ZAB 107

Ubangiji Ne Mai Kuɓutarwa daga Wahala

1 Ku gode wa Ubangiji, gama shi nagari ne,

Ƙaunarsa madawwamiya ce!

2 Ku zo mu yabi Ubangiji tare,

Dukanku waɗanda ya fansa,

Gama ya ƙwato ku daga maƙiyanku.

3 Ya komo da ku daga ƙasashen waje,

Daga gabas da yamma, kudu da arewa.

4 Waɗansu suka yi ta kai da kawowa a hamada inda ba hanya,

Sun kasa samun hanyar da za ta kai su garin da za su zauna a ciki.

5 Suka yi ta fama da yunwa, da ƙishirwa,

Suka fid da zuciya ga kome.

6 Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,

Ya kuwa cece su daga wahalarsu.

7 Ya fisshe su, ya bi da su sosai,

Zuwa birnin da za su zauna.

8 Dole ne su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa,

Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu!

9 Ya shayar da waɗanda suke jin ƙishirwa,

Ya kuma ƙosar da mayunwata da alheransa.

10 Waɗansu suna zaune cikin duhu da inuwar mutuwa,

‘Yan sarƙa suna shan wahala da sarƙoƙi,

11 Saboda sun tayar, sun ƙi bin umarnan Allah Maɗaukaki,

Sun kuwa ƙi koyarwarsa.

12 Suka gaji tiƙis saboda tsananin aiki,

Za su faɗi ƙasa, ba mataimaki.

13 A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,

Ya kuwa cece su daga wahalarsu.

14 Ya fisshe su daga cikin duhu da inuwar mutuwa,

Ya tsintsinka sarƙoƙinsu.

15 Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa,

Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.

16 Ya kakkarya ƙofofin da aka yi da tagulla.

Ya kuma ragargaza ƙyamaren da aka yi da baƙin ƙarfe.

17 Waɗansu suka yi ciwo sabili da zunubansu,

Suna ta shan wahala saboda muguntarsu.

18 Ba su so su ga abinci,

Sun kusa mutuwa.

19 A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,

Ya kuwa cece su daga azabar da suke sha.

20 Da umarninsa ya warkar da su,

Ya cece su daga kabari.

21 Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa,

Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.

22 Dole su gode masa, su miƙa masa hadayu,

Su raira waƙoƙin murna,

Su faɗi dukan abin da ya yi!

23 Waɗansu suka yi tafiya a teku da jirage,

Suna samun abin zaman garinsu daga tekuna.

24 Suka ga abin da Ubangiji ya aikata,

Ayyukansa masu banmamaki waɗanda ya yi a tekuna.

25 Ya ba da umarni, sai babbar iska ta tashi,

Ta fara hurowa, ta sa raƙuman ruwa su tashi.

26 Aka ɗaga jiragen ruwa sama,

Sa’an nan suka tsinduma cikin zurfafa.

Da mutanen suka ga irin hatsarin da suke ciki,

Sai zuciyarsu ta karai.

27 Suka yi ta tuntuɓe suna ta tangaɗi kamar bugaggu,

Gwanintarsu duka ta zama ta banza.

28 Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,

Ya kuwa cece su daga azabarsu.

29 Ya sa hadiri ya yi tsit,

Raƙuman ruwa kuma suka yi shiru.

30 Suka yi murna saboda wurin ya yi shiru,

Ya kuma kai su kwatar jiragen ruwa lafiya,

Wurin da suke so.

31 Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa,

Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.

32 Dole su yi shelar girmansa cikin taron jama’a,

Su kuma yabe shi a gaban majalisar dattawa.

33 Ubangiji ya sa koguna suka ƙafe ƙaƙaf,

Ya hana maɓuɓɓugai su gudana.

34 Ya mai da ƙasa mai dausayi ta zama mai gishiri, marar amfani,

Saboda muguntar waɗanda suke zaune a can.

35 Ya sāke hamada ta zama tafkunan ruwa,

Ya kuma mai da busasshiyar ƙasa ta zama maɓuɓɓugai masu gudana.

36 Ya bar mayunwata su zauna a can,

Suka kuwa gina birni don su zauna a ciki.

37 Suka shuka gonaki suka dasa kurangar inabi,

Waɗanda suka ba da amfani mai yawan gaske.

38 Ya sa wa jama’arsa albarka,

Suka kuwa haifi ‘ya’ya da yawa.

Bai bar garkunan shanunsu su ragu ba.

39 Sa’ad da aka ci nasara a kan jama’ar Allah,

Aka ƙasƙantar da su ta wurin mugun zalunci,

Da wahalar da aka yi musu.

40 Sai Allah ya wulakanta waɗanda suka zalunci jama’arsa.

Ya sa su suka yi ta kai da kawowa

A hamada inda ba hanya.

41 Ya tsamo masu bukata daga cikin baƙin cikinsu,

Ya sa iyalansu su riɓaɓɓanya kamar garkunan tumaki.

42 Da adalai suka ga wannan, sai suka yi murna,

Mugaye kuwa aka rufe bakinsu.

43 Da ma a ce masu hikima

Za su yi tunani a kan waɗannan abubuwa,

Da ma kuma su yarda

Da madawwamiyar ƙaunar Ubangiji.