ZAB 120

Addu’ar Neman Taimako

1 Sa’ad da nake shan wahala,

Na yi kira ga Ubangiji,

Ya kuwa amsa mini.

2 Ka cece ni, ya Ubangiji,

Daga maƙaryata da masu ruɗi!

3 Ku maƙaryata, me Allah zai yi da ku?

Yaya zai hukunta ku?

4 Da kibau masu tsini na mayaƙa,

Da garwashin wuta zai hukunta ku!

5 Zama tare da ku mugun abu ne, kamar zama a Meshek,

Ko tare da mutanen Kedar!

6 Na daɗe ƙwarai ina zama tare da mutane marasa son salama!

7 Sa’ad da nake maganar salama,

Su sai su yi ta yaƙi.