ZAB 108

Addu’ar Neman Tsari daga Maƙiya

1 A shirye nake, ya Allah,

Na shirya sosai!

Zan raira waƙa in yabe ka!

Ka farka, ya raina!

2 Ku farka, ya molona da garayata!

Zan farkar da rana!

3 Zan yi maka godiya a tsakiyar sauran al’umma, ya Ubangiji!

Zan yabe ka a tsakiyar kabilai!

4 Madawwamiyar ƙaunarka ta kai har can saman sammai,

Amincinka kuma ya kai sararin sammai.

5 Ya Allah, ka bayyana girmanka a sararin sama,

Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!

6 Ka cece mu da ƙarfinka, ka amsa addu’ata,

Domin jama’ar da kake ƙauna ta sami cetonka.

7 A tsattsarkan wurinsa, Allah ya faɗa ya ce,

“Da nasara zan raba Shekem,

Da nasara kuma zan rarraba Sukkot ga jama’ata.

8 Gileyad tawa ce, har da Manassa ma,

Ifraimu ne kwalkwalina,

Yahuza kuma sandana ne na sarauta.

9 Amma zan yi amfani da Mowab kamar kwanon wanki,

Edom kuwa kamar akwatin takalmina.

Zan yi sowar nasara a kan Filistiyawa.”

10 Ya Allah, wa zai kai ni birni mai kagara?

Wa zai kai ni Edom?

11 Da gaske ka yashe mu ke nan?

Ba za ka yi tafiya

Tare da sojojinmu ba?

12 Ka taimake mu, mu yaƙi abokin gāba,

Domin taimako irin na mutum banza ne!

13 Idan Allah yana wajenmu,

Za mu yi nasara,

Zai kori abokan gābanmu.