ZAB 106

Tawayen Isra’ila

1 Ku yabi Ubangiji!

Ku yi wa Ubangiji godiya, gama nagari ne shi,

Ƙaunarsa madawwamiya ce.

2 Wa zai iya faɗar dukan manya manyan ayyuka da ya yi?

Wa zai iya yi masa isasshen yabo?

3 Masu farin ciki ne waɗanda suke biyayya da umarnansa,

Waɗanda kullayaumi suke aikata abin da yake daidai!

4 Ka tuna da ni sa’ad da za ka taimaki jama’arka, ya Ubangiji!

Ka sa ni cikinsu, sa’ad da za ka cece su.

5 Ka yardar mini in ga wadatar jama’arka,

In yi tarayya da jama’arka da farin cikinsu,

In yi farin ciki tare da waɗanda suke murna ta fāriya domin su naka ne.

6 Mun yi zunubi yadda kakanninmu suka yi,

Mugaye ne, mun aikata mugunta.

7 Kakanninmu a Masar

Ba su fahimci ayyukan Allah masu banmamaki ba,

Sau da yawa sukan manta da irin ƙaunar da ya nuna musu,

Suka tayar wa Mai Iko Dukka a Bahar Maliya.

8 Amma duk da haka ya cece su, kamar yadda ya alkawarta,

Domin ya nuna ikonsa mai girma.

9 Ya tsauta wa Bahar Maliya, ta ƙafe,

Har ya bi da jama’arsa su haye

Kamar a bisa busasshiyar ƙasa.

10 Ya cece su daga maƙiyansu,

Ya ƙwato su daga wurin abokan gābansu.

11 Ruwa ya cinye maƙiyansu,

Ba wanda ya tsira.

12 Sa’an nan jama’arsa suka gaskata alkawarinsa,

Suka raira yabo gare shi.

13 Amma nan da nan, suka manta da abin da ya yi,

Suka aikata, ba su jira shawararsa ba.

14 Suka cika da sha’awa cikin hamada,

Suka jarraba Allah,

15 Sai ya ba su abin da suka roƙa,

Amma ya aukar musu da muguwar cuta.

16 Can cikin hamada suka ji kishin Musa

Da Haruna, bayin Ubangiji, tsarkaka,

17 Sai ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan,

Ta binne Abiram da iyalinsa.

18 Wuta ta sauko bisa magoya bayansu,

Ta ƙone mugayen mutanen nan.

19 Suka ƙera ɗan maraƙi da zinariya a Horeb,

Suka yi masa sujada.

20 Suka musaya ɗaukakar Allah

Da siffar dabba mai cin ciyawa.

21 Suka manta da Allah wanda ya cece su,

Ta wurin manyan ayyuka da ya yi a Masar.

22 Kai, Allah ya aikata abubuwa masu ban al’ajabi a can!

Ga kuma abubuwa masu banmamaki da ya aikata a Bahar Maliya!

23 Saboda wannan Allah ya ce zai hallaka jama’arsa,

Amma Musa, zaɓaɓɓen bawansa, ya yi godo ga Allah,

Allah kuwa ya huce, bai hallaka su ba.

24 Sai suka ƙi ƙasan nan mai ni’ima,

Saboda ba su gaskata alkawarin Allah ba.

25 Suka zauna cikin alfarwansu suna ta gunaguni,

Sun ƙi su saurari Ubangiji.

26 Saboda haka ya yi musu kakkausan kashedi,

Cewa shi zai sa su duka su mutu a jejin,

27 Zai warwatsa zuriyarsu a cikin arna,

Ya bar su su mutu a baƙuwar ƙasa.

28 Sai jama’ar Allah suka taru suka shiga yi wa Ba’al sujada, a Feyor,

Suka ci hadayun da aka miƙa wa matattun alloli.

29 Suka tsokani Ubangiji, ya yi fushi saboda ayyukansu,

Mugawar cuta ta auka musu,

30 Amma Finehas ya tashi, ya yanke hukunci a kan laifin,

Aka kuwa kawar da annobar.

31 Tun daga lokacin nan ake ta tunawa da shi,

Saboda abin da ya yi.

Za a yi ta tunawa da shi a dukan zamanai masu zuwa.

32 Jama’ar Ubangiji suka sa ya yi fushi.

A maɓuɓɓugan Meriba,

Musa ya shiga uku saboda su.

33 Suka sa Musa ya husata ƙwarai,

Har ya faɗi abubuwan da bai kamata ya faɗa ba.

34 Suka ƙi su kashe arna,

Yadda Ubangiji ya umarta,

35 Amma suka yi aurayya da su,

Suka kwaikwayi halayen arnan.

36 Jama’ar Allah suka yi wa gumaka sujada.

Wannan kuwa ya jawo musu hallaka.

37 Suka miƙa ‘ya’yansu mata da maza hadaya ga allolin arna.

38 Suka karkashe mutane marasa laifi,

Wato ‘ya’yansu mata da maza.

Suka miƙa su hadaya ga gumakan Kan’ana,

Suka ƙazantar da ƙasar saboda kashe-kashenkan da suke yi.

39 Ta wurin ayyukansu, suka ƙazantar da kansu,

Suka zama marasa aminci ga Allah.

40 Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da jama’arsa,

Ransa bai ji daɗinsu ba.

41 Sai ya bar su ƙarƙashin ikon arna,

Abokan gābansu suka mallake su.

42 Abokan gābansu suka zalunce su,

Suka tilasta su, su yi musu biyayya.

43 Sau da yawa Ubangiji yakan ceci jama’arsa,

Amma sun fi so su yi masa tawaye,

Suna ta nutsawa can cikin zunubi.

44 Duk da haka Ubangiji ya ji su sa’ad da suka yi kira gare shi,

Ya kula da wahalarsu.

45 Saboda su ne ya tuna da alkawarinsa,

Ya sāke ra’ayinsa saboda ƙaunarsa mai yawa.

46 Ubangiji ya sa waɗanda suka kama su

Su ji tausayinsu.

47 Ka cece mu, ya Ubangiji Allahnmu,

Ka komo da mu daga cikin sauran al’umma,

Domin mu yabi sunanka mai tsarki,

Mu kuma yi murna mu yi maka godiya.

48 Sai mu yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila,

Mu yabe shi yanzu da har abada kuma!

Dukan jama’a za su amsa su ce, “Amin! Amin!”

Ku yabi Ubangiji!