ZAB 112

Wadatar Mai Tsoron Allah

1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

Mai farin ciki ne mutumin da yake tsoron Ubangiji,

Mai farin ciki ne shi wanda yake jin daɗin yin biyayya da umarnansa.

2 ‘Ya’yansa za su zama manyan ƙasar,

Zuriyar mutumin kirki za ta yi albarka.

3 Iyalinsa za su zama attajirai masu dukiya,

Adalcinsa zai tabbata har abada.

4 Haske yakan haskaka wa mutanen kirki a cikin duhu,

Da waɗanda suke yin alheri, da jinƙai, da gaskiya.

5 Mai farin ciki ne mutumin da yakan ba da rance hannu sake,

Wato wanda yake yin harkarsa da gaskiya.

6 Mutumin kirki ba zai kāsa ba daɗai,

Ba za a taɓa mantawa da shi ba.

7 Ba ya tsoron jin mugun labari,

Bangaskiyarsa tana da ƙarfi,

Ga Ubangiji yake dogara.

8 Ba shi da damuwa ko tsoro,

Ya tabbata zai ga faɗuwar maƙiyansa.

9 Yakan bayar ga matalauta hannu sake,

Alherinsa kuwa dawwamamme ne.

Zai zama mai iko wanda ake girmamawa.

10 Sa’ad da mugaye suka ga wannan,

Sai suka tunzura, suka harare shi da fushi, suka ɓace,

Sa zuciyarsu ta ƙare har abada.