ZAB 122

Yabon Urushalima

1 Na yi murna sa’ad da suka ce mini,

“Tashi mu tafi Haikalin Ubangiji!”

2 Ga shi kuwa, mun iso,

Muna tsaye a ƙofofin Urushalima!

3 Urushalima birni ce wadda aka maido ta yadda take dā,

Da kyakkyawan tsari, a shirye!

4 A nan kabilai sukan zo,

Kabilan Isra’ila,

Domin su yi godiya ga Ubangiji,

Kamar yadda ya umarce su.

5 A nan majalisu suke,

Wurin da sarki yake yi wa jama’arsa shari’a.

6 Ku yi wa Urushalima addu’ar salama!

“Allah ya sa masu ƙaunarki su arzuta!

7 Salama ta samu a garukanki,

Da zaman lafiya kuma a fādodinki.”

8 Saboda abokaina da aminaina,

Na ce wa Urushalima, “Salama a gare ki!”

9 Saboda Haikalin Ubangiji, Allahnmu,

Ina addu’a domin ki arzuta.