ZAB 119

Mafificiyar Shari’ar Ubangiji

1 Masu farin ciki ne, marasa laifi cikin zamansu,

Waɗanda suke zamansu bisa ga dokar Ubangiji.

2 Masu farin ciki ne waɗanda suke bin umarnansa,

Waɗanda suke yi masa biyayya da zuciya ɗaya.

3 Hakika ba su yin laifi,

Sukan yi tafiya a hanyoyin Ubangiji.

4 Kai ka ba mu dokokinka,

Ka kuwa faɗa mana mu kiyaye su da aminci.

5 Na sa zuciya zan yi aminci,

Game da kiyaye dokokinka!

6 Idan na kula da dukan umarnanka,

To, ba zan kasa kaiwa ga burina ba.

7 Zan yabe ka da tsattsarkar zuciya,

A sa’ad da na fahimci ka’idodinka masu adalci.

8 Zan yi biyayya da dokokinka,

Ko kusa kada ka kashe ni!

Biyayya ga Shari’ar Ubangiji

9 Ƙaƙa saurayi zai kiyaye ransa da tsarki?

Sai ta wurin biyayya da umarnanka.

10 Da zuciya ɗaya nake ƙoƙarin bauta maka,

Ka kiyaye ni daga rashin biyayya da umarnanka!

11 Na riƙe maganarka a zuciyata,

Don kada in yi maka zunubi.

12 Ina yabonka, Ya Ubangiji,

Ka koya mini ka’idodinka!

13 Zan ta da murya,

In maimaita dukan dokokin da ka bayar.

14 Ina murna da bin umarnanka,

Fiye da samun dukiya mai yawa.

15 Nakan yi nazarin umarnanka,

Nakan kuma yi bimbinin koyarwarka.

16 Ina murna da dokokinka,

Ba zan manta da umarnanka ba.

Farin Ciki da Dokar Ubangiji

17 Ka yi mini alheri, ni bawanka,

Domin in rayu in yi biyayya da koyarwarka.

18 Ka buɗe idona

Domin in ga gaskiyar shari’arka mai banmamaki.

19 Zamana a nan duniya na ɗan lokaci kaɗan ne.

Kada ka ɓoye mini umarnanka!

20 Zuciyata ta ƙosa saboda marmari,

A kowane lokaci ina so in san hukuntanka.

21 Kakan tsauta wa masu girmankai,

La’anannu ne waɗanda suka ƙi bin umarnanka.

22 Ka kuɓutar da ni daga cin mutuncinsu da raininsu,

Domin na kiyaye dokokinka.

23 Ko da sarakuna za su taru

Su shirya mini maƙarƙashiya,

Duka da haka, ni bawanka,

Zan yi nazarin ka’idodinka.

24 Umarnanka suna faranta mini rai,

Su ne mashawartana.

Ƙudurin yin Biyayya ga Dokar Ubangiji

25 Ina kwance cikin ƙura, an yi nasara da ni,

Ka wartsakar da ni kamar yadda ka alkawarta!

26 Na hurta dukan abin da na aikata, ka kuwa amsa mini,

Ka koya mini ka’idodinka!

27 Ka koya mini yadda zan yi biyayya da dokokinka,

In kuma yi nazarin koyarwarka mai banmamaki.

28 Ɓacin rai ya ci ƙarfina,

Ka ƙarfafa ni, kamar yadda ka alkawarta.

29 Ka kiyaye ni daga bin muguwar hanya,

Ta wurin alherinka, ka koya mini dokarka.

30 Na yi niyya in yi biyayya,

Na mai da hankali ga ka’idodinka.

31 Na bi umarnanka, ya Ubangiji,

Kada ka sa in kasa ci wa burina!

32 Ina ɗokin yin biyayya da umarnanka,

Gama za ka ƙara mini fahimi.

Addu’ar Neman Fahimi

33 Ka koya mini ma’anar dokokinka, ya Ubangiji,

Zan kuwa yi biyayya da su a kowane lokaci.

34 Ka fassara mini dokarka, ni kuwa zan yi biyayya da ita,

Zan kiyaye ta da zuciya ɗaya.

35 Ka bishe ni a hanyar umarnanka,

Domin a cikinsu nakan sami farin ciki

36 Ka sa ni in so yin biyayya da ka’idodinka,

Fiye da samun dukiya.

