ZAB 117

Yabo ga Ubangiji saboda Madawwamiyar Ƙaunarsa

1 Ku yabi Ubangiji, ku dukan sauran al’ummai!

Ku yabe shi, ku dukan kabilai!

2 Madawwamiyar ƙaunarsa, da ƙarfi take,

Amincinsa kuma tabbatacce ne har abada.

Yabo ya tabbata ga Ubangiji!