ZAB 109

Kukan Mutumin da Yake Shan Wahala

1 Ina yabonka, ya Allah, kada ka yi shiru!

2 Mugaye da maƙaryata sun tasar mini,

Suna ta faɗar ƙarairayi a kaina.

3 Suna faɗar mugayen abubuwa a kaina.

Suna tasar mini ba dalili.

4 Suna ƙina ko da yake ina ƙaunarsu,

Har ina yi musu addu’a.

5 Sukan sāka mini alheri da mugunta,

Sukan sāka mini ƙauna da ƙiyayya.

6 Ka zaɓi lalataccen mutum ya shara’anta maƙiyina,

Ka sa ɗaya daga cikin maƙiyansa

Ya gabatar da ƙararsa.

7 Ka sa a same shi da laifi a shari’ar da ake yi masa,

Ka sa har addu’ar da yake yi

Ta zama babban laifi!

8 Ka aukar masa da ajalinsa nan da nan,

Ka sa wani ya ɗauki matsayinsa!

9 Ka sa ‘ya’yansa su zama marayu,

Matarsa kuwa ta zama gwauruwa!

10 Ka sa ‘ya’yansa su rasa gidan zama, su riƙa yawon bara.

Ka sa a kore su daga kufan da suke zaune!

11 Ka sa waɗanda suke binsa bashi su kwashe

Dukan abin da yake da shi.

Ka sa baƙi su kwashe dukan abin da ya sha wahalar nema.

12 Ka sa kada kowa ya yi masa alheri sam,

Kada ka bar kowa ya lura da marayunsa.

13 Ka sa dukan zuriyarsa su mutu,

Har a manta da sunansa a tsara mai zuwa.

14 Sai ka tuna, ya Ubangiji, da muguntar kakanninsa,

Kada ka manta da zunuban mahaifiyarsa.

15 Ka tuna da zunubansu kullayaumin, ya Ubangiji,

Amma su kansu a manta da su ɗungum!

16 Gama mutumin nan bai taɓa tunanin yin alheri ba,

Yakan tsananta wa talakawa, da matalauta, da kasassu, har ya kashe su.

17 Yana jin daɗin la’antarwa, ka sa a la’anta shi!

Ba ya son sa albarka, ka sa kada kowa ya sa masa albarka!

18 Yakan la’antar a sawwaƙe kamar yadda yake sa tufafinsa.

Ka sa la’antarwa da yake yi

Su jiƙa shi kamar ruwa,

Su shiga har ƙasusuwansa kamar mai,

19 Su lulluɓe shi kamar tufa,

Su kuma kewaye shi kamar ɗamara.

20 Ya Ubangiji, ka sa haka,

Wato ya zama yadda za a hukunta wa maƙiyana ke nan,

Waɗanda suke faɗar mugayen abubuwa a kaina!

21 Amma ya Ubangiji, Allahna, ka taimake ni,

Yadda ka alkawarta,

Ka cece ni sabili da alherin ƙaunarka.

22 Ni talaka ne, matalauci,

Na ji zafi ƙwarai a can zuciyata.

23 Na kusa ɓacewa kamar inuwar maraice,

An hurar da ni can kamar ƙwaro.

24 Gwiwoyina sun yi suwu saboda rashin abinci,

Jikina kuma ya rame, ba shi da ƙarfi.

25 Sa’ad da mutane suka gan ni sun yi mini ba’a,

Suna kaɗa kai saboda raini.

26 Ka taimake ni, ya Ubangiji Allahna,

Ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka!

27 Ka sa maƙiyana su sani,

Kai ne Mai Cetona.

28 Watakila su la’anta ni,

Amma kai za ka sa mini albarka,

Ka sa a kori waɗanda suke tsananta mini.

Da ma ka sa ni da nake bawanka, in yi murna.

29 Ka sa kunya ta rufe maƙiyana,

Ka sa su sa kunyarsu kamar riga.

30 Da murya mai ƙarfi zan yi wa Ubangiji godiya.

Zan yabe shi a taron jama’a,

31 Saboda yakan kāre talaka,

Domin ya cece shi daga waɗanda

Suka sa masa laifin mutuwa.