37 Ka kiyaye ni daga mai da hankali ga abin da yake marar amfani,

Ka yi mini alheri kamar yadda ka alkawarta.

38 Ka tabbatar da alkawarin da ka yi mini, ni bawanka,

Irin wanda kakan yi wa waɗanda suke tsoronka.

39 Ka kiyaye ni daga cin mutuncin da nake tsoro,

Ka’idodinka suna da amfani ƙwarai!

40 Ina so in yi biyayya da umarnanka,

Gama kai mai adalci ne,

Ka yi mini alheri!

Dogara ga Dokar Ubangiji

41 Ka nuna mini yawan ƙaunar da kake yi mini, ya Ubangiji,

Ka cece ni bisa ga alkawarinka.

42 Sa’an nan zan amsa wa waɗanda suke cin mutuncina,

Domin na dogara ga maganarka.

43 Ka ba ni iko in iyar da saƙonka na gaskiya a kowane lokaci,

Gama sa zuciyata tana ga hukuntanka.

44 Kullum zan yi biyayya da dokarka har abada abadin!

45 Zan rayu da cikakken ‘yanci,

Gama na yi ƙoƙari in kiyaye ka’idodinka.

46 Zan hurta umarnanka ga sarakuna,

Ba kuwa zan ji kunya ba.

47 Ina murna in yi biyayya da umarnanka,

Saboda in ƙaunarsu.

48 Ina girmama umarnanka, ina kuwa ƙaunarsu,

Zan yi ta tunani a kan koyarwarka.

Amincewa da Shari’ar Ubangiji

49 Ka tuna da alkawarin da ka yi mini, ni bawanka,

Ka ƙarfafa zuciyata.

50 Ko ina shan wahala, ana ta’azantar da ni,

Saboda alkawarinka yana rayar da ni.

51 Masu girmankai suna raina ni,

Amma ban rabu da dokarka ba.

52 Na tuna da koyarwar da ka yi mini a dā,

Sukan kuwa ta’azantar da ni, ya Ubangiji.

53 Haushi ya kama ni sosai,

Sa’ad da na ga mugaye suna keta dokarka.

54 Ina zaune can nesa da gidana na ainihi,

Sai na ƙago waƙoƙi a kan umarnanka.

55 Da dare nakan tuna da kai, ya Ubangiji,

Ina kuwa kiyaye dokarka.

56 Wannan shi ne farin cikina,

In yi biyayya da umarnanka.

Tunani a kan Shari’ar Ubangiji

57 Kai kaɗai nake so, ya Ubangiji,

Na yi alkawari in yi biyayya da dokokinka.

58 Ina roƙonka da zuciya ɗaya,

Ka yi mini jinƙai kamar yadda ka alkawarta!

59 Na yi tunani a kan ayyukana,

Na yi alkawari in bi ka’idodinka.

60 Ba tare da ɓata lokaci ba,

Zan gaggauta in kiyaye umarnanka.

61 Mugaye sun ɗaure ni tam da igiyoyi,

Amma ba zan manta da dokarka ba.

62 Da tsakar dare nakan farka,

In yabe ka saboda hukuntanka masu adalci.

63 Ina abuta da duk waɗanda suke bauta maka,

Da duk waɗanda suke kiyaye dokokinka.

64 Ya Ubangiji, duniya ta cika da madawwamiyar ƙaunarka,

Ka koya mini umarnanka!

Amfanin Shari’ar Ubangiji

65 Kana cika alkawarinka, ya Ubangiji,

Kana kuwa yi mini alheri, ni bawanka.

66 Ka ba ni hikima da ilimi

Domin ina dogara ga umarnanka.

67 Kafin ka hore ni nakan yi kuskure,

Amma yanzu ina biyayya da maganarka.

68 Managarci ne kai, mai alheri ne kuma,

Ka koya mini umarnanka!

69 Masu girmankai sun faɗi ƙarairayi a kaina,

Amma da zuciya ɗaya nake biyayya da ka’idodinka.

70 Waɗannan mutane ba su da ganewa,

Amma ni ina murna da dokarka.

71 Horon da aka yi mini ya yi kyau,

Domin ya sa na koyi umarnanka.

