ZAB 114

Waƙar Idin Ƙetarewa

1 Sa’ad da jama’ar Isra’ila suka bar Masar,

Sa’ad da zuriyar Yakubu suka bar baƙuwar ƙasar nan,

2 Yahuza ya zama tsattsarkar jama’ar Ubangiji,

Isra’ila ya zama abin mallakarsa.

3 Bahar Maliya da ya duba, sai ya gudu,

Kogin Urdun ya daina gudu.

4 Duwatsu suka yi ta tsalle kamar awaki,

Tuddai kuwa suka yi ta tsalle suna kewayawa kamar tumaki.

5 Me ya faru ne, ya teku, da ya sa ki gudu?

Kai fa Urdun, me ya sa ka daina gudu?

6 Ku fa duwatsu, me ya sa kuka yi ta tsalle kamar awaki?

Tuddai, me ya sa kuka yi ta tsalle,

Kuna kewayawa kamar tumaki?

7 Ki yi rawar jiki, ya ke duniya,

Saboda zuwan Ubangiji,

A gaban Allah na Yakubu,

8 Wanda ya sa duwatsu su zama tafkunan ruwa,

Ya kuma sa kogwannin duwatsu su zama maɓuɓɓugai,

Masu bulbulo da ruwa.