarawa suka ƙi jinin jama’arsa,

Suka yi wa bayinsa munafunci.

26 Sai ya aiki bayinsa Musa da Haruna, waɗanda ya zaɓa.

27 Suka aikata manya manyan ayyuka na Allah,

Suka kuma yi ayyukan al’ajabi a Masar.

28 Ya aika da duhu a bisa ƙasar.

Musa da Haruna ba su tayar wa umarnansa ba.

29 Ya mai da ruwan kogunansu su zama jini,

Ya karkashe kifayensu duka.

30 Ƙasarsu ta cika da kwaɗi,

Har a fādar sarki.

31 Allah ya ba da umarni, sai ƙudaje da ƙwari

Suka cika dukan ƙasar.

32 Ya aiki ƙanƙara da tsawa a bisa ƙasarsu

Maimakon ruwan sama.

33 Ya lalatar da ‘ya’yan inabinsu da itatuwan ɓaurensu,

Ya kakkarya itatuwansu.

34 Ya ba da umarni, sai fāri suka zo,

Dubun dubbai da ba su ƙidayuwa.

35 Suka cinye dukan tsire-tsire na ƙasa.

Suka cinye dukan amfanin gonaki.

36 Ya karkashe dukan ‘ya’yan fari maza

Na dukan iyalan Masarawa.

37 Sa’an nan ya bi da Isra’ilawa, suka fita,

Suka kwashi azurfa da zinariya,

Dukansu kuma ƙarfafa ne lafiyayyu.

38 Masarawa suka yi murna da fitarsu,

Gama sun tsoratar da su.

39 Ya sa girgije ya yi wa jama’arsa inuwa,

Da dare kuma wuta ta haskaka musu.

40 Suka roƙa, sai aka ba su makware,

Ya ba su abinci daga sama da za su ci su ƙoshi.

41 Ya buɗe dutse, sai ruwa ya bulbulo,

Yana gudu cikin hamada kamar kogi.

42 Ya tuna da alkawarinsa mai tsarki

Wanda ya yi wa bawansa Ibrahim.

43 Haka kuwa ya bi da jama’arsa, suka fita suna raira waƙa,

Ya bi da zaɓaɓɓun jama’arsa, suna sowa ta farin ciki.

44 Ya ba su ƙasar baƙi,

Ya sa su gāje gonakinsu,

45 Don jama’arsa su yi biyayya da dokokinsa,

Su kuma kiyaye umarninsa.

Ku yabi Ubangiji!