ZAB 139

Cikakken Sanin Allah da Kulawarsa

1 Ya Ubangiji, ka jarraba ni, ka san ni.

2 Ka sa dukan abin da nake yi,

Tun daga can nesa ka gane dukan tunanina.

3 Kana ganina, ko ina aiki, ko ina hutawa,

Ka san dukan ayyukana.

4 Tun kafin in yi magana

Ka riga ka san abin da zan faɗa.

5 Kana kewaye da ni a kowane sashe,

Ka kiyaye ni da ikonka.

6 Yadda ka san ni ya fi ƙarfin magana,

Ya yi mini zurfi, ya fi ƙarfin ganewata.

7 Ina zan tafi in tsere wa Ruhunka?

Ina zan gudu in tsere maka?

8 Idan na hau cikin samaniya kana can,

In na kwanta a lahira kana can,

9 In na tashi sama, na tafi, na wuce gabas,

Ko kuma na zauna a can yamma da nisa,

10 Kana can domin ka bi da ni,

Kana can domin ka taimake ni.

11 Da na iya roƙon duhu ya ɓoye ni,

Ko haske da yake kewaye da ni

Ya zama dare,

12 Amma har duhun ma, ba duhu ba ne a gare ka,

Dare kuwa haskensa kamar na rana ne.

Duhu da haske, duk ɗaya ne gare ka.

13 Kai ne ka halicci kowace gaɓa ta jikina,

Kai ne ka harhaɗa ni a cikin mahaifiyata.

14 Ina yabonka gama kai abin tsoro ne,

Dukan abin da ka yi sabo ne, mai banmamaki.

Da zuciya ɗaya na san haka ne.

15 Ka ga lokacin da ƙasusuwana suke siffatuwa,

Sa’ad da kuma ake harhaɗa su a hankali

A cikin mahaifiyata,

Lokacin da nake girma a asirce.

16 Ka gan ni kafin a haife ni.

Ka ƙididdige kwanakin da ka ƙaddara mini,

Duka an rubuta su a littafinka,

Tun kafin faruwar kowannensu.

17 Ya Allah, tunaninka suna da wuyar ganewa a gare ni,

Ba su da iyaka!

18 In na ƙirga su, za su fi tsabar yashi,

Sa’ad da na farka, har yanzu ina tare da kai.

19 Ya Allah, da yadda nake so ne, da sai ka karkashe mugaye!

‘Yan ta da zaune tsaye kuma sai su rabu da ni!

20 Suna ambaton mugayen abubuwa a kanka,

Suna faɗar mugayen abubuwa gāba da sunanka.

21 Ya Ubangiji, ga yadda nake ƙin waɗanda suke ƙinka,

Da yadda nake raina waɗanda suke tayar maka!

22 Ƙiyayyar da nake yi musu ta kai intaha,

Na ɗauke su, su abokan gābana ne.

23 Jarraba ni, ya Allah, ka san tunanina,

Gwada ni, ka gane damuwata.

24 Ka bincike, ko akwai wani rashin gaskiya a gare ni,

Ka bi da ni a madawwamiyar hanya.