ZAB 113

Yabon Alherin Ubangiji

1 Yabo Ya tabbata ga Ubangiji!

Ku bayin Ubangiji,

Ku yabi sunansa!

2 Za a yabi sunansa yanzu da har abada!

3 Daga gabas zuwa yamma a yabi sunan Ubangiji!

4 Ubangiji yake mulkin dukan sauran al’umma,

Ɗaukakarsa tana bisa kan sammai.

5 Ba wani kamar Ubangiji Allahnmu.

Yana zaune a can ƙwanƙolin sama,

6 Amma ya duba ƙasa,

Ya dubi sammai da duniya.

7 Yakan ɗaga talakawa daga ƙura,

Yakan ɗaga matalauta daga cikin azabarsu.

8 Yakan sa su zama abokan sarakuna,

Sarakunan jama’arsa.

9 Yakan girmama matar da ba ta haihuwa a gidanta,

Yakan sa ta yi farin ciki ta wurin ba ta ‘ya’ya.

Yabo ya tabbata ga Ubangiji!