72 Dokar da ka yi

Muhimmiya ce a gare ni,

Fiye da dukan dukiyar duniya.

Adalcin Shari’ar Ubangiji

73 Kai ne ka halicce ni, ka kuma kiyaye ni lafiya,

Ka ba ni ganewa, don in koyi dokokinka.

74 Waɗanda suke tsoronka za su yi murna sa’ad da suka gan ni,

Saboda ina dogara ga alkawarinka.

75 Na sani ka’idodinka na adalci ne, ya Ubangiji,

Ka hore ni, domin kai mai aminci ne.

76 Ka sa madawwamiyar ƙaunarka ta ta’azantar da ni,

Kamar yadda ka alkawarta mini, ni bawanka.

77 Ka yi mini jinƙai, zan rayu,

Saboda ina murna da dokarka.

78 Ka kunyatar da masu girmankai

Saboda sun ba da shaidar zur a kaina,

Amma ni, zan yi tunani a kan ka’idodinka.

79 Ka sa waɗanda suke tsoronka su zo gare ni,

Da waɗanda suka san umarnanka.

80 Ka sa in yi cikakkiyar biyayya da umarnanka,

Sa’an nan zan tsere wa shan kunyar faɗuwa.

Addu’ar Neman Ceto

81 Na tafke, ya Ubangiji, jira nake ka cece ni,

Na dogara ga maganarka.

82 Idanuna sun gaji da zuba ido ga alkawarinka.

Roƙo nake, “Sai yaushe za ka taimake ni?”

83 Na zama marar amfani kamar salkar ruwan inabi wanda aka jefar da ita,

Duk da haka ban manta da umarnanka ba.

84 Har yaushe zan yi ta jira?

Yaushe za ka yi wa waɗanda suke tsananta mini hukunci?

85 Masu girmankai, waɗanda ba su biyayya da dokarka,

Sun haƙa wushefe don su kama ni.

86 Umarnanka duka, abin dogara ne,

Mutane suna tsananta mini da ƙarairayi,

Ka taimake ni!

87 Sun kusa ci wa burinsu na su kashe ni,

Amma ban raina ka’idodinka ba.

88 Saboda madawwamiyar ƙaunarka, ka yi mini alheri,

Domin in yi biyayya da dokokinka.

Gaskata Shari’ar Ubangiji

89 Maganarka tabbatacciya ce, ya Ubangiji,

A kafe take a Sama.

90 Amincinka ya tabbata har abada,

Ka kafa duniya a inda take, tana nan kuwa a wurin.

91 Dukan abubuwa suna nan har wa yau saboda umarninka,

Domin su duka bayinka ne.

92 Da ba domin dokarka ita ce sanadin farin cikina ba,

Da na mutu saboda hukuncin da na sha.

93 Faufau ba zan raina ka’idodinka ba,

Gama saboda su ka bar ni da rai.

94 Ni naka ne, ka cece ni!

Na yi ƙoƙari in yi biyayya da umarnanka.

95 Mugaye suna jira su kashe ni,

Amma zan yi ta tunani a kan dokokinka.

96 Na koya cewa ba wani abu da yake cikakke,

Amma umarninka ba shi da iyaka.

Ƙaunar Shari’ar Ubangiji

97 Ga yadda nake ƙaunar dokarka!

Ina ta tunani a kanta dukan yini.

98 Umarninka yana tare da ni a kowane lokaci,

Ya sa ni in yi hikima fiye da dukan maƙiyana.

99 Ganewata ta fi ta dukan malamaina,

Saboda ina ta tunani a kan koyarwarka.

100 Na fi tsofaffi hikima,

Saboda ina biyayya da umarnanka.

101 Nakan guje wa halin mugunta

Saboda ina so in yi biyayya da maganarka.

102 Ban raina koyarwarka ba

Saboda kai ne ka koya mini.

103 Ɗanɗanon ka’idodinka akwai zaƙi,

Har sun fi zuma zaƙi!

104 Na ƙaru da hikima daga dokokinka,

Saboda haka ina ƙin dukan halin da yake ba daidai ba.

Haske daga Shari’ar Ubangiji

105 Maganarka fitila ce wadda za ta bi da ni,

Haske ne kuma a kan hanyata.

