ZAB 118

Addu’ar Godiyar domin Cin Nasara

1 Ku gode wa Ubangiji,

Domin shi mai alheri ne,

Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.

2 Bari jama’ar Isra’ila su ce,

“Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”

3 Bari dukan firistoci na Allah su ce,

“Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”

4 Bari dukan waɗanda suke tsoronsa su ce,

“Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”

5 A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji

Ya kuwa amsa mini, ya kuɓutar da ni.

6 Ubangiji yana tare da ni, ba zan ji tsoro ba.

Me mutane za su iya yi mini?

7 Ubangiji ne yake taimakona,

Zan kuwa ga fāɗuwar maƙiyana da idona.

8 Gwamma a dogara ga Ubangiji,

Da a dogara ga mutane.

9 Gwamma a dogara ga Ubangiji,

Da a dogara ga shugabanni na mutane kawai.

10 Ma ƙiya da yawa sun kewaye ni,

Amma na hallaka su ta wurin ikon Ubangiji!

11 Suka kewaye ni a kowane gefe

Amma na hallaka su ta wurin ikon Ubangiji!

12 Suka rufe ni kamar ƙudan zuma,

Amma suka ƙone nan da nan kamar wutar jeji,

Ta wurin ikon Ubangiji na hallaka su!

13 Aka auko mini da tsanani,

Har aka kore ni,

Amma Ubangiji ya taimake ni.

14 Ubangiji yakan ba ni iko, ya ƙarfafa ni,

Shi ne Mai Cetona!

15 Ku kasa kunne ga sowar murna ta nasara

A cikin alfarwan jama’ar Allah.

“Ikon Ubangiji mai girma ne ya aikata wannan!

16 Ikonsa ne ya kawo mana nasara,

Babban ikonsa a wurin yaƙi!”

17 Ba zan mutu ba, amma rayuwa zan yi,

Don in ba da labarin abin da Ubangiji ya yi.

18 Ya hukunta ni da hukunci mai tsanani,

Amma bai kashe ni ba.

19 A buɗe mini ƙofofin Haikali,

Zan shiga ciki in yabi Ubangiji!

20 Wannan ƙofar Ubangiji ce,

Sai adalai kaɗai suke shiga ciki!

21 Ina yabonka, ya Ubangiji, domin ka ji ni,

Domin ka ba ni nasara!

22 Dutsen da magina suka ƙi, wai ba shi da amfani,

Sai ya zama shi ya fi duka amfani.

23 Ubangiji ne ya yi haka,

Wannan kuwa abin banmamaki ne!

24 Wace irin rana ce haka da Ubangiji ya ba mu!

Bari mu yi farin ciki, mu yi biki!

25 Ka cece mu, ya Ubangiji, ka cece mu!

Ka ba mu nasara, ya Ubangiji!

26 Allah yakan sa wa wanda ya zo da sunan Ubangiji albarka!

Daga Haikalin Ubangiji muke yabonka!

27 Ubangiji shi ne Allah, yana yi mana alheri,

Ku ɗauki hadayunku ku yi ta idi,

Ku ɗaura su a zankayen bagade.

28 Kai ne Allahna, kai nake yi wa godiya,

Zan yi shelar girmanka.

29 Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne,

Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.