106 Zan cika muhimmin alkawarina,

In yi biyayya da koyarwarka mai adalci.

107 Azabaina, ya Ubangiji, suna da yawa,

Ka rayar da ni kamar yadda ka alkawarta!

108 Ka karɓi addu’ata ta godiya, ya Ubangiji,

Ka koya mini umarnanka.

109 Kullum a shirye nake in kasai da raina,

Ban manta da umarninka ba.

110 Mugaye sun kafa mini tarko,

Amma ban yi rashin biyayya da umarnanka ba.

111 Umarnanka nawa ne har abada, Su ne murnar zuciyata.

112 Na ƙudura zan yi biyayya da ka’idodinka,

Har ranar mutuwata.

Akwai Lafiya ga Bin Shari’ar Ubangiji

113 Ina ƙin waɗanda ba su yi maka aminci,

Amma ina ƙaunar dokarka.

114 Kai ne kake kāre ni, kake kuma kiyaye ni,

Ina sa zuciya ga alkawarinka.

115 Ku rabu da ni, ku masu zunubi!

Zan yi biyayya da umarnan Allahna.

116 Ka ƙarfafa ni kamar yadda ka alkawarta, zan kuwa rayu,

Kada ka bar ni in kasa ci wa burina!

117 Ka riƙe ni, sai in zauna lafiya,

Koyaushe zan mai da hankali ga umarnanka.

118 Ka rabu da dukan waɗanda ba su biyayya da dokokinka,

Dabarunsu na yaudara banza ne.

119 Kakan yi banza da duk mai mugunta,

Don haka ina ƙaunar koyarwarka.

120 Saboda kai, nake jin tsoro,

Na cika da tsoro saboda shari’unka.

Biyayya da Shari’ar Ubangiji

121 Na yi abin da yake daidai mai kyau,

Kada ka bar ni a hannun maƙiyana!

122 Sai ka yi alkawari za ka taimaki bawanka,

Kada ka bar masu girmankai su wahalshe ni!

123 Idanuna sun gaji da duban hanyar cetonka,

Ceton da ka alkawarta.

124 Ka bi da ni bisa ga tabbatacciyar ƙaunarka,

Ka koya mini umarnanka.

125 Ni bawanka ne, don haka ka ba ni ganewa,

Don in san koyarwarka.

126 Ya Ubangiji, lokaci ya yi da za ka yi wani abu,

Saboda mutane sun ƙi yin biyayya da dokarka!

127 Ina ƙaunar umarnanka, fiye da zinariya,

Fiye da zinariya tsantsa.

128 Saboda haka ina bin dukan koyarwarka,

Ina kuwa ƙin dukan mugayen al’amura.

Niyyar yin Biyayya da Shari’ar

129 Koyarwarka tana da ban al’ajabi,

Da zuciya ɗaya nake biyayya da su.

130 Fassarar koyarwarka takan ba da haske,

Takan ba da hikima ga wanda bai ƙware ba.

131 Ina haki da baki a buɗe,

Saboda marmarin da nake yi wa umarnanka.

132 Ka juyo wurina ka yi mini jinƙai,

Kamar yadda kakan yi wa masu ƙaunarka.

133 Kada ka bar ni in fāɗi kamar yadda ka alkawarta,

Kada ka bar mugunta ta rinjaye ni.

134 Ka cece ni daga waɗanda suke zaluntata,

Domin in yi biyayya da umarnanka.

135 Ka sa mini albarka da kasancewarka tare da ni,

Ka koya mini dokokinka.

136 Hawayena suna malalowa kamar kogi,

Saboda jama’a ba su biyayya da shari’arka ba.

Adalcin Shari’ar Ubangiji

137 Kai mai adalci ne, ya Ubangiji,

Dokokinka kuma daidai ne,

138 Ka’idodin da ka bayar kuwa dukansu masu kyau ne,

Daidai ne kuwa.

139 Fushi yana cina kamar wuta,

Saboda maƙiyana ba su kula da umarnanka ba.

140 Alkawarinka ba ya tashi!

Bawanka yana ƙaunar alkawarinka ƙwarai!

141 Ni ba kome ba ne, rainanne ne,

Amma ban ƙi kula da ka’idodinka ba.

142 Adalcinka zai tabbata har abada,

Dokarka gaskiya ce koyaushe.

143 A cike nake da wahala da damuwa,

Amma umarnanka suna faranta zuciyata.

144 Koyarwarka masu adalci ne har abada,

Ka ba ni ganewa domin in rayu.

Addu’ar Neman Kuɓutarwa

145 Ina kira gare ka da zuciya ɗaya,

Ka amsa mini, ya Ubangiji,

Zan yi biyayya da umarnanka!

146 Ina kira gare ka,

Ka cece ni, zan bi ka’idodinka!

147 Tun kafin fitowar rana ina kira gare ka neman taimako,

Na sa zuciya ga alkawarinka.

148 Dare farai ban yi barci ba,

Ina ta bimbini a kan koyarwarka.

149 Ka ji ni, ya Ubangiji, bisa ga madawwamiyar ƙaunarka,

Ka kiyaye raina bisa ga alherinka!

150 Mugayen nan waɗanda suke tsananta mini sun matso kusa,

Mutanen da ba su taɓa kiyaye dokarka ba.

151 Amma kana kusa da ni, ya Ubangiji,

Dukan alkawaranka gaskiya ne.

152 Tuntuni na ji labarin koyarwarka,

Ka sa su tabbata har abada.

Roƙo domin Ceto

153 Ka dubi wahalata, ka cece ni,

Gama ban ƙi kulawa da dokarka ba.

154 Ka kāre manufata, ka kuɓutar da ni,

Ka cece ni kamar yadda ka alkawarta!

155 Ba za a ceci mugaye ba,

Saboda ba su yi biyayya da dokokinka ba.

156 Amma juyayinka yana da girma, ya Ubangiji,

Saboda haka ka cece ni yadda ka yi niyya.

157 Maƙiyana da masu zaluntata, suna da yawa,

Amma ban fasa yin biyayya da dokokinka ba.

158 Sa’ad da na dubi waɗannan maciya amana,

Sai in ji ƙyama ƙwarai,

Domin ba su yi biyayya da umarninka ba.

159 Ka dubi yadda nake ƙaunar koyarwarka, ya Ubangiji!

Ka cece ni bisa ga madawwamiyar ƙaunarka.

160 Cibiyar dokarka gaskiya ce,

Dukan ka’idodinka na adalci tabbatattu ne.

Duƙufa da Bin Dokar Ubangiji

161 Ƙarfafan mutane sun auka mini ba dalili,

Amma maganarka ce nake girmamawa.

162 In farin ciki ƙwarai saboda alkawaranka,

Farin cikina kamar na wanda ya sami dukiya mai yawa ne.

163 Ina ƙin ƙarairayi, ba na jin daɗinsu,

Amma ina ƙaunar dokarka.

164 A kowace rana nakan gode maka sau bakwai,

Saboda shari’unka masu adalci ne.

165 Waɗanda suke ƙaunar dokarka sun sami cikakken zaman lafiya,

Ba wani abin da zai sa su fāɗi.

166 Ina jiranka ka cece ni, ya Ubangiji,

Ina aikata abin da ka umarta.

167 Ina biyayya da ka’idodinka,

Ina ƙaunarsu da zuciya ɗaya.

168 Ina biyayya da umarnanka da koyarwarka,

Kana kuwa ganin dukan abin da nake yi.

Addu’ar Neman Taimako

169 Bari kukana yă kai gare ka, ya Ubangiji!

Ka ganar da ni kamar yadda ka alkawarta.

170 Bari addu’ata ta zo gare ka,

Ka cece ni kamar yadda ka alkawarta!

171 Zan yabe ka kullayaumin

Domin ka koya mini ka’idodinka.

172 Zan raira waƙa a kan alkawarinka,

Domin umarnanka a gaskiya ne.

173 Kullum a shirye kake domin ka taimake ni,

Saboda ina bin umarnanka.

174 Ina sa zuciya ga cetonka ƙwarai, ya Ubangiji!

Ina samun farin ciki ga dokarka.

175 Ka rayar da ni don in yabe ka,

Ka sa koyarwarka su taimake ni!

176 Ina kai da kawowa kamar ɓatacciyar tunkiya,

Ka zo ka neme ni, ni bawanka,

Saboda ban ƙi kulawa da dokokinka ba.